UKU-BALA'I 69

UKU BALA'I
             NA.
        KAMALA MINNA.

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
​​WÉ› ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucÉ‘tÉ›, MѳtiѵɑtÉ› ɑɳɗ ɛɳtɛʀtÉ‘iɳ ѳuÊ€ ʀɛɑɗɛʀร​.
  BABI NA SITTIN DA TARA.
Dubansa take yi zuciyarta na kara mikata wani mataki na son sa duk cin mutunci da wulakanci da yake yi mata sam bai damunta kamar yarda yake bayyana kiyayyarsa gareta sosai take jin zuciyarta na suya ruhinta da kwanyarta ja take kamar za su kama da wuta numfashi take ja a hankali idanuwanta sai zubda hawaye suke masu zafi ta duɓe shi a karo na ba a dadi hannunta rike da Huzaif.
 "Huzaif yau ni ce kake wulakanta wa Huzaif yau ni ce kake ciwa mutunci bayan kai ne silar faruwar komai gareni...".
Wani banzan kallo yayi mata kafun ya mika mata Huzaif dake hannunsa dama duk ya gaji da rikonsa ji yake yi kamar an daura masa ƙaya a hannu in ba don Hajiyarsa tayi masa umarni da cewa ya dinga zuwa ba in ba haka ba zata bata masa ba abin da zai kawo shi wajan banzar yarinyar nan da bai san ma ya akayi ya fara kulata ba a yarda yake na matashi mai jini a jika amma ace shine yake tsayawa da wannan kazamar har za ta zama matar auren sa nan da sati guda.
Wani kunci ne ya mamaye zuciyarsa ji yake yi kamar ya sheka ta ta mutu kowa ma ya huta.
"Karki sake daura min laifi don bani na kawo ki ba ke kika kawo kan ki gareni sannan ban yi miki dole ba balle kiyi tunanin ko na KETA HADDI a gareki".
Runtse idanu tayi tana jin yarda maganganunsa ke ratsa zuciyarta da kwanyarta suna haifar mata da wani yanayi mai kokarin kona mata duk wani sassa na jikinta girgiza kai ta shiga yi numfashinta sai kai kawo yake yi kamar zai dauke.
"Ki rubuta ki ajje ko da kin aure ni wallahi ba zan taba son ki ba bana kaunar ki daidai da kwayar zarra a zuciyata domin ni ba zan auri jahila...".
 "Ya isa haka Huzaif ya isa nace maka!".
Hafsat ta fadi cikin karaji tana toshe kunnuwanta da take jin maganganun kamar za su fasa mata su kuka ne ya sake kwace mata duban sa tayi.
"Ba sai ka gaya min baka kauna ta ba sannan ba sai ka gaya min ka tsane ni ba amma ka ajje wani abu a ranka wallahi tallahi Huzaif sai na aure ka kuma wallahi sai ka so ni a yarda nake don ba wanda ya bata min rayuwa sai kai ba wanda ya jefani cikin bala'i sai kai don haka wallahi tun da muka dama tare da kai sai mun shanye sai dai in an kai ni gidanka ka dinga yagar nama kana watsarwa".
Ta fadi tana hadiye kukan Huzaif ta saba abaya ta goyashi sannan ta sanya hannu ta shafe fuskarta da hawaye suka ki tsayawa da zuba wani abu ta hadiye mai tauri kafun ta dubi Huzaif da yayi fakare yana kallonta wani kunci da takaicinta na kara turawa zuciyarsa bakin ciki murmushi ne mai ciwo ya wanzu a fuskarta.
"Kasan Allah Huzaif sai na aure ka a baya ina jin takaicin cin mutuncin da kayi mani bayan ka keta mani haddi amma tun da abin naka haka ne MU ZUBA MU GANI shege ka fasa".
Da sauri ta juya zata tafi sai kuma ta tsaya zuciyarta na bijiro mata da wani tunanin juyowa tayi ta dube shi da mugun kallo a fuskarta goyon ta kwance sannan ta iso in da yake tsaye mamaki duk ya gama cika shi ganin yarda lokaci guda Hafsat ta juye kamar ba ita ba gaban motarsa ta isa ta ajje jaririn kafun ta dube shi hawaye na kara balle mata.
"lokacin da muka hadu da kai ni kadai ka gani ba tare da wannan jaririn ba".
Ta nuna Huzaif da yake ta faman wutsul-wutsul da kafa kafun lokaci guda ya balle da kuka.
"ka dauke shi don bani ni ne ya kamata na rike shi ba a halin yanzu ka je kai ma ka É—anÉ—ana abin da ake ji".
Tana gama fadin haka ta juya da sauri ta shige cikin gida kunnuwanta sai faman ansa sautin kukan É—anta suke yi wani irin yanayi take jin kanta a ciki gabadaya duniyar take ji ta sure mata ina ma ace za ta mutu da sai tafi kowa farin ciki.
Kwalla mata kira yake yi amma ina ko ta kan sa ba ta bi ba juyawa yayi ya dubi Huzaif ganin yarda yake rusar kuka gabadaya yaji ya firgice da sauri ya isa gareshi ya dauke shi yana jinjigashi amma ina kamar ana kara rura wutar kukan nashi waige-waige ya shiga yi amma ba kowa a layin da sauri ya isa kofar gidan ya tsaya idanuwansa sunyi tsuru-tsuru gabadaya kwanyarsa yake ta rikice kafun ya ankara yaji saukar fitsari a jikinsa wani ihu ya saki yana daga shi daga jikinsa fitsari sai tsartuwa yake yi hakan ya kara bata masa rai ya shiga yatsine fuska ji yake yi kamar yayi cilli da jaririn amma ya kasa ya leka soron yana zundumawa Hafsat kira amma ina kamar yana kiran dutse tana jin sa amma tayi banza dashi zuciyarta kuwa sai zafi take yi in ta jiyo kukan É—an nata ji take yi kamar ta tashi ta anso shi amma in ta tuna abin da Huzaif yayi mata sai ta komata zauna tana rusar kuka.
Mota ce kirar Benz tayi Parking a daidai kofar gidan su Mariya da Baseera suka fito daga can gefen direba kuma Dr.Karami ya fito fuskarsa da yalwataccen yanayin farin ciki duban su yake yi su duka kafun ya sauke akan Mariya da tayi kasa da kai Baseera kuwa sai zabga dariya take yi tana duban Dr.Karami da yake harararta.
"Malama ba ma son ranin sense ga ya za ayi za ki dinga mana dariya".
Ya karashe shima dariya na kokarin kwace masa a daidai lokacin Mariya ta dago kai ta dube shi tana watsa masa harara.
"Malama zo mu wuce ciki in kun gama dariyar".
Mariya ta fadi tana duban Baseera Dr.Karami ne ya miko musu jaka mai dauke da IV Baseera ta ansa tana dubawa kafun ta mikawa Mariya.
"Naki yafi nawa kyau gaskiya".
"Ai sai ki sauya".
Ta fadi tana harararta sake tuntsirewa da dariya Baseera tayi kafun ta ja hannun Mariya su fara tafiya.
"Au ko sallama babu da yake nayi muku abin da kuke so ko, ai ko ni direbarku ne sai haka inda na san haka Allah sai dai naki Dr. ya zo yayi wannan yawon dake amma saboda son kai ya tashi ya gudu ya barni da iyayinki".
Dariya ta sake yi kafun ta dubi Mariya da gabadaya ta ki sakin jikinta sai faman hade fuska take yi.
"Kai ka san in da ba abin da ya sanya shi gaba ba abin da ba zai mani ba kuma ko da ka tafi dani ai na taimaka maka ita mutuniyar taka mai tayi bayan zaman shiru komai ni nake yi".
Tana gama fadin haka ta ja Mariya sukayi gaba bin su yayi da kallo zuciyarsa na mika shi wata duniya ta musamman sosai yake jin zuciyarsa na kara narkewa da wani irin yanayi game da Mariya ji yake yi kamar ya sake janyo lokacin bikin ya dawo nan da kwana biyu ba sati guda ba.
Sai da ya ga shigewarsu sun sha kwana sannan ya shige motarsa cike da farin ciki ya ja ya tafi.
Turus suka tsaya a kofar gidan ganin abin da ke faruwa Baseera ce ta dubi Mariya baki na rawa.
"Mugun abu Mariya me nake shirin gani?".
Wani yaƙe Mariya ta saki kafun ta dubi Huzaif da yayi wujiga-wujiga dashi gabadaya jikinsa ya gama bacewa da fitsari da kashin ɗan nasa fuskarsa kawai zaka kalla ya baka tausayi don gabadaya yayi laushi ji yake yi kamar ya kurma ihu don takaici sam bai lura da su Mariya ba sai da suka iso kofar gidan za su shiga ya gansu ji yayi kamar ya nutse a kasa don kunya duk sai yayi wani wiƙi-wiƙi dashi kamar wanda yayi wa sarki karya Baseera kuwa abin dariya ya bata amma sai ta kanne dama ta dade tana jin haushin Huzaif tun lokacin da ta samu labarin abin da ya faru tana kokarin yin magana taji Mariya ta fizgi hannunta sun faɗa soro da sauri ya bi bayan su yana kwalawa Mariya kira cikin wani irin yanayi na rawar murya tsayawa tayi cak! batare da ta juyo ta dube shi ba.
"Don Allah taimaka ki mikawa Hafsat É—an nan tun dazu yake ihu na kirata amma ta ki zuwa ban san mai take nufi ba".
Baseera ce ta juyo ta dube shi a wulakance.
"Meye nata ita da kake cewa ta anshe shi ta kai shi ai na dauka gidan ba bakon ka bane ko ai sai ka shiga ka kai shi ba ma wannan ba ai na dauka É—an ka ne ka ga ai kaima zaka iya zama ka rarrashe shi ba dole sai uwarsa ba".
Runtse idanu yayi domin sosai yaji maganganun Baseera sun taba masa zuciya amma sai yaki nuna haka a fili sai ma murmushi yaƙe da yake ta faman yi yana sanɗa kai domin ba abin da yafi bukata a yanzu illa a raba shi da yaron nan don ya gama firgitashi gabadaya musamman in ya dubi jikinsa yarda ya baci duk abin duniya ya bi ya dame shi.
 "Don Allah na roke ki".
Ya fadi da muryar tausayi ganin Baseera ta ja hannunta za su shige juyowa tayi ta dube shi.
 "ka bari za a turo maka ita sai ta anshe shi da kanta ban san abin da ya hada ku ba har ta bar É—an nata a nan ba zan asa taje taga baÆ™ina ba".
Tana fadin haka ta juya suka shige shi kuwa ji yayi kamar ya kurma ihu don takaici sai ya tafi kamar zai shiga cikin gidan sai kuma ya dawo da baya.
Suna isa cikin gidan suka hangota can kofar daki ta hada kai da gwuiwa sai shsashekar kuka take yi Baseera ta dube ta ta taɓe baki kafun ta saki hannun Mariya ta fada dakin Umma.
" Bai kamata ace kin zo nan kin zauna kin barshi rike da É—anki ba ya kamata kisan darajar É—a kuka yake yi fa amma kin zo nan kin zauna ai ko mai yayi miki shi Huzaif din bai kamata ki haÉ—a hukucin da zakiyi masa har da É—an naki ba domin shi bai san komai ba bai ma san abin da kuke yi ba don haka ki je ki anso shi don ya É“ata masa jiki sosai".
Tana gama fadin haka ta juya ta shigewarta dakin Umma zuciyarta na kara tausayawa yanayin da Hafsat take ciki gabadaya ta sauya kamar ba ita ba Mikewa tayi tana faman tankaÉ—i kamar wacce ta kwana ta wuni bata sakawa cikinta komai ba a hankali take tafiya har ta isa soron yanayin da ta ga Huzaif din a ciki sai da zuciyarta ta harba da sauri ta isa gareshi ta anshe shi tana wurga masa wani kallo kafun ta juya ta koma cikin gida ranta ba dadi gabadaya.
Umma ce ta dube su su duka kafun ta dubi ledar da Baseera ta ajje gefe guda.
 "Wannan kuma na meye...ba ma wannan ba ina kuka tsaya tun dazu ku da kuka ce mani ba daÉ—ewa za kuyi ba".
Ta karashe tana duban Mariya da ta koma gefe ta takure kamar wacce bata da lafiya.
 "Wallahi abin da muka je ansowa ne muka samu ba a karasa ba".
Baseera ta fadi tana zaro Iv din tana mikawa Umma ansa tayi tana dubawa kafun ta dubi Baseera.
 "Amma fa sunyi kyau sosai".
Murmushi Baseera tayi kafun ta dubi Mariya wacce itama izuwa lokacin ta dago kai.
"AMAREN BANA".
Baseera ta fadi cikin zolaya hararar ta Mariya tayi kafun ta dubi Umma.
"Ya kamata Umma ki yiwa Mariya magana gabadaya taki sakin jikinta shi kansa Dr. sai da ya tambaye ni ko akwai abin da ke damunta ne nace masa a,a gaskiya yanayin da take nunawa kamar akwai abin dake damunta".
Numfashi Umma ta ajje kafun ta dubi Baseera.
 "Ni ban san ta ina zan fara miki ba nima yanayin da Mariya take nunawa ya fara isa ta wani in ya ga haka sai ya dauka kamar auren dole za ayi mata..."
Bata karasa maganar ba wayar Baseera ta dau kara da sauri ta zarota daga jaka ganin sunan Mami ya sanyata saurin mikewa.
 "Umma bari na tafi kin ga har Mami ta kira ni nasan tana can tana jira na itama daÉ—ewar da mukayi yayi yawa".
Tana fadin haka ta dauki jakarta da ledar IV dinta ta fice bayan ta yiwa Umma Sallama Mariya ta mike jiki a sanyaye tayi mata rakiya....
   *Kamala Minna*💞💞💞😘😘
Post a Comment (0)