UKU-BALA'I 65

UKU BALA'I
                NA.
            KAMALA MINNA.

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
​​WÉ› ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucÉ‘tÉ›, MѳtiѵɑtÉ› ɑɳɗ ɛɳtɛʀtÉ‘iɳ ѳuÊ€ ʀɛɑɗɛʀร​.
  BABI NA SITTIN DA BIYAR
Sosai ya kasa gane kansa komai yake jinsa yana sauya masa lokaci guda zuciyarsa yake ji tana harbawa da wani irin yanayi mai raÉ—aÉ—i a zuciya bai san yarda zai yi ba bai san abin da ya kamata yayi ba zuciyarsa ta cushe kwanyarsa sai hayaki take yi kamar zata kama da wuta duniyar gabadaya yake ji tana kai komo dashi jin sa yake kamar bashi ba kamar wani daban aka dauko aka ajje.
Numfashi yasake ja karo na ba a dadi yau kusan kwana uku kenan yana jinyar kansa kokari yake yi ya saita kansa amma hakan ya gagara zuciyarsa taki amanna akan abin da ake so yayi sosai yake jin GURBIN SO mai girma wanda ya baiwa Mariya ba zai iya barinsa ya so wata daban ba baya tunanin hakan zai iya kasantuwa son Mariya ta zama komai nashi ita ce rayuwarsa dama numfashin sa baya tunanin rayuwarsa zata yi karko in har ba soyayyar Mariya bace tadawo gareshi sosai yake kallon kansa a matsayin GAWA DA RAI.
Hannayensa duka biyu ya dafe kansa da su yana faman jan numfashi mikewa yayi kan gadon yayi zaman dirshan gami da zabga tagumi yawatawa ya shiga yi da idanuwansa komai gani yake yi yana sauya masa komai yake ganin baya burgesa a filin duniyar nan komai yake ji kamar ciwo ne a gareshi zuciyarsa yake ji tana matsewa da wani irin tashin hankali mai girman gaske ji yake yi ko wani sashi da lungu na zuciyarsa na kara yayyagewa da son Mariya kokari yake yi ko zai iya abun da ta bukata amma ji yake yi kamar kara rura wutar sonta ake yi a zuciyarsa.
A hankali ya zuro kafafuwansa zuwa kasa ya mike akan su jikinsa sanye da kayan barci farare masu dingo blue maballin gaban rigar ya gyara da ya fice ya zura silifas din dake yashe a kasa toilet ya nufa cikin rashin kwarin jiki da na zuciya.
Yana shiga ya sakarwa kansa shawa mai ruwan dumi sosai yake jin ruwan na ratse shi ta ko ina zuciyarsa dake zafi yake jin tana sauka kadan-kadan runtse idanuwansa yayi yana furta.
 "Yaa Hayyu Yaa Kayyum".
Kusan minti ashirin ya shafe a toilet din kafun ya wanke bakinsa gami da dauro tawul a kugunsa da wani kuma a hannunsa yana tsane kansa da sajen fuskarsa da yake karawa fuskart asa kyau da kwarjini fitowa yayi ya tsaya gaban Mirrow yana kallon kansa sosai yake hango ramar da yayi shi kadai ya san wahalar da yake sha shi kadai ya san azabar da zuciyarsa take kawo masa gabadaya ya daina jin dadin komai WALWALAR ZUCIYA gabadaya yanzu bai samunta har ya manta yaushe rabonsa ya jidadi da nishadi a duniyarsa.
Numfashi ya ja gami da juyawa ya nufi sif din dake manne da bangon dakin buÉ—ewa yayi yana kallon ko wani sashi na cikin sa kaya ne makil a cikinsa a shirye hannu ya sa ya shiga dagawa yana kallo so yake yi ya zabi wanda zai saka amma gabadaya kayan ma jin su yake yi wani iri ya jima a tsaye yana zarowa yana mai dawa ya rasa wanda zai dauko lokaci kankani duk ya yamotse sif din kafin ya zaro wani lallausar yaÉ—i light-blue mai dikon dark anyi masa dinkin zamani wanda ya fita sosai.
Bakin gado ya ajje su sannan ya juya ya koma wajan Mirrow din fuskarsa ya dan gyara sannan ya koma ya zura kayan a jikinsa wanda sukayi matukar hawan sa sosai suka kara fidda masa da kyansa gami da kwarji agogon Rolex ya daura a hannunsa gami da kafa hularsa wacce ta hau kayan sosai takalmin kafarsa sau ciki baki sai daukar idanu yake yi glass ya saka a idanuwansa wanda ya kara sirrinta yanayin da yake ciki.
Key din motarsa ya dauka gami da wayoyin sa bayan ya feshe jikinsa da daÉ—aÉ—ar turarurruka masu sanyin kamshi a hankali ya shiga taka kafafuwanta yanayin sa kadai zai nuna maka ba ya cikin nishadin zuciya saidai cikar halintarsa da mazatakarsa da ka kalla zaka gane namiji hadadde mai ansa sunan sa na mijin.
Kokari yake yi ya aikata abin da zuciyarsa take hana shi so yake yi ya koyi wannan rayuwar da aka zaɓar masa bashi ya zaɓa ba so yake yi ya koyi rayuwar da ake cewa ba zai yi nadama akan ta ba so yake yi ya matse zuciyarsa ta koyi abin da ake so ta koya so yake yi a wannan ranar komai ya canza so yake yi zuciyarsa da koyi kaunar wacce ake so ya mikawa soyayayarsa ya sani SO ƘADDARAR ZUCIYA ne so ne kadai ke wahalar da ita ya sata cikin duk wani kunci da gangar jiki zai wahala shi ma.
Da wannan tunanin ya isa gaban sabuwar motarsa kirar Benz mai kalar baki sai faman daukar idanu take yi sai da ya kare mata kallo yau ne rana ta biyu da zai hau ta tun da yayo odarta haka kawai yaji yana bukatar ya fita da ita daga can nesa ya hango mai gadin sa hannu ya daga masa da gudu ya iso gareshi yana mai kwasar gaisuwa kafun ya mike ya nufi wajan Get ya hangame shi a daidai lokacin shi kuma Dr.Aqeel ya shige motar har yayi mata key ya doshi Get din a hankali har ya fice mai gadi nayi masa a dawo lafiya sannan ya mai da Get din ya rufe.
****
Gabanta ne ya yanke ya fadi sallamar da tayi ba ta karasa ta ba taja burki ta tsaya sai faman rarraba idanu take yi shi kuwa ya kafe ta da idanu kamar zai haÉ—iyeta hakan ya kara rikita mata lissafi ji tayi kamar ta juya ta falle da gudu amma jin muryar Hajiya ya sanyataa motsa kafafuwanta da take jin su kamar za su zubda ita kasa a hankali ta shiga takawa tana karasa cikin falon ko ina na jikinta rawa kawai yake yi ga wani dokawa da gabanta ke yi musamman irin kallon da ta ga Tareeq na yi mata kau da kai tayi shiyasa sam bata son zuwa gidan nan ko don saboda shi ba ta son irin abin da yake yi mata.
"Ina yini Mami".
Mariya ta fadi bayan ta isa gareta ta zauna.
"Lafiya lau Mariya ya gida ya su Umman taki da Abban naki?".
GyaÉ—a kai tayi kafun ta ansa da cewa.
"Lafiya lau duk suna gaishe ku".
Daga nan bata sake tsinkawa ba sai Mami ce ta sake cewa.
"Shekaran jiya ai mun je kina Islamiyya ba mu tadda ki ba".
Murmushi tayi gami da kokarin mikewa.
"Umma ta gaya min Mami Allah ya saka da alheri ya kara buÉ—e gami da rufin asiri...".
"Mariya kar ki sake kin ji ko ai mun zama daya komai aka yi muku a gidan nan ai ba faduwa bane kun zama yan uwanmu mu ma haka duk an zama abu daya...mutuniyar taki tana ciki kisan dai san halinta kullum tana kunshe a daki kamar mai zaman takaba".
Dariya ta sake yi sannan cikin hanzari ta nufi sama sashin Baseera zaune ta same ta hannunta rike da littafi da sauri ta karasa kusa da ita ta zauna sam hankalinta ba ya jikinta domin tunani take yi ba wai karatun littafin ba da sauri Mariya ta zungurar mata kafaɗa a firgice ta dube ta ganin Mariya ya sanyata zaro idanu waje tana mai da numfashi ta shiga motsa laɓɓanta tana son yin magana amma ta kasa.
"Kin kyauta Baseera wato shi ne kika dauke mani kafa ko kirana ma da kike yi a wayar Umma kin daina sabida na yi miki laifi mai girma ko har da ya kai kiyi mani hukunci irin haka....Hmm Hakuri na zo na baki akan abin da nayi miki ba daidai...".
Da sauri Baseera ta rufe mata baki wasu kwalla na taruwa a idanunta ta shiga girgiza kai .
"Ba haka bane wallahi ba na jindadi ne...".
Turo kofar da akayi ne ya sanya Baseera saurin yin shiru tana goge fuskarta Mami ce ta shigo duban su tayi ganin yanayin da suke ciki batare da tace komai ba sosai suka gane kallon zargin wani abu take yi musu.
"Baseera kin yi bako".
Abin da ta fadi kenan ta fice daga cikin dakin gaban Baseera ya buga gami da duban Mariya da ita ma idanuwanta suke kanta kallan kallo suke yi wa juna kafun Mariya tayi murmushi tana mai dafa kafaÉ—arta.
"Kin yi bako aka ce".
Runtse idanu Baseera tayi tana jin yarda gabanta ke yankewa ya na faduwa.
"Ban san waye ba Mariya ba muyi da wani zai zo waje na...".
Daga mata hannu tayi tare da mikewa tana kamo kafarta doguwar riga ce a jikinta don haka ta janyo mata gyalan rigar ta yafa mata fuskarta ba wata baci tayi ba don haka ta ja hannunta suka fice.
A harabar gidan suka hango mota girke da sauri suka dubi juna gaban Mariya ne ya fadi tana tunano inda ta san motar nan sosai ta ke ji a ranta ta taba ganinta amma ta rasa waye mai ita...
Bata gama tunanin tuno mai motar ba ta ga an buÉ—e kofar ana kokarin fitowa da sauri ta runtse idanu jin yarda kirjinta ya doka rikon da taji Baseera tayi mata ne jikinta na karkarwa tana jin yarda take kokarin yi mata magana amma ta kasa hakan ya tabbatar mata da zarginta da sauri ta zare hannunta daga na Baseera tana kokarin juyawa ta koma ciki amma jin amon muryar sa ya sanyata tsayawa cak! tana mai da numfashi takun takalminsa da yake tunkaro su hakan ya kara rikita mata lissafi ta kara danke idanuwanta kamshin turarensa take ji ya dokar mata hanci zuciyarta take ji tana matsewa da wani irin yanayi tana mikata wani mataki bata san ya za tayi ba bata san da wani idanu zata kalle shi ba sosai take jin rashin adalcin da tayi masa a ranta haka kawai take jin wata kunyarsa ta ratsa ta.
"Gani na zo domin yiwa so biyayya Mariya abin da kika bukata shi na zo yi domin tabbatar da abin da kike tsammanin ba haka bane".
Wata irin bugawa taji zuciyarta tayi da sauri ta juyo gami da buÉ—e idanuwanta da suka kaÉ—a sosai ta dubi Baseera da tayi fakare da idanu tana dubansu daya bayan daya zuciyarta na bugawa da tashin hankali ashe da gaske Mariya take ashe abinda take faÉ—i mata zatayi ashe zata yi din da gaske.
 girgiza kai ta shiga yi tana saka idanuwanta cikin na Mariya da ta gama shiga wani yanayi mai wuyar fassaruwa.
"Ban gane ba Mariya mai hakan ke nufi?".
"Soyayyarta ta sadaukar gareki".
Zare idanu Baseera fuskarta da wani irin yanayi mai girma a zuciyarta sosai take jin zuciyarta na matsewa da tashin hankali maganganun Dr.Aqeel take jin su wani iri a gareta sosai take jin suna hawa mata kai hannunta taji Mariya ta kama ta damke sosai da sauri ta dago ta dube ta idanuwanta ta gani cike da hawaye suna kokarim zuba.
 "Kin yi mani alkawari in har ya amince ke ma zaki amince don Allah karki watsa min kasa a idanu Baseera ki dubi Dr.Aqeel a matsayin masoyi mai kaunarki tsakani da Allah kiyi mani wannan sadaukarwar don Allah ban taba neman alfarma gareki ba sai yau don Allah ki anshe ta".
Fizge hannunta Baseera tayi tana mai da numfashi zuciyarta take ji tana bugawa da wani irin yanayi.
"A,a Mariya ba na tunanin hakan za ta faru karki takurawa zuciyoyin da ba sa kaunar junansu karki yi kokarin hada abin da kika san ba zai taba faruwa ba karki hada abin da kika san zuciyoyi ba za su samu farin ciki ba".
Ta fadi muryarta na rawa wasu hawaye na zubo mata a hankali ta shiga ja da baya tana girgiza kai.
A daidai lokacin shi kuma Dr.Aqeel ya kara takowa kusa da su sosai zuciyarsa yake ji tana matsewa da kuna gami da radadi runtse idanu yayi kafun ya buÉ—e su akan Mariya wacce gabadaya ta gama shiga wani yanayi idanu suka hada tayi saurin dauke nata zuciyarta na harbawa da sauri-sauri.
"BASEERA!".
muryar Dr.Aqeel ta doki kunnuwanta sautin na ansawa a kwanyar zuciyarta na buÉ—ewa sosai tsayawa tayi cak! tana mai da numfashi kafun ta dube shi kallonta yake yi da wani irin yanayi wanda ba zata ce ga matsayin da zata ajje shi ba.
"Na anshi soyayarki in har zaki iya bani nima zan baki zuciyata gabadayanta".
Ya fadi yana mai runtse idanuwansa zuciyarsa yake ji tana matsewa da wani irin yanayi mai kokarin haifar da bugun zuciyar sosai yake jin idanuwansa na zafi da raÉ—aÉ—i ko ina na jikinsa yake jin lokaci guda ya tsaya jinin jikinsa yake ji ya shiga gudu da sauri-sauri kwanyarsa yake ji tana hayaki kamar zata kama da wuta.
Mariya kuwa mutuwar tsaye tayi ba abin da take fadi sai 'Innalillahi wa inna ilaihir raji'un' wata katangar tashin hankali ne taji ta rikito mata hannayensa duk biyun ta saka ta dafe kirjinta da take jin yana barazanar tarwatsewa kanta taji ya shiga dokawa kamar zai rabe biyu muryar Dr.Aqeel da taji yana furta kalaman so jin saukar su take kamar garwashi wuta runtse idanu tayi gami da kokarin saita kanta kafun ta taka kafafuwanta da take jin su kamar za su watsar da ita kasa hannayenta ta kamo ta sarke a cikin nata.
Idanuwansu suka sarke da juna murmushi Mariya tayi mai tafe da hawaye.
"Ki amince ke ma Baseera zuciyoyinku su kasance waje daya su rayu tare su zama abu daya har gaban abada".
Girgiza kai Baseera ta shiga yi idanuwanta na kara ballewa da hawaye a hankali ta zare hannayenta gami da duban inda Dr.Aqeel yake wani kallo tayi masa kafun ta juya cikin hanzari tayi cikin gida.
Mai da numfashi Mariya tayi tare da duban Dr.Aqeel shima ita yake kallo kafun ya girgiza kai yana cizon laɓɓa wani murmushi yayi tare da juyawa ya nufi motarsa...
*Kamala Minna*💞💞💞💞
Post a Comment (0)