UKU-BALA'I 62

UKU BALA'I
               NA.
        KAMALA MINNA.
 
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
​​WÉ› ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucÉ‘tÉ›, MѳtiѵɑtÉ› ɑɳɗ ɛɳtɛʀtÉ‘iɳ ѳuÊ€ ʀɛɑɗɛʀร​.
  BABI NA SITTIN DA BIYU
Gabanta take ji yana faduwa sosai da sosai ga wani irin yanayi da take jin gangar jikinta na shiga runtse idanu tayi a daidai lokacin da Umma ta shigo cikin dakin dauke da bokitin Cake da ta gama yi can gefe ta ajje shi sannan ta juyo ta dubi Mariya da tayi shiru kamar wacce ake yiwa wasiyya girgiza kai tayi kafun ta motsa laɓɓanta.
 "Kin ga Cake din nan na yau ya bani mamaki kamar ba yarda ake yi ba wallahi yayi albarka sosai".
Ta fadi tana mai zaunawa gefe gudu har zuwa lokacin idanuwan Mariya na buÉ—e sai faman ajiyar numfashi take yi hannu ta kai saman kirjinta ta dafa gami da buÉ—e idanuwan nata tana duban Umma.
Murmushin yak'e ta sakar mata kafun ta mike ta iso gareta jikinta a sanyaye.
 "Umma jikina nake ji wani iri wallahi ga kirjina sai bugawa yake yi kamar wani abu zai faru dani tun safe nake jin haka".
Dubanta Umma tayi idanuwanta na yawatawa akanta so take yi ta hango wani abu da zai bata ko tabbacin abin da yake damun Mariyar.
 "Addu'a kawai zaki tayi Mariya irin haka in yana samun bawa musamman faduwa gaba Innalillahi wa inna ilaihir raji'un ake so ya ta maimaitawa".
GyaÉ—a kai tayi tana juyar da ganinta zuwa ga bokitin Cake din sannan ta juyo ta dubi Umma.
 "Yayi auki fa a hakan ma na gani...ko da yake Birin gidanmu ba ya nan shiyasa Cake din bai shiga uku ba".
Mariya ta fadi tana murmushi ita ma Umma murmushi tayi don ta gano da Mu'azzam take....
Da gudu ya fado cikin dakin yana hak'i ya fada jikin Umma dukkan su suka dube shi da mamaki dago fuskarsa yayi ya dubi Umma sannan ya dubi Mariya.
 "Ga wasu mutane nan a kofar gida su hudu har da masu kayan fulani".
Gaban Mariya ne ya yanke ya fadi kamar yarda yake yi mata tun dazu da sauri ta dubi Umma dafe da kirji yanayin ta ya sauya lokaci guda.
Ita kanta Umma ta ji faduwar gaban sosai don sai da taji cikinta yayi kara zuciyarta na tsalle kamar zata fito waje.
 "Wai cewa yayi na zo na sanar daku nan gidan su ka zo daya daga cikin mutanan yace mani haka kuma yana kama da Yah Mariy....".
Wata irin zabura Mariya tayi ta mike kan kafafuwanta idanuwanta a warwaje bugun zuciyarta take ji yana sauyawa sosai haka kawai take ji a jikinta akwai abin da ke faruwa.
Umma kuwa rintse idanu tayi tana ambaton sunayen Allah da dukkan wata addu'a da ta zo mata baki haka kawai ta ji a jikinta akwai kamshin wani abu muhimmi a batun Mu'azzam.
 "Yace fa ku zo yanzu Umma".
Ya fadi ya na mai jan hannun Mariya bayan ya tashi daga jikin Umma a hankali Mariya ta shiga bin sa kamar rakumi da ak'ala tana kallon Umma ita kanta Umma rasa abin yi tayi domin gabadaya take jin wata gajiya da kasala ta dirar mata a jiki lokaci guda ga wani bugu da zuciyarta take ta faman yi ba ƙanƙautawa laɓɓanta tashiga motsawa ta na son yi wa Mariya magana amma kamar an dora mata katon dutse a harshe hannunta tayi mata nuni dashi ta dauki mayafi .
Duban jikinta tayi ita sam ta manta ma da kayan dake jikinta a hankali ta kwace kanta daga hannun Mu'azzam ta ja kafafuwanta da take jin su kamar za su zubda ita kasa ta janyo hijabin Umma ta zira ajikinta fita tayi cikin kokarin saita kanta Mu'azzam na gaba tana biye dashi har suka isa soron gidan nan ta ci burki ta tsaya jin yarda zuciyarta take dokawa da sauri-sauri jingina tayi da bango tana mai da numfashi Mu'azzam shi kam idanu ya zuba mata har ta gama shan sharafinta ta taka a hankali suka cigaba da tafiya har suka isa kofar gida sai dai me.
Abin da Mariya ta gani ne ya kusan kashe ta da ranta runtse idanuwanta tayi sosai tana mai daura hannu aka ta kurma ihu gabadaya ta sulale zuwa kasa da sauri suka yo kanta ba wanda ya tabata ganin Babbar mace ce duban Mu'azzam sukayi gabadayan su kafun Baffa yace
 "Me ya same ta?".
"Mu'azzam da yayi firi-firi da idanu cikin yanayi na tsorata.
 "Yah Mariya".
Ya fadi ai Bello na jin haka ya sake dubanta sosai zuciyarsa da kwamyarsa suka mika shi wani mataki mai tsayin gaske da ya gama shuÉ—ewa sosai yaji wani irin abu ya dokar masa zuciya mai girman gaske.
 'Mariya'.
Ya furta hakan a ransa yana sake muntsuka idanunsa yana saukewa akanta juyawa yayi da sauri ya fizgo gorar ruwan dake rataye a jikin Ja'e ya balle kanta ya shiga kwarara mata kamar yarda hawaye lokaci guda suka shiga zubo masa a fuska wani dogon numfashi ta ja gami da buÉ—e idanunta ganin mutanan dake kanta ya sanyata saurin runtse ido tana furta. 
 "Innalillahi wa inna ilaihir raji'un".
Da karfi komai ganin sa take yi kamar ba gaske ba sosai zuciyarta ta tsorata ta sosai take jin jikinta wani iri gani take yi kamar a mafarki ba gaske ba laɓɓanta ta tura cikin bakinta tana cizawa zafin da yake ratsa ta ne ya tabbatar mata da GASKIYAR LAMARI da sauri ta sake ware idanunta.
Fuskar dake saitin ta take kallo fuskar da take hango hawaye suna zuba a samanta fuskar da ta jima tana cigiya fuskar da ta bace mata a rayuwa tsayin shekaru wai ita ce yau take gani kunnuwanta ta rufe da tafukan hanayenta gami da sake runtse idanu zuciyarta na harbawa da wani irin yanayi wanda ba za ta ce ga matsayin da zata ajje shi ba.
 "Mariya".
Muryar da ta shuÉ—e sama da shekaru bakwai ita ce yau take jinta a saitin ta tana ambatar sunanta muryar da tayi kewarta muryar da kullum take yabonta da shi mata albarka yau ita ce ta dawo gareta bayan shuÉ—ewar lokaci.
  Wani irin kuka ne taji ya zo mata da saurin ta rufe bakinta amma ina sai da sautin sa ya fita da sauri ta shiga kokarin mikewa amma ina ta kasa gaÉ“É“anta take ji kamar an doke mata su kamar daga sama taji hannaye da tajima da saninsu sun riko mata kafaÉ—u cikin wani irin yanayi suna mikar da ita kan kafafuwanta wani numfashi take ja mai tafe da kuka buÉ—e idanuwanta tayi sa'ilin da taji ana dauke mata hawayen fuska sosai take kallon sa da wani irin yanayi na mamaki da tu'ajibi gani take yi kamar bashi ba gani take yi kamar gizo yake yi mata hannayenta ta shiga dagawa tana kokarin kai fuskarsa amma ta kasa da sauri ta shiga ja da baya tana duban sauran fuskokin wanda bata shaida su ba amma a jikinta take jin wani irin yanayi game da su.
Da gudu tayi cikin gida kamar wacce za a sace a soro suka ci karo da Umma da Mu'azzam a hargitse domin tun lokacin da ya ga ta fadi din nan ya kwasa yayi cikin gida yana kiran Umma.
Kallon ta Umma take yi da wani irin yanayi gabanta take ji yana yankewa yana faduwa hawayen da ta gani a fuskar Mariya ya kara rikita mata lissafi da sauri ta riko hannunta jikinta sai faman É“ari yake yi bakinta na karkarwa.
 "Su waye Mariya...tambayarki nake yi su waye?".
Yanayin da take maganar kawai ya isa ya tabbatar maka da cewa sosai take cikin firgici Mariya da ta ga yanayin da Umma ke ciki ya sanyata sake rushewa da kuka kafun ta tsagaita da cewa. 
 "Umma Allah yasa ba mafarki nake yi ba gaskiya ne Abbana ne...".
Da sauri ta sake ta tana ja da baya gabanta na kara tsananta bugawa kafafuwanta take ji suna lauyewa idanuwanta suna lullubewa lokaci guda taji duniyar na juya mata kwanyarta na ansa kuwwa sosai jingina tayi da bango tana maida numfashi kafun ta zabura kamar wacce aka tsikara tayi hanyan waje da sauri a daidai lokacin shikuma ya sanyo kai cikin gida cikin rashin tsammani suka bangaji juna taga-taga Umma tayi zata fadi dama ba wani karfin jiki take dashi ba da sauri ya rikota gabadaya jikinsu ya dauki wani irin yanayi runtse idanu Umma tayi sosai tana jin yarda jikinta ke ansawa da wasu bakin lamari masu girman gaske gareta.
 A hankali ta shiga kokarin buÉ—e idanuwanta tana saukewa gareshi bakinta dauke da addu'a don gani take yi kamar a mafarki ba gaske ba jikinta na rawa ta dago hannunta tana shafe fuskarsa lokaci guda wasu hawaye suka shiga kwaranyo mata a fuska zuciyarta na kara matsewa kwanyarta take ji kamar za ta kama da wuta a hankali ta zare jikinta daga na shi tana ja da baya kallonsa take yi a yanzu cikin tuhuma shi kansa ya hango hakan da sauri ya dube ta amma ita juyawa tayi tana kokarin komawa cikin gida.
 "Tare da su Baffa nake".
Da saurin Maganganun nasa suka bugar mata zuciya da kwanya lokaci guda jinin jikinta da numfashinta sukayi tsayawar wucin gadi ji tayi kamar ba a duniya take ba kunnuwanta sai faman maimaita maganar da Bello yayi suke wani GWAURON NUMFASHI taja da take jin kamar zai fasa mata kirji tsoro ne sosai ya bayyana a gareta maganar take ji kamar ba gaske ba so take yi ta gasgata zuciyarta take jin tana ansawa tana amanna da batun juyawa tayi cikin wani irin yanayi mai wuyar fassaruwa ta dube shi wani kuka mai girma taji yana zuwa mata zuciyarta na buÉ—e wani wawaken ciwo da ta jima tana jinyarsa.
A hankali ya isa gareta yana riko hannayenta gami da girgiza kai idanuwanta sai faman bin shi da kallo suke komai take ji kamar almara gani take yi ko a cikin barcinta hakan ba zai faru ba amma zuciyarta sai kara karfafa mata guiwa take yi a kan ta yarda.
 Mariya da Mu'azzam suka iso garesu kallon kallo suka shiga yi a tsakaninsu Bello na duban su Mariya da Mu'azzam yana kuma duban Umma wacce ta zama wata butun butumi a tsaye zuciyarta take ji tana mikata wani mataki mai girma dauke da tashin hankali da ciwon rai ciwo ne mai girma zuciyarta ta fama mata shi wanda take ta jinyarsa ya kasa warkewa.
Duban Mariya yayi yana son yin magana amma ya kasa wani irin yanayi yake jin kansa a ciki ji yake yi kamar ba shi ba.
Sallamar da su Baffa sukayi ne ya sanya Umma mutuwar tsaye zuciyarta tayi wani bugun da sai da kirjinta ya daga da saurin ta runtse idanun tare da yin cikin gida da sauri sai faman hada hanye take yi.
A daidai lokacin da suka shigo ta karasa shigewa cikin gidan don haka Bello yayi musu jagora suka karasa shiga sai bin gidan suke yi da kallo Baffa na faman gyaÉ—a kai zuciyarsa na matsewa da ciwon da yake ji yana motsa masa tsayin lokaci wai shine yau a garin Gwada garin da yayi wa kansa alkawarin ba zai taba WAIWAYE izuwa gareshi ba yau shine a ciki a kuma gidan da 'yarsa take aure wacce ita ce silar barin sa garin hawaye idanuwansa suka kawo da sauri ya shafe su ciki da nadamar abin da ya aikata wanda yake jin ya cuci kansa sannan ya cuci 'yarsa.
Har cikin dakin su ka shiga zaune take ta hada kai da kafafuwanta zuciyarta na ta faman harbawa da wani tashin hankali mai girman gaske sallamar da taji Muryar Baffa na yi ne ya kara jefata tashin hankali runtse idanuwanta tayi gami da sake kankame kanta da sauri Mariya ta isa gareta ta zauna gefenta ganin halin da mahaifiyar tata take ciki ya sanya ta duban su Baffa da sukayi carko-carko a tsakar dakin lokaci guda kirjinta taji ya buga kallon Baffa ta shiga yi zuciyarta na dauko mata wani lamari da tunanin mai girma da take son ta tabbatar da gaskiya a kansa can kasar zuciyarta take furta 'Baffa' da sauri ta sake duban Umma sannan ta dubi Baffa zaro idanu tayi waje ta shiga nuna shi da yatsa laɓɓanta sai motsawa suke yi.
 "Umma dago kanki wannan kamar Baffanki?".
Mariya ta fadi Muryarta na rawa sosai Baffa da ke tsaye a hankali ya tako ya iso garesu hannun Umma ya riko wanda taji rikon a bazata sosai ta firgita tare da kau da kanta domin bata son kallonsa ta san ita mai laifi ne laifin ta mai girma ne a gareshi.
 "HABEEBA!".
Ta ji ya ambaci sunanta da muryar mai laushi wacce rabon da taji ta har ta manta dago kanta tayi wanda sukayi face-gace da hawaye ta sauke a fuskarsa murmushi ta ga yanayi mata hakan ba karamin mamaki ya bata ba bakin ta na rawa.
 "Baffa na san ni mai laifi ce ban cancanta ka dube ni ba ban cancan ci ka zo gareni ba Baffa na tuba na san na kuntata maka na san na dasa maka ciwo a zuciya shiyasa tun da na rabu da kai har yau ban samu natsuwa da kwanciyar hankali ba...".
 "Habeeba".
Ya sake fadi da muryarsa mai taushi gami da nuna mata alamun tayi shiru hakan yayi matukar bata mamaki wai Baffanta ne haka yau shine yake yi mata magana a cikin salama ba zata taba manta ranar da ya rabu da ita ba ya mikata a hannun Bello yace ya yafeta amma yaushi ne a gareta abun yayi matukar daure mata kai sake runtse idanu tayi don ita har yanzu ba ta yarda wai Baffa da Bello bane a gabanta.
 "Habeeba ki daina fadin haka ni Mahaifinki ne nasan na dauki hakkinki na sanya ki cikin damuwa da rashin kwanciyar hankali a dalilin son zuciya irin tawa ina neman afuwanki ki yafe mani nima na yafe miki duk wani laifi da ki kayi mani ga mijin ki nan ya fada min komai".
Wani kuka ne ya sake sarke ta shiga yin sa ba kankautawa ba wanda bai tausaya mata ba cikin dakin Ja'e da Iro su kan su sai da suka ji tausayin yayar ta su gwuiwowinta a kasa take neman afuwan Baffa Mariya da Mu'azzam suma haka suke yi suna taya ta rokon Baffa kamar yarda suka ga tana yi sai da suka shafe tsayin lokaci a haka kafun suka yi shiru nan dakin ya dau shiru.
Baffa ya shiga karanta mata komai da ya faru da Bello don sam! Umma kamar ba tayi maraba dashi ba sosai yayi mata bayani sannan ta yarda shima ya kora mata da irin matsalolin da ya fuskata da irin SIRAÆŠIN RAYUWA da ya fada sosai Umma tayi kuka jin irin bala'in da mijinta ya fada ciki musamman da taji yace bai san lokacin da ya tafi ya bar su ba shi dai kawai ya tsincin kansa a wani waje ne.
 "Wai hayaniyar me nake ji ne cikin dakin nan tun dazu kamar gidan yan barik...".
Guntse sauran maganar ta tayi daidai lokacin da ta daga labule idanuwanta suka sauka kan na Bello da ya kafe ta da idanu hannunsa rungume da Mu'azzam mutuwar tsaye tayi kafun ta dawo hayyacinta tana duban mutannan cikin dakin daya bayan daya idanuwa a warwaje kamar wacce tayi wa sarki karya bakinta ya fara motsi jikinta yana rawa ta shiga fadin.
 "Bello dama kana duniyar nan".
Da sauri ya ansata da murmushi a fuskarsa.
 "Ga zahiri kin gani Goggo Marka".
Da sauri ta juya tayi waje har tana tuntube dukansu suƙa hada idanusu kowa da abinda ke ransa...
    *KAMALA MINNA*😘😘😘😘😘

Post a Comment (0)