UKU-BALA'I 70

UKU BALA'I
           NA
       KAMALA MINNA.

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
​​WÉ› ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucÉ‘tÉ›, MѳtiѵɑtÉ› ɑɳɗ ɛɳtɛʀtÉ‘iɳ ѳuÊ€ ʀɛɑɗɛʀร​.
  BABI NA SABA'IN
Runtse idanunta take yi zuciyarta na zafi ji take yi kamar ta haÉ—iyi zuciyarta ta mutu don bakin ciki kukan da take yi tana samun sauki a yanzu ya zama wahala a gareta HAWAYEN ZUCIYA da take jin zubar su suma tana samun sauki kadan suma sun dai na zuba idanuwanta gabadayan sun kekeshe ba alamun za su zubda hawaye zafin zuciya ne da na ruhi kawai take jin su kamar a wuta aka jefa ta.
Dago kanta tayi ta dubi jikinta wani kunci ne ya sake mamaye zuciyarta in ta tuna yarda ta ga Mariya a wannan rana cikin yanayi na alfarma da shiga ta burgewa a matsayinta ta amaryar gobe har da ita amma ita ko wacce ta fi kowa rashin gata a duniyar nan sai ta fita jindadin irin wannan ranar wai ita ce yau kayan ma da zata saka ta fito a matsayinta na wacce za a daurawa aure amma sun gagareta kaicon wannan rana.
Sautin guÉ—ar da taji ta karaÉ—e gidan ne ta daki kunnuwanta ya sanyata sake runtse idanunta gami da toshe kunnuwanta ji sautin take kamar ana zirara mata ruwan dalma cikin kunnuwanta mikewa tayi kan kafafuwanta tana faman haÉ—e hanya fuskarta kadai zaka kalla ka gane kuncin da take ciki duban Huzaif tayi dake kwance a yan kwane kamar wanda ya fado daga sama ba uwa ba uba kau da kai tayi tana taka kafafuwanta tana kokarin fita a daidai lokacin Goggo Marka ta sanyo kanta cikin daki cikin yanayi na razana saura kadan su yi gware idanuwansu suka sarke da juna idanun Goggo Marka lokaci guda suka kawo hawaye da sauri ta kau da kai tana karasawa cikin dakin tayi zaman yan bori gami da dafe kanta wani irin kunci da takaici suke nukurkusar zuciyarta ga wani raÉ—aÉ—i da zafi da take jin ruhinta na yi mata kwanyarta take ji na ta faman ihu da hayaniyar abin da ya jefata cikin wannan halin bata taba zaton rayuwa zata juya mata haka ba bata taba zaton duniya zata yi mata gwatson mage ba sai yau.
Dago jajayen idanuwanta tayi ta sauke a fuskar Hafsat wani irin tausayinta take ji na kara narkar mata da zuciyarta tana kaico da wannan rayuwa da suke ciki wacce ita ce ta zamo sanadi garesu baki daya ita ce silar faruwar duk wani bala'i da masifa da suka tsinci kan su.
"Kiyi Hakuri Hafsat ki yafe mani NA YI NADAMA...".
Wani banzan kallo ta wurgama mata dama cike take da ita tun jiya da ake ta shagalin baki tana kallonta ta kwashi jiki ta shiga tana farin ciki ita kuma ta barta da kayan takaici makale cikin daki sai dai in mutuwa za tayi tayi kenan haka a shekaran jiya Huzaif ya zo suka kai ruwa rana akan bikin nan nasu akan haka yayi fushi uban komai bai bata ba kuma duk Goggo Marka ce sanadi dan kayan ma da ake yi cewa yayi ba zai yi ba ita kuma bata so ta hadashi da iyayensa saboda yanayin da suka nuna mata ba ta so ta nuna masu yanayin da suke ciki da É—ansu domin É—a da iyaye Allah ne kawai ya san tsakanin su tana tsoron su canza mata da ga kulawar da suke bata.
"Me zaki fada min Goggo ai kin rigaya kin gama cuta ta ba abin da zan ce da ke sai Allah yayi mani sakayya ba wanda ya jefani cikin bala'in rayuwa sai ke ba wanda ya zaɓa min wannan kazamar rayuwar sai ke bani ga karatu gani da dan shege ga shi mijin aure ma wulakantani yake yi tun kafin naje gidan sa wannan UKU BALA'In da mai yayi kama ni dai na san na gama ASARAR RAYUWA a filin duniyar nan".
Wani kuka ne ya kwace mata da sauri ta zame bayanta na kartar bango ta zube kan kafafuwanta wani kuka ne mai cin rai take yin sa amma idanuwanta kemadagas ba alamun hawaye runtse idanuwanta take yi tana buÉ—e su so take yi kawai ta buÉ—e su ta ganta a wata duniyar ba wannan ba...
Sallamar da ake kwaɗawa tsakar gidan ya sanya su duban junansu jin ana ambatar Hafsat da sauri ta fice ta leka ganin tsirarun mutane yan biki suna ta kai kawo sai wasu mata biyu da suke tsaye wanda kallo daya zaka yi musu ka gane cikakkun masu ji da kan sune gaɓadayan su sai wani yatsine fuska suke yi suna taunar cingam gaban Hafsat ne ya yanke ya fadi kafun ta juyo ta dubi Goggo da tayi fakare da idanu.
Da sauri ta fice daga cikin dakin gabanta na cigaba da buguwa ta isa garesu dubanta sukayi tun daga kasa har sama kafun su watsar dayan ta ja tsaki gami da tsartar da yawu hakan ya jawo hankalin yan bikin da suka fara taru har da na dakin Umma duk sun fito.
"Kece Hafsat?".
Babbar ciki ta tambayeta tana nunata da hannun hagu daga kai Hafsat tayi gabanta na kara tsinkewa ganin irin kallo da suke watsa mata a sa'ilin da ta tabbatar musu ita ce Hafsat din.
"Da farko dai ni sunana Assama'u yayar Huzaif wanda kike fata ya zama mijin ki ta ko wani irin hali sannan ina so in sanar sake cewa ki shirya zaman kunci da takaici a gidan sa sannan ki sani mu zuri'armu ba 'yar iska sannan babu wacce tayi yawon ta zubar har ta samu kyautar tukuicin É—an shege na gaba da fatiha wanda kika likawa kanina kika ce shine sanadin sa".
Gabadaya mutanan gidan idanuwansu yayo waje don wasun su da yawa ba su san abin da ke faruwa ba abin ka da mata nan aka fara kuskus ana duban Hafsat wacce ta gama sankarewa a tsaye gabadaya ta ji duniyar na juya mata kafafuwanta take ji suna lauye suna kokarin zubda ita kasa numfashi taja mai tafe da zafin zuciya duban su ta shiga yi daya bayan daya kallon da suke mata mai cike da tsana da kiyayya ya kara tsinka mata zuciya.
"Na san ba komai ba ne ya sanyaki makale masa har kika kunsa masa wannan sharrin saboda an ga gidan dala an ga gidan da jar miya ke kai kawo ba a saba lasa ba mai dattin hula ba ya kawo shine za a makalewa ɗan mutane to ki rubuta ki ajje bar ganin hajiya da Alhaji na goya miki baya to kisa ni ba da su za ki zauna ba da ɗan su za ki zauna har ɓarin jiki kike karen ki ya kamo zomo to wallahi zaki ya kawo miki wanda zai zaɓa miki UƘUBAR RAYUWA a gareki".
Dayar ta fadi tana watsowa mata ledar dake hannunta gabadaya kayan suka zube a jikinta daidai nan wasu hawaye na takaici suka surnano mata a saman kunci gabadaya ta kasa motsi jin komai take kamar a mafarki ba gaske ba dafa kafaÉ—ar ta taji anyi a hankali ta juyo Goggo Marka ce tsaye ita ma idanuwanta na zubda hawaye duban matan tayi cikin jin haushi kafun ta hadiye wani abu da ya tokare mata zuciya.
"Rashin arzukin har ya kai haka ai ba karya akayi ba shi Huzaif din ai ya san shi ya lalata mata rayuwa don haka ya kamata ku gyara kalamanku sannan ku sani ba a 'yar iska daya dole sai an samu dan iska...".
"Tsohuwar alagidigo tsohuwar banza gayyar kwadayayyu kisan dai ba yarda za ayi namiji ya tursasa mace akan wani ra'ayi ko dole sai ta aminta abu ke tabbata don haka karki sake karki sake dorawa Huzaif kalmar dan iska domin wannan karuwar 'yar taki ita ce silar komai".
Gabadaya gidan ya dau salallami Umma dake tsaye bakin kofa idanuwanta sun kawo hawaye da sauri ta iso garesu ta shiga ba su hakuri da su tafi amma ina kamar kara ingiza su ake yi nan suƙa shiga hayaniya suna tsinewa Hafsat da Goggo Marka a cikin wannan yanayin Abulle tayi sallama ta shigo hankalinta yayi matuka wajan tashi ganin abin da ke faruwa da sauri ta isa ga Goggo Marka dake ta faman rusar kuka kamar ranta zai fi janye ta tayi ta kai ta daki kafun ta fito idanuwanta itama sun kaɗa sun yi jajir ta dubi Hafsat ta watsar domin kuncin da take ji a ranta akan Hafsat ji take yi kamar ta hauta da bugu domin komai ya faru duk ita ta jawo musu.
Rigima ce ta balle sosai gidan biki ya hautsi ne sai da akayi da gaske bayan Umma ta kira Abban su Mariya ganin abin ya ki ci yaki cinyewa sannan komai ya lafa yan uwan su Huzaif suka fice Hafsat ta koma daki cike da takaicin wannan rayuwa da ta faÉ—a nan gidan biki lamari ya sauya nan da nan batun Hafsat ya zagaye ba abin da ake tattaunarwa akai sai maganar cikin shege da tayi Abulle ganin abin ya girmama kasa zama tayi ba tare da kowa ya sani ba ta fice daga cikin gidan cike da É—acin rai.
****
Sosai wajan ya tsaru tun da ga Get din in ka kalla zaka gane ba karamin waje bane aka kama domin shagalin bikin kamu na yau da za ayi tsaruwar ciki kuwa ba a magana ko ta ina haske kwayaye ne ke walwali kamar a kasar turai ga wani daddaɗar kamshi mai sanyaya zuciya kawai ke tashi ga wani CoolMusic dake ta faman tashi yana kara jefa al'ummar dake wajan kara faɗawa kogin nishadi sosai wajan ya ƙawatu da kayan alatu na more rayuwa ga wasu lafiyayyun kujeru za gaye da wani hadadden Table mai shimfiɗe da wani kayataccen yadi mai kalar Pink sai a tsakiyarsa an ajje wata fulawa mai kyalli da daukar idanu.
A daidai lokacin da jama'a suka gama hallara ana jiran amare su ido Mc sai faman zubda zance take yi da yake mace ce KHADEEJA S MUHAMMAD yarda ka kusan taci bakin aku kawai nishaɗantar da mutane take yi ana ta dariya a wannan lokacin aka fara sanar da cewa amare sun iso a hankali Mc ta sanya Dj ya canza kiɗa wani lafiyayya sauti ya shiga tashi ga duka na faman ratsa jikin yan biki nan suka shiga gyaɗa kai suna rausayawa hankalin su gabadaya ya koma kan kofar Hall din wani turirin kamshi ya shiga fesowa kawayen amarya guda biyu daga gaba suƙa shigo hannayensu dauke da kaskon turaren wuta suka shiga zagaye wajan da shi kafun cikin sakanni AMAREN BANA Mariya da Baseera suka sanyo kai cikin Hall din da yake hada bikin akayi waje daya.
Sanye suke cikin wani tsarren material Mariya ta saka Yellow colour ita kuma Baseera ta saka Light-Blue fuskokin su kawai zaka kalla ka gane suna cikin farin ciki da nishaÉ—i ratsantsiyar kwalliyar da akayi musu ta kara bayyanar da kyan su.
Nan da nan waje ya hargitse shewa kawai ake yi sauti na cigaba da tashi a cikin wannam yanayi har suka iso mazaunin su suka zauna sannan Mc ta bada umarni a tsayar da kiÉ—a nan ta shiga jawabin da abin da ya tara su a wajan kafun ta nemi daya daga cikin yan biki ta zo ta buÉ—e taro da Addu'a Anty Yusra ce ta fito yayar Baseera tayi addu'o'i na neman yin taro lafiya a tashi lafiya sannan ta goÉ—ewa duÆ™ wanda ya samu damar zuwa wannan bikin daga nan kuma lamari ya sauya a ka shiga biki gadan-gadan
Malam Sanah S Matazu aka gayyata ta gwangwaje amare da wa'azi da duk wasu karin haske na zaman gidan miji da nuna masu hanyoyin na salo salo na kula da miji da yi masa biyayya sannan da hakuri da juriya da boye sirrin miji sannan da girmama iyayen miji da yan uwansa da duk wani majibancin sa wa'azi sosai tayi musu mai ratsa zuciya da jiki tsayi lokacin mai nisa kafun daga bisa lamari ya sauya sosai da sosai kamu ya ƙawatu sai son barka nan ka shiga ciye ciye da shaye shaye kafun wani lokaci kuma komai ya zama daidai misalin karfe shida da rabi a ka tashi na yamma domin mazajen sun ce ba su yarda su kai dare a wajan ba ita kanta Mariya bata so yin taron ba bayar da za tayi ne Baseera son bidi'a gareta sannan ta samu goyan bayan su Dr.Karami.
Haka ko waccen su ta koma gida a gajiya Mariya gabadaya ta gama yin la'asar musamman in ta tuna gobe kamar yanzu ta jima da zama matar wani abin sosai take jin sa wani iri banbarakwai a cikin wannan daren sai da Umma ta kara kwantar mata da hankali sannan ta kara nuna mata darajar aure da martabobinsa ga 'ya mace sanna ta tunatar da ita fa'idar hakuri da juriya a gidan aure da duk wasu tsarurruka da yakamata ta bi domin dacewa da gidan aurenta sosai ta tsoratar da ita akan raina miji da dangin sa sosai ta nuna mata illar kin biyayya ga miji da duk wasu abubuwa da za su bata mata gidan aure ta.
GyaÉ—a kai kawai Mariya take yi tana jin yarda zuciyarta ke kara tsinkewa da lamarin a wannan daren barci sai dai barawo ne ya yi yawon gaba da ita...
*Kamala Minna*😘😘😘😘
Post a Comment (0)