UKU BALA'I
NA.
KAMALA MINNA.
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร.
BABI NA SITTIN DA HUDU.
Duban idanuwanta yake yi dauke da wani irin yanayi mai taba zuciyar masoya wanda suka tsumu cikin kugin soyayya da kaunar juna fuskarsa sai kara yalwatuwa take yi da murmushi mai girman gaske janye idanuwansa yayi lokaci guda yana mai da numfashi kafun ya motsa laɓɓansa.
"Mariya kin yi shiru baki ce komai".
Murmushi ita ma tayi gami da tura dan yatsanta guda cikin baki kafun ta shiga kokarin magana.
"Duniyarnan a yanzu jin ta nake kamar ba wanda ya kai ni farinciki a cikinta".
Cikin mamaki da tuhuma yake dubanta jin abin da tace dashi sosai yake ji a zuciyarsa wani iri yanayi musamman yarda ya ga ta saki jiki dashi yau rana daya tana dariya gami da murmushin da yake kokarin hallaka masa zuciya.
"me ke faruwa ne Preety? da alamun zuciyoyi sun kusan barin kunci zuwa farinciki".
Runtse idanu tayi gami da buÉ—e su sosai akan sa kafun ta juya ta kalli kofar gidansu.
"Mahaifina ya dawo".
Zare idanu yayi cikin mamaki da kuma al'ajabi bakin sa yake motsawa yana son yin magana amma ya kasa wani farinciki ya ke jin kansa a ciki a daidai wannan lokaci da bai taba tsammani ba lokaci guda yaji kamar an watsa shi cikin aljanna don farin cikin da sauri ya kara takowa zuwa gareta kamar zai hade jikinsa da nata da sauri ta ja baya da murmushi afuskarta.
"Are you Seriuos?".
Ya fadi yana mai tallaɓe haɓarsa sai faman zabga murmushi yake yi gyaɗa masa kai tayi da sauri ya juya yana kokarin tunkarar kofar gidan da sauri ta daga masa hannu tana mai sanya idanuwanta cikin nasa.
"Me kenan kake kokarin yi?".
"Oh God! don Allah ki bar ni naje na gan shi kin ji kuwa yarda zuciyata take farin ciki kin ji irin dadin da nake ji a wannan ranar sosai nake jina a wani mataki mai girma wanda na jima ban shige shi ba ZUCIYARMU DAYA ne ni dake abu daya muka zama dole na tayaki farinciki dole na nuna kauna ga yanayin da kike ciki ayanzu".
Yana gama fadin haka ya riko hannayenta ya fara kokarin janta da sauri ta fizge tana dubansa lokaci guda ta daure fuska tamau kamar ba ita bace mai dariya da farinciki yanzu idanuwanta take amfani da su tana tura masa hukuncin kuskuren da yayi a yanzu abin da ta tsana abin da bata so shine yau yayi mata tana soron irin wannan yanayin sam bata so ko numfashi suna hadawa da É—a namiji domin kuwa sosai ta tsorata dashi musamman ganin halin da Hafsat ta shiga A DALILIN ÆŠA NAMIJI duk da dai ita har da yardarta da amincewarta domin ba yarda za ayi namiji ya saka mace yin abu dole ba tare da amincewarta.
Sosai ya gane yayi kuskure sosai yake jin kallon da take masa yana bula masa jiki yana yanke masa hukunci mai girma runtse idanu yayi ganin yarda fuskar tata ta sauya a lokaci guda.
"Kiyi hakuri Mariya hakan ba halina bane ban yi da wata manufa ba dokin farincikin ki ne shi ya je fani a wannan matakin da na so aikata kuskure mafi girma a gareki".
Kau da kanta tayi batare da ta ce dashi kala ba ta fara tafiya domin komawa cikin gida shi kansa ya tsorota sosai ganin yanayin da take ciki a hankali ya fara bin ta a baya tana jin ta kunsa amma tayi banza dashi domin kuwa sai ta nuna masa kuskurensa ko da kuwa ba da gangan yayi ba.
Ko da suka isa cikin soro juyowa kawai tayi ta dubeshi ta dauke kanta hakan ya sanya shi saurin tsayawa sai faman ware idanu yake yi yana jin yarda zuciyarsa ke wani irin abu kamar zata faso kirji ta fito waje.
Bai san gangancin da ya kai shi aikata haka ba bai san tsautsayi da ruÉ—un da ya shige shi ba har ya aikata haka ba yake kokarin yiwa kasan salalar tsiya ya manta rabon da ya ga bacin ran Mariya amma yau daya abi sa kuskuren sa yana kokarin yi wa kansa SAGEGEDUWA...
Motsin da yaji ne ya sanya shi saurin dawowa hayyacinsa daga duniyar tunani Mu'azzam ya gani tsaye hannunsa dauke da babbar sallaya da sauri ya isa gareshi yana kamo hannusa gami da durkusawa gabansa yana kallon sa cikin idanuwansa da wani irin yanayi riko sosai yayi wa Mu'azzam har sai da ya fara mutsu-mutsun kwace kansa.
"Dagaske Abba ya dawo?".
Ya tambayeshi don ya rasa ma abin da zai ce dashi fuskarsa yake kallo kamar ta Mariya sak! Runtse idanu yayi kafun yaja wani dogon numfashi ganin yarda Mu'azzam ke kallon sa kamar a tsora ce.
Sakin sa yayi gami da mikewa ya anshi Sallayar ya shimfida Mu'azzam ya juya yana kokarin komawa ciki ya riko shi gami da jan sa a jikinsa suka zauna kan sallayar.
Sun dauki lokaci a haka Dr.Karami sai faman tambayarsa yake tun yana É—ari-É—ari dashi har ya saki jiki dashi yana bashi labarin abin da ya sani suna cikin haka sai ga Abban ya fito da sauri Dr.Karami ya shiga kokarin mikewa yana sauka daga kan Sallayar yana zubewa cikin girmamawa da ladabi da sauri Abba ya riko shi fuskarsa da murmushi a cikinta.
"Haba Hisham meye kuma haka kake yi sai kace wani karamin yaro tashi ka koma ka zauna".
Ya fadi yana mika masa hannu suyi musabaha amma Dr.Karami sai wani nokewa yake yi yana mai jawo Mu'azzam yana zaunar dashi kan cinyarsa.
Soron ne ya dau shiru na yan dakikai kafun Dr.Karami ya kara kasa da kai cikin murya kasa-kasa ya shiga yi masa jaje akan abin da ya faru.
"Bakomai Hisham komai da ka ga ya faru a duniyar nan to dama tun fil'azal Allah ya rubuto shi a KUNDIN ƘADDARARMU".
Ya nisa gami da sake duban Dr.Karami sosai, da kansa ke kasa wata kunya ce yaji ta lullube shi tun da yake bai taba yin haka ba yau ce rana ta farko duk sai ya jishi wani banbarakwai.
"Ban san da bakin da zance da kai komai ba, ban san da wasu irin kalamai zan yi maka godiya ba, Hisham kayi mani komai a rayuwa kayi mani abin da ko dangina da yan'uwana bana tunanin akwai wanda zai iya hakan. Sosai naji dadi sosai naji farin ciki zuciyata ta jima tana kuna da takaici acan cikin wahalar da na tsinci kai na ban damu da tawa rayuwar ba sai ta IYALINA sosai nayi kuka nayi bakin ciki akan rashin basu kariya a ga rayuwarsu musamman a yarda na bar su na shiga tashin hankali tashin hankali mai girman gaske na tsani kai na tsani rayuwar da nayi dalilin ban san halin da IYALINA suke ciki ba...".
"Abba da ka daina TUNA BAYA abin da ya wuce ya rigaya ya wuce kuma komai ya faru damu a duniyar nan ALKALAMIN ƘADDARA ne sila ba a son ranka komai ya faru ba ba wai kayi haka bane da wata manufa Allah ya ƙaddara sai ka je wani wajan ka rayu akwai abin da Allah ya gani ya sanya ya turaka wata duniyar kayi rayuwa".
Dr.Karami ya fadi muryarsa can kasa sai faman wasa yake yi da yatsun hannun Mu'azzam.
Hawaye Abba ya goge wanda bai san sun zubo masa ba sai da ya ji dumin su a hankali ya shiga baiwa Dr.Karami labarin rayuwar da ya tsinci kan sa har izuwa haduwarsu da Baffa...
Sosai ya ji zuciyarsa wani iri sosai yaji tausayin su Mariya ya kamashi dago kai yayi ya dubi Abba da idanuwansa ke ta faman ZUBAR KWALLA zuciyarsa yaji tana kara matsewa da kaunar ahalin nan masu ciki da SADAUKARWA da kaunar juna su musamman yarda yaji AKAN SO suka fada wannan rayuwar su dukan su ashe haka akewa SO BIYAYYA ashe haka ake sadauƙar da komai da kowa a rungumi masoyi ashe shi bai ma yi so ba.
Numfashi yaja mai karfi yana sake duban Abba wanda ya shafe fuskarsa kamar bai yi kukan ba sosai yake duban Dr.Karami yana jin wata kaunarsa na ratsa masa zuciya sosai yake jin zai iya yarda ya zama mijin 'yarsa domin ya yi amanna dashi da kuma irin nagartarsa ya tabbata 'yarsa ba zata koka ba a gidan sa so yake yi yayi masa magana amma ya kasa so yake yi yaji daga bakin sa in har ya furta KALMAR SO ga Mariya shi kuwa zai masa tukuici da ita.
A hankali Dr.Karami ya shiga kokarin tashi alamun tafiya sallama sukayi ya mike har zuwa lokacin Mu'azzam na like dashi hannu ya saka ya zaro kudi masu dan dama ya ajje kan sallayar ya juya yana kokarin tafiya.
"HISHAM!".
Yaji Abba da wata irin muryar mai girma da zurfi a jikinsa yake ji kamar akwai abin da yayi ba daidai ba da sauri ya juyo ya dubi Abba kallon da ya ga yanayi masa yayi matukar bugar masa da zuciya sai dai murmushin da ya gani kuma ya bashi mamaki.
"Zo ka dauki kudin ka don Allah".
Ya fadi shima yana mikewa yana kara faÉ—aÉ—a murmushin sa, kuri yayi masa da idanu wani irin kwarjini ya ga yanayi masa magana yake so yayi amma ya kasa a hankali ya ja kafafuwansa ya iso gami da sanya hannu ya dauki kuÉ—aÉ—en.
"Abba kayi Hakuri...".
"Bakomai Hisham hidimar za tayi yawa ka gaishe da Hajiyar taka".
Ya fadi yana mai juyawa ya koma cikin gida cike da farin ciki da kwanciyar hankali yarda yaga halayen Dr.Karami dama tuni Umma duk ta karance masa komai da komai da yake faruwa.
Dr.Karami hannusa rike da na Mu'azzam suka isa bakin motarsa ya buÉ—e wata katuwar leda ya dauko ya mika masa kafun ya sake dauko wata ya bashi.
"Wannan taka ce kai kadai ko Yah Mariya karka baiwa wannan kuma Umma za ka kaiwa".
Dariya yayi gami da fadin 'Nagode' sannan ya juya ya fara tafiya yana daga masa hannu shima hannu yake daga masa yana jin kaunar wannan Iyalin na kara ratsa masa zuciya da ruhinsa..
*****
Da mamaki yake dubanta zuciyarsa na yayyagewa da tashin hankali bai taba zaton abin da zata fada masa ba kenan bai taba zaton in ya zo abin da zai tadda ba kenan in da yasan wannan bakar maganar zai tadda da bai zo ba zuciyarsa kara matsewa take yi da tashin hankali idanuwansa sun kaÉ—a sun yi ja duk wani farinciki da ya jima yana yi tun da yaji ta sanar dashi dawowar mahaifinta har rawar jiki yake yi wajan zuwa taya ta murna sai dai ashe ba nan gizo ke sakar ba.
numfashi yake ja wanda yake jin sa kamar zai tafi masa da ransa duban ta yasake yi karo ba adadi kanta akasa yake yana hango yarda hawaye ke zubowa saman kuncin ta wani irim rauni ya sake jin zuciyarsa tana kara mikashi a ciki, hannayensa duk biyu ya dafe kansa dashi da yake jin yana faman kumbura kamar zai tarwatse laɓɓasa ya tura cikin bakin sa yana cizawa.
"Mariya dama bakya so na dama duk BIYAYYAR SO da nake yi akan ki ta banza ce ashe akwai ranar da zaki nuna min iyakata haba! Mariya don Allah karki ce dani wannan maganar gaskiya ce don Allah ki ce wasa kike yi".
Ya fadi yana jin duniyar na kara yamutse masa da wani irin tashin hankali mai girman gaske dago idanuwanta tayi wanda suka kaÉ—a sukayi jajir bakin ta sai rawa yake yi hannayenta dafe da kirjnta da take ji kamar zai tarwatse ita kanta ta san tayi ganganci ba ta san abin da yasa ta aikata hakan ba abin da take gudu kenan nayin BUTULCI ga Dr.Aqeel ta san batayi masa adalci ba batayi wa ita kanta adalci ba numfashi ta ja kafun ta sake dubansa sosai.
"Kayi hakuri Dr.Aqeel ban yi haka don na tsane ka ba hasali ma ni ce mai son ka da kaunar k...".
"Ya isa haka ki daina yiwa so karya akai na kawai ki fito fili kice bani kike so ba wani na kike so".
Runtse idanu tayi tana jin sautin muryarsa mai sauti tana dukan zuciyarta da kwanyarta wani kuka ne ya kwace mata da sauri ta rufe bakinta jikinta ya shiga rawa numfashinta ya shiga tsittsinkewa hakan da Dr.Aqeel ya gani ya kara rikita shi da sauri ya iso gareta ji yake yi kamar ya rikota ya hadata da jikinsa ya rarrashe ta.
"Kayi hakuri na san ban kyauta maka ba na san naci amanar soyayyarmu amma ina so ka dube ni da idon basira sannan ka fahimce ni ban yi haka don in tozarta ka ba ban yi haka don ba na son ka ba in da bana son ka ba yarda za ayi har nake tsayuwa da kai in da bana son ka ba yarda za ayi na bar zuciyata ta kauna ce ka ka sani ni da Baseera abu daya ne duk wani abu da kake tsammanin zaka samu gareni na kulawa da biyayya a soyayarka zaka samu a gareta fiye ma da haka hasali ma Baseera tafi ni komai da komai na rayuwa ina rokonka don Allah don Annabi ka dauki Baseera kamar yarda kake dauka ta ka sannan ina so kayi mata so kamar yarda kake yi mani koma fiye da hakan don Allah na roke ka in har son da kake yi mani kana so na kara gasgata shi to ina so ka komar dashi kanta".
Ta fadi cikin rawar murya a hankali ta shiga ja da baya idanuwanta na kara ballewa da hawaye hannu ta daga masa kafun ta juya cikin sauri ta fada cikin gida.
Runtse idanu yayi maganganunta yake ji suna yi masa yawo akai zuciyarsa yake ji tana kara matsewa da kalamanta da sauri ya ja jiki kafafuwansa yake ji suna harÉ—ewa kamar za su zubda shi kasa ya fada cikin motarsa tare da yi mata key ya fizgeta ya fice daga cikin unguwar zuciyarsa na wani irin mataki wanda ba zai ce gashi ba...
*Kamala Minna*😘😘😘