UKU BALA'I
NA.
KAMALA MINNA.
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร.
BABI NA NA SITTIN DA SHIDA
A hankali take tafiya kanta akasa ga wani zundumemen Hijabi da ta saka a jikinta har yana sharar kasa hannayenta cikin hijabin sai wasa da su take yi.
Kallo daya zaka yi mata ka gano yanayin rashin kwanciyar hankali a tattare da ita fuskarta tayi fari sosai ga wata rama da ta zabga kamar wacce tayi ciwon shekara guda.
Ratso layin take yi tana bin gefe mutane sai binta da kallo suke yi kamar sun ga watan ramadana sosai take jin zuciyarta na zafi da raÉ—aÉ—in wannan fitowar da tayi bata taba zaton zata tsani kanta ba sai a cikin wannan kwanakin da fita ma gagararta take yi in kuwa ta fito an dinga zundenta kenan ana nuna ta da baki wasu har tararta suke suna gaya mata magana son ransu sai dai ba yarda zatayi ita ta jawo wa kanta.
Cikin wannan yanayin ba zato ba tsammani taji an janyo mata hijabi ta baya wata irin dokawa taji gabanta yayi zuciyarta harba da sauri ta dago kanta cikin wani irin yanayi na tsoro da firgici dubansa take yi tun daga kasa har sama bata san shi ba bata san daga ina yake ba.
"Ke ba kya ganin mutane ana yi maki magana kin yi banza da mutane iye wacece ke dan kan...".
Ya lailayo ashar ya dire gami da daga hannunsa daya yana kokari kife ta da mari mai ya gani kuma sai ya sauke yana mai da numfashi.
Sosai tsoro ya bayyana a fuskarta a hankali ta shiga ja da baya tana raɓashi zata wuce don ta lura dan iskan gari ne dan kwaya in ba don haka ba ai bai isa yayi mata wannan cin mutuncin ba ta kyaleshi da sai ta keta masa rashin mutunci amma halin da take yanzu ba zata iya ba duk da zafi da raɗaɗin da zuciyarta ke yi akan zagin kare dangin da yayi mata.
Sake fizgo mata hijabin yayi ganin tana kokarin raɓashi ta wuce ya tsaya dab da ita har suna shakar numfashin juna ba abin da ke tashi a jikinsa sai warin solisho da sukuɗaye kau da kai tayi da sauri gami da toshe hanci wani yinkuri taji zuciyarta ta nayi tana kokarin yin amai.
Ganin abin da take yi masa yasanya shi duban fuskarta da take yatsine masa tana toshe hanci wata irin ashariya ya danna mata gami da cafko hijabin jikinta ya cikuikuye.
"Ke dan kan uban ki ni kike toshewa hanci to ubanki ne ke wari ba ni ba matsiyaciya karuwan banza da wofi".
Yana fadin haka ya fizge hibajin gabadaya daga jikinta daga ita sai zani da ves ga katon cikinta da ya fito sosai wanda haihuwarsa nan kurkusa runtse idanu tayi gami da toshe kunnuwanta wani kuka ne ya zo mata da sauri ta durkushe tana mai sakin sa shi kuwa sai faman danna mata ashar yake yi.
Lokaci kankani mutanan layin duk suka taru aka rasa wanda zai zo ya kwace ta domin kuwa suna tsoron TANGA ba wanda bai sanshi ba a fadin garin nan tattarin dan jagaliya ne kashe mutum a wajansa ba komai bane yayi zaman gidan kaso yafi a lissafa a fitowa dashi.
"In kana yiwa Allah da Annabi ka bani hijabi na".
Ta fadi cikin muryar kuka jikinta sai rawa yake yi wani takaici take ji a zuciya ji take kamar ta hadiye zuciyar ta mace.
Cilli yayi da hijabin da sauri ta rarrafa za ta dauka ya danne mata yatsun hannu ta kurma uban ihu a daidai lokacin motar Dr.Karami ta sanyo kai ganin abin dake faruwa a layin ya sanya shi taka burki ya fito da sauri yana duban mutanan da sukayi cirko-cirko suna kallon rigimar Hafsat da Tanga da sauri ya isa wajan sam bai san wacece ba amma ganin irin cin zarafin da ake yi mata ya sanya shi zuwa ya hankaÉ—e tanga a daidai lokacin ita kuma Hafsat ta dago kai.
'Innalillahi' abin da Dr.Karami ya furta kenan yana ja da baya duban ta yayi kafin cikin hanzari ya isa ya dauko mata hijabin nata ya yafa mata a jikinta cikin sauri duban mamaki yake mata da al'ajabai ganin yarda ta koma kamar ba ita ba.
"Hafsat me ya hadaki da wannan mutumin har yayi miki wannan cin zarafin?".
Girgiza kai kawai take yi zuciyarta na suya hawaye sai ambaliya suke yi mata a fuska numfashi taja mai cike da takaici ta mike kan kafafuwanta ta dubi Tanga sannan ta dubi Dr.Karami a hankali ta raɓashi zata wuce gabanta ya sha yana mai sake tambayarta amma ta kasa bashi ansa kuka kawai take yi abin duniya ya yi mata yawa abin da bata so a gane yau gashi a bainar jama'a kowa ya gani kuma ya san halin da take ciki dama an dade ana zarginta yau dai gashi zargin ya tabbata kowa zai tsine mata da kazamar rayuwar da ta zaɓawa kanta wanda take ciwa mutunci take yi wa kallon banza ta sani yau sai sun zuba ruwa aka sun sha.
Ihun da taji ne ya katse mata dogon tunanin da take yi cikin razana ta juya Dr.Karami ta hanga ya cakumi Tanga sai jibgarsa yake yi gabadaya ya kumbura masa fuska bakinsa har ya fashe yana zubda jini ware idanu tayi mamaki ya sake cikata da sauri ta ja jiki ganin hankalin mutane ya bar kanta ya koma wajan su Dr.Karami.
Tafiya take yi cikin sauri-sauri kamar zata kifa hijabin sai harÉ—e ta yake yi tattareshi tayi sosai ta rike a hannu ta shiga jefa kafarta a duk in da taji ta dira idanuwanta sun kara kaÉ—awa sun yi jajir tana kokarin karya kwanar da zata shigar da ita gida suka yi arba da Abulle kallo ta bita dashi daga sama har kasa kafun ta dauke kanta cike da takaici da bakin cikin wannan rayuwar da 'yarta ta tsinci kanta a ciki Allah na gani tayi bakin ciki tayi takaici tayi kuka sosai a kan wannan lamarin zuciyarta ji take yi kamar za ta soye don raÉ—aÉ—in da take ji tun da abin nan ya faru ta kasa kwanciyar hankali kullum cikin fargaba take akan abin da zai je ya dawo.
"Daga ina kike?".
Ta fadi fuskarta a daure tamau kamar bata taba yin dariya ba ba alamun tausayi amma in da zaka fasa zuciyarta tausayin 'yar ta ta ne makil a cikinta.
Girgiza kai Hafsat tayi hawaye na sake balle mata sautin kukan da take boyewa ya bayyana sosai hakan ya kara tayar da hankalin Abulle da sauri ta riko mata hannu tana mai tambayar ta cikin yanayi na firgici amma ta kasa magana sai girgiza mata kai take yi tana kai hannayenta saman bakinta tana toshewa.
Riko ta tayi sosai ta sanyata gaba suka nufi gida tafiya suke yi gabadayan su zuciyoyinsu na suya musamman Hafsat in ta tuna cin zarafin da akayi mata a bainar jama'a sai ta sake rushewa da kuka kamar numfashinta zai dauke a soro suka ya da zango Abulle sai mai da numfashi take yi ita kuwa Hafsat zubewa kan gwuiwowinta tayi ta rufe fuskarta da tafukan hannayenta tana hadiyar zuciya sai shassheka take yi idanuwan nan nata sunyi luhu-luhu jikinta na faman kyarma.
"Ya isa haka Hafsat dai na kukan fada min abin dake faruwa?".
Dago jajayen idanuwanta tayi ta sauke su kan Abulle cikin wani irin yanayi muryarta na rawa ta shiga bata labarin abin da ya faru da ita a yanzu...
Wani kuka ne ya sake kufce mata ta rarrafo ta riko mata kafa.
"Don Allah Umma ki yafe mani na tuba wallahi ba zan sake ba ina cikin bala'in rayuwa ita cikin kazamar rayuwa wacce ni ne na zama silar faÉ—awa cikin ta don Allah ku yafe mani abin da nayi muku na san ban kyauta muku ba a matsayin ku na iyaye na...".
Da sauri Abulle ta toshe mata baki tana mai duba kofar gidan da soron gidan ganin ba kowa ya sanyata duban Hafsat wacce gabadaya ta fice daga hayyacinta.
"Hafsat kukan ya isa haka nan kiyi shiru karki haifarwa kanki da wata matsalar ciki ne a jikinki wannan kukan kuma da kike yi kina ta da hankalin ki sai ki fuskanci matsala...".
"Nafi kaunar in shiga matsalar da zan mutu akan wannan rayuwar da nake yi na tsani wannan rayuwa na tsani wannan duniyar na tsani kaina...".
Da sauri ta rufe mata baki ita kanta 'yarta ta tausayi take bata kwalla ne suk cika mata idanu da sauri ta kau da kai ta dauke su ta janyo Hafsat jikinta.
"Ya isa haka ki daina fadin haka komai da kika ga yana samun bawa a duniyar nan ƙaddararsa ce haka...".
"A,a Umma wallahi ba ruwan kaddara ni ne sila komai da yake faruwa dani ni ce sila kiyi hakuri Umma ku yafe mani na gaji da rayuwar nan nafi kaunar mutuwa da wannan rayuwar na san ko a wajan Allah ni mai laifi ce nayi abun da yake fushi dani nayi abin da ya kauce hanyar addini na kaico! Umma nasan na aikata kuskure Umma duk abin da kika ga yana faruwa Goggo ce sila ita take sanya ni".
Da sauri ta sake rufe bakinta tana mai girgiza mata kai.
"Nace kiyi shiru ko bana son jin komai daga gareki...".
"Umma ki bari na fadi domin ni dai na san rayuwata ta kare gwanda na fadi komai domin ki rokar min afuwa wajan mahaifina da wanda ya zama ina da hannu cikin faÉ—awarsu hukubar rayuwa".
Nisawa tayi tana mai da numfashi kafin ta gyara zaman da tayi dirshan akasa ɗan cikinta take ji yana ta faman juyawa yana tokare mata kirji laɓɓanta ta ciza gami da runtse idanu hakan da Abulle ta gani ya sanyata ware idanu tana tambayarta ko lafiya amma ta kasa bata ansa sai da ta dauki lokaci a haka kafun ta nisa wasu zafafan hawaye suka zubo mata.
"Duk halin da su Mariya suka shiga da Ummanta Goggo ce sila haka bacewar Abban su Mariya Goggo ce sila ita taja ni muka je wajan wani mutumi a dajin kauyen Sulalla akayi masa kurciya...".
"Innalillahi wa inna ilair raji'un".
Abin da Abulle ke maimaitawa kenan tana dafe kanta da take jin yana kokarin rabewa biyu lokaci guda idanuwanta suka kaÉ—a sukayi jajir wata irin tsanar kanta take ji tana tsanar zaman ta a duniyar nan a daidai wannan lokacin wani takaici ne da bakin ciki ya turnuke ta bata san tsanar da Goggo tayi ma su Bello har ta kai haka ba ta san kiyayyar da take masu takai haka ba.
Mikewa tayi kan kafafuwanta tana duban Hafsat kafin ta fidda hannu cikin zafin nama ta dauketa da Mariya hagu da dama har sai da ta tuntsira ta bugu da bango hancinta da bakinta duk sun fashe suka dinga zubda jini da sauri ta ja jiki zuciyarta na suya ta fice daga cikin soron zuciyarta take ji tana kara ya mutsewa gabadaya taji ta tsani zaman ta a duniyar ina ma numfashinta zai dauke ta rabu da wannan takaicin da bakinciki da uwarta da 'yarta suka cusa mata a zuciya.
Hafsat ganin yarda Abulle tayi mata ta sake rushewa da kuka tana hada kanta da bango kamar ba a jikinta yake ba sai da tayi kuka ma ishinta sannan ta mike tana faman hade hanya ta nufi cikin gidan.
********
Fizgo shi yayi suka isa kofar gidan sai faman cin magani yake yi Alhaji Abdurrazaq ya kwala sallama hannunsa rike da Huzaif da gabadaya ya gama kumbura ji yake yi kamar ya fashe don takaici da bakin ciki wai mahaifinsa ya yi masa irin wannan cin zarafin akan wata banza wacce bai ganin ta da wata kima ko daraja.
Abban su Mariya ne ya fito yana duban su daya bayan daya don bai san su ba Alhaji Abdurrazaq ne yayi masa sallama ya ansa shi cikin yanayi na son karin bayani.
"Kai ne mahaifin Hafsat?".
Bello ya gyaɗa kai yana duban Huzaif ganin yarda aka riƙe shi kamar wanda yayi sata shi abin har dariya ya so ya bashi.
"Sunana Alhaji Abdurrazaq ni ne mahaifin Huzaif wanda ya ci zafin 'yarku ya keta mata haddi".
Zaro idanu yayi sosai yana duban su zuciyarsa yake ji tana bugawa da sauri-sauri wani takaici ya kume shi da sauri ya juya cikin gidan dakin Goggo Marka ya nufa ba ko sallama ya shiga tadda ita zaune yayi ta hada tagumi can gefe kuma Hafsat ce ta dukunkune sai faman numfashi take ja tana saukewa.
"Kunyi baki ku taho suna jiranku"..
Yana fadin haka ya fita daga cikin dakin zuciyarsa na raÉ—aÉ—i gami da zafi ya jima yana takaicin wannan lamarin tun lokacin da ya gane wa idanuwansa ya tambaya amma Goggo Marka ta so ci masa mutunci tun daga wannan lokacin bai sake magana ba sai dai yaje har gidan Abulle ya hadu da mahaifin Hafsat suka zauna sukayi magana a nan ya san komai yayi bakin ciki sosai yayi takaici.
Tabarma ya dauka yanufi soro da ita ya shimfiÉ—a sannan yayi musu iso har lokacin Huzaif na hannun mahaifinsa ya ki sakin sa zama sukayi amma shi Huzaif ya tsaya kerere a tsaye a daidai lokacin suka iso su kuma Hafsat tun da ta hango huzaif ta ji gabanta ya yanke ya fadi wani kallo ta ga ya watsa mata ita ma kallon ta watsa masa daga nan ta kau da kai.
Alhaji Abdurrazaq ne ya muskuta ya dubi Goggo Marka da tayi wiri-wiri da idanu sai hada gumi take yi abi duniya duk yabi ya addabeta.
"Maganar da mukayi kwana ki dake na cewa zan aurawa É—ana jikarki domin kuwa cin zarafin da yayi mata ba zan yarda dashi ba domin ba zan yarda ko 'yata ayi wa haka ba don haka shine nake so ku bashi aurenta domin ba wanda zai aureta bayan shi in kuma ba ku yarda ba ni zan shigar da wannan maganar kotu kuma zan tsayawa Hafsat kai da fata har in ga an kwatar mata hakkinta".
Bello ne ya dube shi sosai yanayin sa ya burgesa yarda ya nuna ba yarda ba akan cin zarafin da É—ansa yayi wa Hafsat ba ya ji dadin haka sosai ko ba komai ya nuna shi mutum ne mai mutunci da sanin ya kamata duban Goggo Marka yayi kafun ya kau da kai.
"Ba sai maganar taje kotu ba ni ina bayanka nima a matsayin uba nake ga Hafsat in dai ta haihu ni na aminci ya aureta sai dai kuma magana daya akwai sharaÉ—i na lura kamar dole kayi wa É—an naka don haka zan masa gargaÉ—i in har ya aureta ya ci zarafinta ko ya kuntata mata wallahi tallahi ni da kaina zan shigar da maganar nan kotu sannan a sake tada tsohon duk wani cin zarafi da yayi mata".
Wani kuka ne ya zo wa Hafsat mikewa tayi ta dubi Huzaif da yayi tsiru-tsiru da idanu sosai take jin har yanzu tana son sa bata jin zata iya rabuwa dashi duk da abin da yayi mata son sa ya zama jinin jikinta wanda hakan har yanzu ya kasa sanyata ganin laifinsa duban su tayi dukkan su kafin ta ja kafafuwanta da sukayi mata nauyi ta shige cikin gida....
*Kamala Minna*💞💞😘😘