UKU-BALA'I 68

UKU BALA'I
            NA.
    KAMALA MINNA.

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
​​WÉ› ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucÉ‘tÉ›, MѳtiѵɑtÉ› ɑɳɗ ɛɳtɛʀtÉ‘iɳ ѳuÊ€ ʀɛɑɗɛʀร​.
  BABI NA SITTIN DA TAKWAS
  *BAYAN SATI UKU*
Kai kawo kawai take yi tsakar dakin gabadaya ta gama firgicewa yau sati guda kenan ta rasa gane kanta tunda Dr.Karami ya sanar da ita zai turo iyayensa ta dauka abun wasa ne sai taga ya tabbata hakan ba karamin kara rikita mata lissafi yayi ba musamman da Abba ya turke ta akan tsakaninta da Dr.Karami duk da ya san komai amma sai ya matse ta sosai domin ta tabbatar masa da cewa Dr.karamin ne zabin ta ita dai Umma yar kallo ce har sukayi kidin su sukayi rawar su fata alheri kawai take yi don ta fi kowa farinciki da jindadin wannan lamari.
"Wai ke lafiyarki kalau kuwa cikin kwanakin nan gabadaya na rasa gane kan ki?".
Umma ta fadi tana duban Mariya numfashi ta ja kafun ta daga laɓɓanta tana koƙarin yin magana wayar Umma dake yashe ta dau kara tsuke bakinta tayi tana duban wayar ganin su Baseera ya sanyata saurin daukar wayar jiki a sanyaye.
"Mariya kina ina ne?".
Muryar Baseera ta karaÉ—e mata kunne ba tare da tayi sallama ba yanayin muryarta da ta yi maganar da alamun tsoro da fargaba numfashi Mariya ta ja kafun ta nisa.
"Ina gida ya akayi ne?".
"Wai kin ji yau za a kawo lefe inji Dr.Aqeel jiya yake sanar dani da daddare kin san shekarar jiya iyayensa sun zo tambaya".
'Innalillahi wa inna ilahir raji'un'.
Mariya ta fadi a zuciyarta tana mai runtse idanuwanta kanta taji yayi mata wani gingirin gim! kamar an daura mata dutsen dala da goron dutse zuciyarta taji ta matse da wani irin yanayi komai take jin sa yana sauya mata ji take yi kamar ba ita ba komai take ji tamkar a mafarki yake faru.
"Meye kuma haka ya za ayi kiyi shiru kuma kina jin ana zuke mata kudaÉ—en wayar ta ta".
Umma ta fadi ganin yarda Mariya tayi mutuwar tsaye wayar a hannunta amma ta kasa furta komai kwanyarta take ji tana hautsewa da tashin hankali lamarin ne take ganinsa kamar ba gaske ba kalmar 'lefe' ce kawai ke mata hayaniya aka.
"Nima haka take Baseera yanzu haka shirye shiryen da nake gidanku zan taho don bana son...".
Shiru tayi tana duban Umma da ta kafe da idanu cike da zargi kau da kai tayi ta fara jan kafafu za ta fice daga cikin dakin Umma ita dai ido take watsa mata tun da aka fara maganar bikin nan na ta ta rasa gane kan 'yar ta ta komai nata ya sauya ga wani sanyin jiki da yake damunta ita dai ba ta ga abin damuwa a wannan lamarin ba abin farin ciki ya same ka amma gabadaya kuma sai ka sauya kamar mara lafiya.
"...Uhmm fa kin san mi nima fa yau za su kawo anya Dr.Karami ba hada baki sukayi da Dr.Aqeel ace daga fara magana sai su zage suna kokarin rusa mana rashin mutunci nifa Allah na gani ban shirya ba...".
Fizge wayar taji anyi da sauri ta juya Umma ce a tsaye fuskarta a hade kamar bakin hadarin dake kokarin zubda ruwa kasa tayi da kanta ganin irin kallo da Umma take yi mata nuna ta tayi da dan yatsan hannunta tana kokarin yin magana Bello ya shigo bin su yayi da kallo kafun ya dubi Mariya da kanta ke kasa.
"Me kuma ke faruwa naga kun yi cirko-cirko da ku haka kamar zakaru?".
Ba wacce tayi magana a cikin su Umma ta juya da sauri ta koma cikin dakinta duban Mariya yayi.
"Ke me kika yi mata na ga ranta a É“ace?".
Girgiza kanta tayi idanuwanta na kawo kwalla.
"Ni ba kuka nace kiyi mani ba kin san natsani wannan hawayen naki ko don haka ki shafe su ki fada min abin da ke faruwa".
"Ni ban yi mata komai ba Abba kawai dai...".
Shiru tayi tana susar gefen kuncinta kafun ta dago kai ta dube shi shima ita yake duba kafun ya juya yayi cikin dakin Umma ya hango zaune ta zabga tagumi da sauri ya isa gareta zauna gefen ta gami da cire mata tagumi.
"Me kuma ya hadaki da 'yar taki yau abin da ban taba gani ba?".
Kallonsa tayi kafun ta dauke kai tana ajiyar numfashi.
 "Mariya har yanzu hankalin ta bai gama zama daidai akanta ba in ban da rashin hankali da wauta bayan an gama magana meye kuma na son mai da hannu agogo baya wai maganar nan fa ta kawo lefen take tayi wa kunci alamun bata son wai yayi wuri kaji fa shiririta".
Murmushi yayi kafun ya shafi haɓarsa.
 "Da sauki in ba auren ne tace bata so ba duk labarin kanzon kurege take son biya miki ba wani abu ba".
Ya fadi yana mikewa kan kafafuwansa dubansa tayi da mamaki.
"Au haka ma zaka ce Abban Mu'azzam kasan dai halin yaran nan abin da kake ganin ba komai ba sai ka ga su sun girmama shi".
Tsayawa yayi da tafiyar da yake yi ya juyo ya dube ta yana gyaÉ—a kai.
"Bana so kina saka kokwanto a ranki don Allah ki daina in Allah ya yarda ba abin da zai faru sai alheri".
GyaÉ—a kai tayi gami da daga kafada tana mai da kallon kan Mu'azzam dake ta faman sheka barcin sa hankali kwance tashi tayi ta shiga kokarin gyara dakin domin ta san yau dai gidan sai abin da hali yayi ta san yanzu haka iyalan su Baffa da wasu tsirarun dangin Abban su Mariya na hanya domin su ne za su zo har da su za a anshi lefen.
Fita tayi can ta hango Mariya tana cigaba da gyaran gidan ba ta yi mata magana ba ta bi sahunta lokaci kankani duk suka kammala komai nan suka hau girke-girken tarar baƙi.
Sosai Mariya ta gaji domin ba su gama aikin ba sai wajan daya kuma karfe biyu yan kawo lefen za su zo so take yi ta bar gidan amma Umma ta kasa ta tsare ta hana ta sak! ji take yi kamar ta daura hannu aka ta kurma ihu musamman yarda ta ga Umma ta tsare mata gida ko magana kuma ba tayi mata tun da safen.
Zaune take ta zabga tagumi sai faman tunanin yarda zata bar gidan take yi gidan su Baseera ta so zuwa to ita ma gashi an yi mata bazata an kwakuya mata rashin mutunci tana tunanin hadin bakin su ne Dr.Aqeel da mutumin nata.
*******
Horn taji anayi mata sam! bata dauka da ita ake ba sai da taji abin yaki ci yaki cinyewa sannan ta tsaya gami da waigowa motar da ta gani ne hakan ya sanyata tsuke fuska tana kokarin cigaba da tafiyarta.
Da sauri ya kashe motar ya fito da hanzari har da gudu gudu ya isa gareta gabanta ya sha yana kure ta da idanu ita mata kallonsa take yi kafun ta kau da kai tana jin yarda zuciyarta ke bugawa da sauri-sauri.
 "Ina zaki je bayan kin san dai yau rana ce ta musamman".
harararsa tayi kafun ta dauke kanta hakan da ya gani ya so bashi dariya don ya san laifin sa yayi mata abun da ba ta san dashi ba shi kasan kasa rike kan sa yayi tun da aka yarje masa an bashi ita gabadaya ya ji kamar nan da wani lokaci wani zai kwace masa ita musamman in ya tuna irin TAQADDAMA da aka kwasa.
 "Ba laifi na bane laifin mutumin Æ™awarki ne".
Da sauri ta dube shi kafun ta motsa laɓɓanta kamar mai son yin magana amma ta fasa.
GyaÉ—a kai yayi fuskarsa da murmushi.
 "Har kun gama rigimar taku ne?".
Ta tambaye shi idanuwanta cikin nashi dariya ya tuntsure da ita kafun ya sake dago kansa ya dube ta.
 "Rigima ai dama kece sanadi tun da kuwa kika yi masa tukuici Æ™awarki komai ya koma normal tun ranar da abin ya faru ya sanar dani komai kuma mun yafi juna SHARRIN SO ne kawai dama ba wani abu ba".
Da mamaki take dubansa kafun ta saki murmushi tana mai rufe fuskarta da hannayenta.
 "kin rufe fuska mana tunda kin hada zuciyoyi masu cike da ingantacciyar ABOTA suna rigima kamar mu abokai tun na makaranta amma ace a SANADIN 'YA MACE mun samu matsala abinda ya bani mamaki sannan na kara yarda SO ba abin da bai zai haifarwa zuciya ta aikata ba".
ya fadi yana juya idanunsa da suke kara rikita mata lissafi.
"Ina kika nufa naga kin fito a daidai wannan lokacin?".
Juyawa tayi ta dubi Kofar gidan sannan ta dube shi tana yatsine fuska.
"Ba zan iya zama bane su Baffa sun iso fa kuma hayaniya yayi yawa ni kuma bana so bayan haka kuma nasan yanzu...".
Sai kuma tayi shiru ta kasa karasa abin da tayi niyyar fadi tana mai sunne kai kasa murmushi yayi don ya gano in da zancen nata ya dosa.
 "Zo muje ki raka ni tunda zaman gidan ne bakya so".
Da sauri ta dube shi idanuwanta da wani irin yanayi kafun ta shiga girgiza kai alamun a,a shima mamaki ne ya cika shi ganin abin da take yi masa.
 "Saboda me ba zaki ba, ba fa nisa za muyi ba?".
"Ka bar shi kawai ai ba dadewa za suyi ba nima makota zan shi akwai abin da zan yi ne".
Ta fadi tana mai kokarin wuce shi ta tafi shan gabanta ya sake yi yana dubanta cikin idanunsa da suke kokarin sanya mata gajiya a jiki.
 "Baki yarda dani bane ko meye nufin ki?...ko da yake zo mu je to na kai ki gidan mutuniyar taki na san zaki fi sake wa a can din".
 Yana son takura mata ba ta son abin da zai dami zuciyarta so take yi ta tafi ta huta ko ta samu hutun kwakwalwarta don ta san tabbas in tabi Dr.karami surutunsa ya isa ya hanata sukuni ko kuma yayi ta yawo da ita ba su can shagon ba su can wajan shan Icea Cream ita kuma bata son yawa ce ya wacen nan.
 "Ina yini Dr.Karami".
Kamar daga sama suka juyo muryar daga bayan su da sauri suka ji ya macece sanye da nikaf a fuskarta bayan ta da goye kallo daya Mariya tayi mata ta gane wacece kau da kai tayi a daidai lokacin ita kuma ta dage nikaf din Hafsat ce gabadaya ta rame tayi zuru-zuru da ita ga wani baki da ta kara yi kamar wacce ta jima tana jinya duban ta sosai yayi kafun ya gane ta murmushin yake ya saki yana ansawa.
 "A,a Hafsat daga ina haka da ranar nan".
Murmushi tayi itama na yake duk ta sha jinin jikinta domin kuwa gabadaya kunyar Dr.Karami take a yanzu.
 "Wallahi Huzaif na kai asibiti ba shi da lafiya ".
 'Huzaif' Ya fadi a ransa sunan nayi masa yawo kwanya kafun ya dawo tunaninsa ya sake yi mata magana har tayi gaba duban Mariya yayi wacce takure shi da mayun idanuwanta ta na jefa masa kallon mai dauke da yanayin bacin rai kau da kai yayi shima a zuciyarsa dariya yake yiwa Mariya ganin yanayin da ta nuna masa yaji dadin haka sosai ko ba komai ya hango kauna gami da kishinsa a tsakar idanuwanta.
 "Kallon na meye haka?".
Ya fadi yana murmushi hakan ya kara tura mata haushi sake tsuke fuska tayi tana kokarin wuce shi da sauri ya kai hannu zai riko mata hijab mai ya gani kuma yayi saurin janye hannunsa zuciyarsa na bugawa ba zai taba manta yarda suka kwashe da ita ba lokacin da ya rike ta bisa kuskure in kuwa ya sake maimaitawa a yau ya san zata dauka a gaske yayi Allah kadai ya san hukuncin da za tayi masa numfashi yaja daidai lokacin da yaji tsayuwar motoci ita kanta Mariya tsayawa tayi da tafiyar da take yi ta juyo ganin motocin sunyi parking kure su tayi da idanu gabanta taji ya yanke ya fadi ta tabbata yan gidan su Dr.Karami ne masu kawo lefe don haka da sauri ta juya ta dube shi ganin yana yi mata dariya har da gwalo ya sanyata turo baki gaba tana harararsa kafun ta juya da sauri ta fada gidan makotansu.
Shi abin ma dariya ya bashi bai san wacce irin kunya bace Mariya gareta ko da yake jinin fulani in yayi duba da Umma sak! ita ma haka take da sauri ya shiga motarsa ya ja ya isa inda motocin suke mazaje ne ziryan ba Mace ko daya a cikin su sune yan kawo lefen.
Gaida su yayi bayan ya fito daga cikin mota wani kanin Hajiyarsa ce ya kalle shi cikin harara.
 "Au wai ke dama kana nan unguwar ko biye damu kake?".
So sa kai yayi kafun ya dubi sauran yan uwan mahaifin nasa da sukayi masa kuri da idanu suna dariya.
 "Kawu Sako fa na kawo mata shi...".
 "Sako eh tabbas na ga sako ai sai ka zo muje Lefen ma mu kai da kai tare ko".
Gabadayan su suka kwashe da dariya a hankali ya ja da baya kansa akasa ya fada cikin motarsa ya yi mata Key sannan ya leko da kai waje.
 "Kawu sai kun dawo a dai yi duk abin da ya kamata surukar taka ta musamman ce".
Ya fizgi motar da gudu yana faman sheka dariya suma dariyar suke yi kafun su bude kofofin wata mota kirar Benz sabuwar dalla sai daukar idanu take yi suka shiga sauke tika-tikan akwatina masu kyau da tsari har set biyu kallo daya za ka yi musu ka kasa dauke idanuwanka domin sun hadu iya haduwa tsayawa masalta su wani cin lokaci ne da nuna kauyanci...
*Ina Yan Team din Dr.Karami da Mariya lokaci fa ya zo ku zo ku fara shirye shiryen biki ku fidda mana da Anko domin biki mai ansa sunansa biki za ayi*
  *Haka ma Yan Team din Dr.Aqeel da Baseera Ku shirya shagalin ku*😀😀
A gefe guda ga bikin su *Hafsat mai jego da angon karni Huzaif...lol*😀😀
 *Kamala Minna.*💞💞😘😘😘
Post a Comment (0)