UKU-BALA'I 67

UKU BALA'I
            NA.
         KAMALA MINNA.

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
​​WÉ› ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucÉ‘tÉ›, MѳtiѵɑtÉ› ɑɳɗ ɛɳtɛʀtÉ‘iɳ ѳuÊ€ ʀɛɑɗɛʀร​.
  BABI NA SITTIN DA BAKWAI.
Gumi ne kawai ke ta faman keto mata kamar wacce aka juyewa diron ruwa sai faman yamutse fuska take yi tana cizon laɓɓa gabadaya ta gama galabaita ta fice daga hayyacinta lokaci-lokaci take ajiyar zuciya ita kadai tasan bala'i da masifan da take ciki yau kusan kwana uku kenan tana jin ciwon a tsaitsaye amma na yau ya shafe na kwanakin da tayi.
Jikinta har karkarwa yake yi buÉ—e idanuwanta tayi da suke runtse sun kaÉ—a sunyi jajir jijiyoyin goshinta sun fito sosai kamar shirya su akayi kan fatar goshinta hawaye ne suka kwaranyo mata karo na ba a dadi duban dakin tayi gani take yi yana juya mata sama na dawo kasa kasa na dawo sama sake runtse idanun tayi gami da yin wani yinkuri da ya sanyata sakin wata kara mai razanarwa kafun lokaci guda tayi luf! kamar ba ita bace tayi ihun ba.
Goggo Marka ce ta fado dakin cikin hanzari tana dubanta ganin yanayin da take ciki ya sanyata saurin isa gareta rikota tayi tana faman duddubata kafun lokaci guda ta gano abin da ke wakana da sauri ta gyara mata zaman dirshan da tayi tana mai rike mata kafadu da sauri ta fizge kanta daga hannun Goggo Marka tana faman sakin wani wahalallan numfashi hawaye sai ambaliya suke mata a fuska.
Sake kai hannu tayi zata rikota a daidai lokacin cikin nata ya sake juyawa wata irin zabura tayi gami da wancakalar da ita gefe guda kan ta ya hadu da gadon karfen dake gefen su da sauri ta ja da baya tana riko goshinta don sosai ta bugu lokaci guda wajan ya kumbure sosai duban Hafsat ta shiga yi idanuwanta suna kawo kwalla gabadaya ta gama rikicewa kanta gabadaya ya gama shiga duhu tunda Hafsat ta fara nakudar nan a tsaitsaye hankalinta ya kai kololuwa ba ta san lamarin zai kai ga haka ba wai yau Hafsat ce za ta haife musu abin kunya É—an shege na gaba da fatiha ba ta taba dana sanin wannan lamarin da kaico ba kamar yau zuciyarta gabadaya ta gama karyewa da tashin hankali bata san yarda za tayi ba bata san wa za ta kai wa kukan ta a daidai wannan lokacin ba kowa ya juya musu baya musamman Abulle da gabadaya ta dauke musu kafa ta daina bi ma ta kansu ga gidan yanzu ita kanta kunyarsu take yi ta rasa dalili ko da yake ita kadai ta san abin da ta aikata a garesu sosai take jin zuciyarta na kara karye da komai na duniyar ma.
Ihun da Hafsat ta kuma yi ne ya sanyata dawowa hayyacinta dubanta ta shiga yi a tsaye take sai faman ya kice kayan jikinta take yi tana jifa dasu laɓɓanta cikin baki sai faman cijesu take yi kamar ba a jikinta ba idanuwanta a rufe da sauri Goggo Marka ta ja gefe ganin al'amarin ya girmama waje tayi da hanzari tana faman hada hanya Umma ce ta fito ta dubeta ganin yanayin da take ciki ya tabbatar mata ba lafiya isa tayi gareta tana riko hannayenta ba abin da jikinta ke yi sai karkarwa.
 "Habeeba Ban san abin da ke faruwa da Hafsat ba ga ta can cikin dakin sai fizge-fizge take yi".
Zaro idanu tayi tana ambaton innalillahi wa inna ilaihir raji'un da sauri ta saki Goggo ta nufi daki durkushe ta same ta sai faman nishi take yi ga wani mahaukacin gumi da ta hada gabadaya tayi jagaf! duban kasan ta tayi ganin ruwa na kwarara ya tabbatar mata haihuwa ce da sauri ta fice ba tare da ta taba ta ba can ta hango Goggo sai safa da marwa take yi hannu aka hakan yayi matukar bata mamaki yau kuma girgiza kai tayi gami da komawa daki mayafinta ta dauko ta yi hanyar waje.
Tana sanya kai kofar gida ta hango su da sauri ta yo baya tana mai da numfashi ita gabadaya ta manta ma Mariya na waje lekawa tayi a daidai lokacin ita kuma Mariya idanuwanta na kallon kofar gidan don ta ga lokacin da Umma ta fito ta koma da sauri ya fito ta tayi da hannu sannan ta koma cikin soron sai faman kai kawo take yi don yanayin da ta ga Hafsat a ciki yayi matukar tsorata ta ba abin da ta tuna sai lokacin haihuwar Mu'azzam sosai zuciyarta ta karye lokaci guda hawaye su ka zubo mata a daidai lokacin Mariya ta iso ganin Umma da hawaye a fuska ya tsoratar da ita da sauri ta iso gareta tana tambayarta lafiya numfashi ta ja kafun ta runtse idanu jin yarda zuciyarta ke mikata wani yanayi.
"Mariya Hafsat na cikin wani yanayi matuka haihuwar ce na ke zaton lokaci yayi amma yanayin da take ciki yana bani tsoro".
Gaban Mariya ya yanke ya fadi idanuwa a waje.
"Haihuwa!?".
Ta fadi tana dafe kirjinta Umma ta gyaÉ—a mata kai da sauri ta juya tayi kofar gida wajan Dr.Karami ta koma kallo daya yayi mata ya gano tashin hankalin da take ciki da sauri ya iso daf! da ita kamar zai koma jikinta bakinsa har rawa yake yi wajan tambayarta lafiya runtse idanu tayi kafun ta buÉ—e su da kwalla hakan ba karamin kara tayar masa da hankali yayi ba.
"Hafsat ce take wani mataki na haihuwa amma lamarin sai a hankal...".
Tun kafin ta rufe baki yace da ita.
"Muje!".
Da sauri ta juya yana biye da ita suna shiga cikin soro suka tadda Umma wata irin kunya ce ta lullubeta shima Dr.Karami sadda kai yayi kasa don ba su yi tsammanin tadda da juna ba da sauri Umma tayi cikin gida shikuwa sai kokarin buÉ—e baki yake yi don gaishe Mariya ce tayi masa jagora zuwa cikin gidan dakin Goggo suka nufa wacce take bakin kofa lokaci-lokaci take daga labule tana duban Hafsat sai hawaye su zubo mata shar-shar.
Daga labulan yayi ya shiga da sauri ya isa gareta ya dago kanta da ke sunkuye yana kiran sunanta amma ina ta kasa ansawa da sauri ya kalli inda take durkushe shiru yayi na dan lokaci kafun ya mike ya leka waje Mariya ya yafito dake tsaye ita ma cikin yanayin fargaba da hanzari ta iso gareshe.
"Ku kamo ta kawai mu wuce asibiti ina ganin hakan zai fi dace wa don kin ga dai yanzu ko nace zan yi wani abu ba komai na aiki a wajena da zan taimaka mata domin ba a san yarda haihuwa zata kaya ba duk da dai gaf! take da yinta...".
Wani ihu ne ya cika musu kunnuwa da sauri Dr.Karami da Mariya suka faÉ—a dakin a daidai lokacin kan jaririn ya sanyo kai ware idanu yayi kafun yayi waje da sauri cikin sakanni ya dawo hannayensa da safa a ciki duban Mariya yayi wacce ta runtse idanu har da rufe fuska da mayafin jikinta girgiza kai yayi kafun ya isa wajan Hafsat wacce sai faman nishi take yi na wahala da taimakon Dr.Karami cikin ikon Allah Hafsat ta haihu bayan ta gama kururuwa jaririn na fadowa ta ta baje a kasa numfashinta na fita kadan-kadan.
"Mariya anso mani reza wajan Umma".
Da sauri tayi waje ta isa inda Umma ke tsaye sai faman Addu'a take yi idanuwanta sun kaÉ—a Mariya na isa ta dubeta jiki a sanyaye.
"Umma reza ake bukata".
Da sauri ta faÉ—a daki ta binciko sabuwar reza ko buÉ—eta ba ayi ba ta mikata mata zuciyarta na rage fargaba tunda ta ga an anshi reza da alamun an haihu da sauri Mariya ta juya ta koma dakin tana mika masa ya buÉ—eta ya yanke cibi a daidai lokacin kuma mahaifa ta fado dauke jaririn yayi wanda ya kasance namiji kyankyawa dashi dube-dube ya shiga yi.
Mariya ta lura dashi kuma ta gane abinda yake nima don haka da sauri ta kara so ciki dakin can gefe ta nufa inda wata akwaku take budewa tayi ta zaro wani sabon zani da alamun ko daura shi ba a taba yi ba ta mika masa goge jaririn ya shiga yi dashi sai da yayi masa tsaf! Sannan ta sake dauko wani ta mika masa ya nannaÉ—e shi a ciki ya mika mata komawa yayi wajan Hafsat ya dubata ganin yanayin da take ciki ya sanya shi yin waje da sauri Goggo Marka ya duba da ta gama firgicewa can gefe Umma ce ganinsa ya sanya ta yin kasa da kai.
"Alhamdulillah ta sauka".
Yana fadin haka yayi waje da sauri su kuwa har rige-rige sukeyi wajan fadawa dakin duban juna suka shiga yi kafun Umma ta shiga tsaftace dakin ta gyarawa Hafsat jikinta sosai ta tsorata ganin yarda ta karu a kasan ta hakan ya fadar mata da gaba duban Mariya tayi wacce itama idanuwanta na kanta gyaÉ—a mata kai tayi ba tare da tace komai ba a daidai lokaci Dr.Karami ya yi sallama suka ansa shi shigowa yayi hannunsa dauke da dan karamin kwanati (First Aid Box) cikin taimakon Allah yayi mata dinkin inda ta karu gami da allurai duban Umma yayi bayan ya ajje kunyar gefe.
"Jininta ya hau sosai kar ku saka mata ruwan zafi yanzu a dai samu mai dumi ta wanke jikinta dashi sannan ga wannan magangunan...".
Ya mikawa Mariya ledar yana mai cigaba da fadin.
"In ta ci abinci sai ku bata ta sha tsarin na nan a ciki Mariya sai ki duba ki gani Allah ya raya ya É—ayyaba".
Yana gama fadin haka ya mike yana duban Hafsat wacce ta dawo hayyacinta idanuwanta sai zubda hawaye suke yi ta kasa kallon kowa ma a cikin dakin yana kokarin fita yaji muryar Umma nayi masa godiya gami da Addu'a murmushi yayi gami da cewa 'Ameen' azuciyarsa sosai yaji dadin addu'ar a ransa.
*****
A wulakance ya anshi jaririn da ta mika masa sai faman cin magani yake yi yana hararar Hafsat da kanta ke kasa ita kadai ta san yanayin da take ciki tunda ta haihu yau kwana uku kenan gabadaya taji komai ya canza mata bata jin dadin komai rayuwar ta take ji gabadaya ta gaji da ita zuciyarsa sai zafi take yi ruhinta kamar zai kama da wuta.
"Meye haka Huzaif ya naga kana riƙe shi a wulakance ne kamar ba jininka ba ban son rashin hankali fa".
Mahaifiyarsa dake zaune ta fadi dama tunda da ta mika masa jaririn ta ga rikon da yayi masa ranta ya É“aci sosai ji take yi kamar ta mike ta kwada masa mari don sosai take jin haushin sa tun a gida don da kyar da dole sannan ya zo wajan ganin jaririn da Hafsat ta haifa masa.
Sake turbuÉ—e fuska yayi yana dubanshi ya wullawa Hafsat wani mugun kallo cikin tsana da takaici abin da ke kara bata masa rai yarda jaririn yayi kama da shi sak! kamar kak'i yayi ya ajje hakan na kara kona masa zuciya domin kuwa bashi da wata mafita ko yace ba shi yayi ba ina ma zai ce bashi yayi ba ba yarda za ayi ba yarda ya ga kowa na gidan su ya dau zafi dashi akan Hafsat har sun fi kaunar ta dashi a yanzu.
"Ka tafi ka kaiwa mahaifin naka shi ya ga jikansa".
Ta sake fadi cikin ba da Umarni gabanshi yaji ya yanke ya fadi tunawa yayi da mutannan da suke soro a zaune ga Abban su Mariya ga nasa ga kuma mahaifin Hafsat wani irin ihu yaji kwanyarsa tayi saura kadan jaririn ya suɓuce a hannunsa da sauri ta kai hannunta ta na cilla masa mugun kallo.
"Wai mai yasa Huzaif kake son bata min rai ne kai yanzus aboda rashin imani É—an naka zaka yasar saboda wata banzar akiÉ—a taka da bata da madafa ko mafaka kasan Allah zan bata maka rai in baka yi wasa ba kuma ka rike shi ka mika musu shi tun kafin na bata maka rai".
Da sauri ya juya ya fita ta bishi da mugun kallo kafun ta juya da idanuwanta ta dubi Hafsat dake ta faman zubda hawaye.
"Kin ga irinta ko Hafsat duk macen da bata kama kanta ba har namiji yayi galaba akanta tana cikin masifa duk son da namiji zai nuna miki duk kaunar da namiji zai ce zai miki karki sake ki saki jiki dashi har wani abu ya shiga tsakanin ku domin duk namijin da ya kasance da mace ba tare da aure ba har ta yarda to wallahi ya daina ganinta da daraja da kima kenan yanzu dai kin ganewa idanunki wani uba ne zai dinga wulakatar da ɗansa har haka in da kunyi hakuri kunyi aure ba ku keta hakkin Allah ba duk haka ba zata faru gareku ba kuna da son zuciyarku so na rufe muku ido har kuyi sake Shaidan yayi tasiri akan ku kina dai kallon yarda Huzaif yake yi miki a yanzu wanda ni sam bana jindadin haka don ba zan goyi bayan sa ba ina so ki kwantar da hankali ki ajje komai a gefe ki fuskanci rayuwa ki raini ɗanki sannan ki dauki komai a matsayin ƙaddara a rayuwarki ta duniya kuma nayi miki alkawari in har auren nan naku ya tabbata ni zan tsaya miki ba zan taba yarda Huzaif ya cutar dake ba ko yaci zarafin ki".
Dago idanuwanta tayi ta dubi Mahaifiyar Huzaif idanuwanta na kara rikicewa da zubda kwalla zuciyarta take ji tana kara yamutsewa wai ita ce yau namiji ke wulakanta wa bayan shine ya yi mata cin zarafin da ya zama bala'in rayuwa a gareta gaban kowa yake yi mata kallon tsana da k'yara É—an cikinta da ya kasance jininsa shima bai tsira ba kaicon wannan rayuwa duban tsakar dakin tayi niki-nikin kayan da su kawo mata take bi da kallo kafun ta kau da kai ta cikin yanayi na zafin rai da kaicon wannan yanayi da ta tsinci kanta a ciki.
Huzaif sai da ya gama safa da marwa a tsakar gida domin kuwa kunya ce gabadaya ta gama baibaye shi ya kasa zuwa ya kai musu jaririn duk abin da yake yi Mariya na laɓe a labulan dakin su tana kallon shi ji take yi kamar ta fita ta rufe shi da duka don takaici yarda taga yana duban jaririn yana harararsa ya bata haushi da sauri ta dage labulan ta fito wani firgita yayi don ya dauka mahaifiyarsa ce ta fito har zai kwasa da gudu jin gyarar muryar da Mariya tayi ya sanya shi tsayawa yana dubanta kallon sa ta shiga yi zuciyarta na zafi da raɗaɗi kafun ta dauke kanta ta koma cikin dakin fakare yayi da idanu yana kallonta kamar ya ga sabuwar halitta zuciyarsa yaji ta buga da wani irin yanayi kwanyarsa na ansawa runtse idanu yayi sannan ya buɗe a hankali ya taka kafafuwansa ya shiga cikin soron gabansa na yankewa yana faduwa yana shiga gabadaya suka zubo masa idanu ji yayi kamar ya nutse cikin kasa don kunya kafafuwansa sai harɗewa suke yi ji yake yi in ya kara taku daya zai baje a kasa mahaifinsa ne ya dubeshu da mugun kallo kafun ya ce dashi cikin daga murya mai cike bacin rai.
 "meye haka zaka zo ka tsayawa mutane a kai in ba zaka iso ba ka fita mana".
Da hanzari ya iso gareshi gami da mika masa jaririn ansa yayi ya shiga dubansa kafun ya dago kai ya dubi Huzaif sak! kamar su ta bayyana a ransa ya dinga ina ma ina ma ace da aure ka samar masa wannan jikan da sai yafi kowa farinciki da jindadi a rayuwarsa amma ƙaddara ta rigayi fata.
 "Ƙayi masa huÉ—uba ne?".
Ya fadi yana kallon Huzaif da yayi kasa da kai abin duniya duk yabi ya dame shi dago idanuwansa yayi ya sauke a na mahaifinsa yana girgiza kai.
"Wa kake so to yayi maka wa ka mai da dan aikin ki haka za ka haifi 'ya'yan baka yi musu huduba don baka san darajar su ba?".
"Ayi hakuri Alhaji miko min shi nayi masa ni zan wakilce shi".
Abban Mariya ya fadi da murmushi a fuskarsa.
"Da kan sa zai yi masa ko nan gaba ya koya".
"Ba za ayi haka ba".
Ya sake tarar sa, shi dai Mahaifin Hafsat abin duniya ne duk ya addabe shi ya kasa cewa kala sai bin su yake yi da kallo yana wurgawa Huzaif mugun kallo ji yake yi kamar ya mike ya rufe shi da bugu.
"Wani suna za a saka masa?".
"Tambayi shi rasa kunya din".
"Hakuri za kayi".
"Saka masa Muhammad Huzaifa".
Dukkansu suka dube shi cike da mamaki Huzaif kuwa daskare wa yayi a kasa yanayin da suka ga Fuskar Alhaji Abdurrazaq ba wasa ba wanda ya tanka shi Abban Mariya yayi masa huduba sannan ya mika wa Mahaifin Hafsat amma sai ya kau da kai ya ki ansa ba yarda ya iya dashi ya mikawa Huzaif shi.
"In tayi arba'in za a daura musu aure in Allah ya kaimu".
Alhaji Abdurrazaq ya fadi ya harara Huzaif da ya mike jiki a sanyaye ya koma cikin gidan.....
*Kamala Minna.*💞💞💞😘😘😘
Post a Comment (0)