UKU-BALA'I 71

UKU BALA'I
   NA.
    KAMALA MINNA.

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
​​WÉ› ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucÉ‘tÉ›, MѳtiѵɑtÉ› ɑɳɗ ɛɳtɛʀtÉ‘iɳ ѳuÊ€ ʀɛɑɗɛʀร​.
  BABI NA SABA'IN DA DAYA.
Zazzaɓi ne mai zafi rufe ta, bata tare da kowa ya sanin ba, sai karkarwa take yi numfashinta na kai wa da kamo wa, sautin haduwar hakoranta sai bada sauti yake yi gabadaya ta jigata, cikin wani irin yanayin tun a daren jiya. sosai take jin jikinta ba dadi, sosai take jin kamar akwai abin da ke shirin faruwa da ita, motsin da taji na shigowa ne ya sanyata kara kankame jikinta, zama taji anyi kusa da ita gami da yaye bargon da ta lulluba dashi, kara runtse idanuwanta tayi.
"Mariya".
Taji sautin muryar Umma ta sauka a saitin kunnuwanta, numfashi taja kafun ta buÉ—e idanuwan nata a hankali, ta sauke su a saitin Umma.
 "Me ke damun ki haka Mariya, sosai naji zazzaÉ“i a jikinki, me yasa haka mai yasa kike son cutar da kan ki ne, bayan kuma kin san wannan abin ba abin cutar bane gareki, mu ma iyayenki mun sani ba za mu so abin da zai cutar dake a duniyar nan ba".
Ta karashe cikin sanyin muryar tana riko kafadunta, ta tayar da ita zaune, tana dubanta.
"Ban son haka Mariya, ya kamata ki ajje komai na fargaba da ke a zuciyarki duk wani bahagon zance da zaki ji zuciyarki da kwanyarki na kawo miki ki ajje su gefe, shaiÉ—an ne kawai ke miki kuwwa yaka so ya bata miki lamarin ki na alheri, ki kokarta ki mike lokaci tafiya yake yi nan da wasu awanni MATAR WANI zaki zama, karkashin wani zaki koma komai naki zai koma garesa, rayuwar taki ma kacokan zata bar hannunmu, mu iyayenki zata koma karkashin sa. kin ga kuwa bai kamata ki saka wa zuciyarki wata damuwa ba zama ne muke fatan har gaban abada ayi shi, zama ne mai daraja da martaba da kuma hanyar tsira gareki da mu kanmu iyayenki, Mariya ina horar dake ki rike darajarki da ta mijinki ki anshe shi a matsayin miji na tabbara Hisham ba zai taba cutar dake ba, duk da dai ansan DAN ADAM ajizi ne amma bana SHAKKA akan sa, ke ma na san ba za a taba samun matsala ta fannin ki ba".
 Hayaniyar da ta kaure ne a tsakar gidan ya sanya Umma saurin mikewa ta fice, yan biki ne suka cika tsakar gidan, ga wasu tika-tikan tukwane da aka daura an banka masu wuta ko wani bangare ka duba na cikin gidan, zaka gane eh biki ne na musamman za ayi sa na masu rangwamin rufin asiri.
 Haka abubuwa su kai ta tafiya, har misalin sha biyu da rabi, da yake daurin auren karfe daya ne nan da nan maza masu zuwa daurin aure suka fara shiri, amarya kuwa na can kudundune acikin daki, gabanta sai dukan uku-uku yake yi.
Zaune take tana faman rarraba idanu tana duban jikinta yarda ya canza lokaci guda yayi haske gami da laushi, ga wani kamshi da yake ta fesowa daga jikin nata lokaci-lokaci take dago hannayenta tana kallo zane suke da lafiyayyan lalle baki da ja hakan ya kara ƙawata hannun nata sosai da sosai...
 Wayar Umma ce ta dau kara, da sauri ta dube gefenta in da take ajje, sunan da ta gani a jikin wayar ne ya tsinkar mata da gaba, runtse idanu tayi zuciyarta na mikata wani mataki mai girman gaske tana jin yarda zuciyarta ke kara buÉ—ewa da wani al'amari mai girma a gareta, sosai take jin wani shauÆ™i da begen Dr.Karami na kara bula mata jikinta ta ko ina, burinta da fatan ta za su cika muraÉ—in zuciyarta yau zai kasance tabbatacce.
A hankali ta kai hannunta ta dauki wayar gami da kaiwa kunnanta bayan ta latsa madannin ansa kira.
Wani numfashi mai sauti ta ji ya ajje, kafun ya saki wani murmushi da taji shi har kunnuwanta runtse idanu tayi, tana buÉ—e su sosai.
"Me yasa haka Mariya. kin san dai a irin wadannan lokutan sosai nake bukatar ki kusa dani ko na ji muryarki, amma tun jiya nake kiran wayar nan kin ki dagawa kin san kuwa yarda nake ji a raina, kin san kuwa irin damuwar da na shiga jiya zuwa wannan lokaci, ji nake yi kamar bani ba, zuciyata nake ji kamar ba ta kirjina kwata-kwata...".
  Da sauri ta zare wayar daga kunnuwanta tana duban fuskar wayar, don tabbatar da wanda take waya dashi. jin abin take yi kamar a mafarki, gani take yi kamar ba Dr.Karamin da ta sani ba, sautin kalaman take ji suna ansawa a cikin kunnuwanta da zuciyarta suna haifar mata da kasala.
"kice wani abu mana Mariya Please, kin ganni nan yanzu haka na kasa shiryawa saboda rashin jin ki ko barci banyi ba jiya, sosai nake ji a jikina kamar akwai abin dake faruwa dake".
Numfashi ta ja lokacin da ta mai da wayar kunnuwanta, tana jin yarda yake furucin nasa mai kokarin rikita mata lissafi, muryar take ji kamar batasa ba, muryar take ji ta sauya mata...
 "Please ki ce wani abu da zai karamin karfin guiwa mana, na kasa shiryawa, kin ga Dr.Aqeel har ya gama shiryawa tun dazu yake kirana a waya, suna hanya amma ni nakasa aikata komai Mariya sosai nake jin wani iri a jikina, sosai nake jin kamar akwai abin da zai faru..."
Runtse idanu tayi gabanta yayi wani irin dokawa, mikewa tayi kan kafafuwanta kafunta ja numfashi mai tsayi.
"Nima haka nake ji a jikina, ban san dalili ba".
Ta fadi da wata irin murya mai taushi, wacce bata san tana da irinta ba.
 "Yaa Rabbi!!".
Ya furta da sauti, kafun ya saki muryarsa sosai.
"Dafatan dai ba wani abu bane yake damun ki ba, Mariya Please fada min abin da ke damun ki...ko da yake bari na zo yanzu kin ji...".
  "A,a ba sai kazo ba, ba komai Allah..".
Ina! tun kafin ta ida zancenta har ya kashe wayar, sosai taji jikinta yayi sanyi komawa tayi ta zauna ragwaf! tana mai da numfashi bata san abin da ke damunta ba, gabadaya take jin wani iri a jikinta, kamar bata da lafiya.
 Sallamar da akayi ne ya katse mata hanzari, wasu mataye guda biyu suka shigo fuskarsu kunshe da murmushi suka isa gareta kallo daya tayi musu ta gane su waye, itama murmushin yaÆ™e tayi musu kafun ta hadiye abin da take ji ya tsaya mata a makoshi.
 "Ya kamata ki tashi ki yi wanka fa, lokaci tafiya yake yi kin ga har su Baffa sun wuce wajan daurin auren".
 Wani irin bugu taji gabanta yayi runtse idanu tayi, kafun ta buÉ—e su a saitin su, tana duban su daya bayan daya, wannan rana sosai take jin ta tana haifar mata da wani yanayi a zuciyarta, da ma jiki baki daya. komai take jin yana sauya mata komai na duniyar take ji yana canzawa.
"Yaa Mariya..Yaa Mariya".
Mu'azzam ne ya shigo da gudu har yana kokarin faduwa, Mariya ta kai hannu ta riko shi tana dubansa.
 "Kizo wai inji...".
Da sauri ta rufe masa baki, tana ajje numfashi. a zuciyarta ta shiga mamaki da tu'ajibi akan zuwan Dr.Karami, don ta tabbata shi ne ba wani ba. tana mamakin sa cikin yan kwanakinnan musamman irin kulawa da yake bata, numfashi ta ja kafun ta dubi su Asiya da suka zuba mata idanu, kau da kai tayi yarda zata fita ne take tunani ta tabbata ba za a bar ta ba, amma zuciyarta sai tunzurata take yi akan ta fita taje domin kuwa ita akaran kanta tana son ganin sa.
Mikewa tayi ta ja hannu Mu'azzam sukayi tsakar gida, su dai su Asiya ba su ce mata komai ba, sai bin ta suke da kallo, ba su gano abin dake faruwa ba.
  A hankali suka karasa tsakiyar tsakar gidan hankalin yan biki duk yana wajan aikin da suke, kara sauko da gyalen jikinta tayi, ya rufe mata fuska sosai, sai da ta tabbatar ba Umma a wajan da sauri ta fada soro sannan suka tsaya ta dubi Mu'azzam.
 "Dr.Karami ne?".
GyaÉ—a kai yayi. Batare da ta sake cewa dashi komai ba, suka nufi waje can ta hango shi jikin motarsa, jikinsa sanye da riga da wando kananu wani haske taga ya kara yi mata gami da kwarjini kau da kan ta tayi, zuciyarta na mikata matakin son Dr.karami da take jin yana kara narkar da zuciyarta.
 Sam bai lura da su ba sai da ya dago kansa daga wayar da ake ta faman kiransa ya kasa dagawa, da sauri ya shiga takowa garesu ji yake yi kamar fizgarsa ake yi idanuwansa gabadaya suna kan Mariya ya kasa dauke su, har ya iso inda take tsaye bai sani ba numfashi ya ja lokacin da yaji wani kamshi mai ratsa zuciya na dukan hancin sa, idanu sosai ya zuba mata kafun ya shafi fuskarsa.
 "Me ke faruwa ne?".
"Ba komai".
Ta bashi ansa a daidai lokacin wayarsa ta sake daukar burari da sauri suka dubeta su duka, sunan kawunsa ya gani da sauri ya daga, ba tare da yace komai ba na yan sakanni ya numfasa.
 "Ga ni nan zuwa Kawu, ina kan hanya yanzu haka kayi hakuri".
Ya fadi yana sauke wayar, idanu ta kura masa kafun ta ce.
 "Sai da nace karka zo, don Allah ka tafi na san suna can suna jiranka".
Tana gama fadin haka ta juya cikin gida da sauri, tana jin yana kiranta amma ko ta kan sa ba ta bi ba, saboda yanayin da take jin dukan zuciyarta.
*****
Misalin karfe daya da mintina ashirin aka shaida daurin auren DR.HISHAM MUKHTAR KARAMI da MARIYA BELLO GWADA sannan na DR.AQEEL MUNKA'IL da BASEERA HARUNA SA'AD daga karshe aka daura na HAFSAT DANLITI da HUZAIF ABDURRAZAQ sosai babbar masallacin juma'an garin Gwada ya cika, sai kace ranar idi gabadaya ma garin in ka shiga zaka gane ana gagarumin biki, Angwaye biyu bakin su a buÉ—e cike da farin ciki da muraÉ—an jindadi, haka yan uwa da abokanan arzuki, sai dai Ango daya in ka kalle shi kamar bakin kumurci haka ya koma, domin ana gama daurin auren ya bar wajan zuciyarsa yake ji tana zafi da raÉ—aÉ—i bai so zuwa ba kawai don ba yarda ya iya ne huzaif wannan ranar ta kasance masa ta bakin cikida takaici a filin duniyarsa, bai taba zaton abin zai tabbata ba sai yau, sosai yayi kudiri a zuciyarsa sai ya baiwa Hafsat mamaki sai ta gwammace zaman gidan yari da gidansa, sai ya gana mata azabar da sai tafi kaunar mutuwar da ita.
  Misalin karfe biyar na yamma aka shirya hadaddiyar Dinner a Hdyro hotel dake cikin Birnin Minna, sosai liyafan ta hadu waje ya cika makil amare da angwaye sun sha kyau na musamman kowa ka gani fuskarsa kunshe da farin ciki da jin dadi.
 Misalin karfe tara aka tashi ko wacce amarya da ta wagarta suka nufi gidan su, zuwa lokacin Mariya ta gama sadakarwar komai ya tabbata, ta zama matar Dr.karami sosai take jin zuciyarta na buÉ—ewa tana kara haifar mata da son sa, komai take ji nata na duniya ta mika masa.
  Lokaci lokaci take dauke hawayen da suke kwaranyo mata musamman in ta tuna rayuwarta a can baya, yarda ta kasance wai yau ita ce a wannan mataki ikon Allah kenan.
 Ko da suka koma gida nasiha sosai akayi musu mai ratsa jiki da zuciyar duk wani wanda yake zaune a wajan, Mariya kuka take yi mara sauti tana jin yarda a yau za ta rabu da Ummanta, zata rabu da Abban ta da Mu'azzam din ta, lokaci guda ta tuna lokacin da Dr.Karami yake cewa da ita anya zata iya rabu da Mu'azzam yarda take nuna masa so da kulawa?.
  Tabbas yau ga ranar ta zo ranar da zata koma wani gida na daban, gidan da Umma tayi mata fatan zama na har abada.
  A banagaren Hafsat kuwa rigima ce ta kaure sosai domin suna zuwa gidan amarya suka tadda su Assama'u sun kasa sun tsare tun daga lokacin da Hafsat ta sako kafar cikin gidan bayan an gama artabu wajan daukota don sai da akayi dak'yar sannan aka aiko da mota daya abin ya kara tayar mata da hankali ganin irin luntsuma luntsumar motocin da aka zo daukar Mariya da su sun yi jejir gwano a kofar gida hakan ya kara tabbatar mata da cewa Huzaif da gaske bai kaunarta.
  Numfashi ta ja wasu hawaye su zubo mata a kunci zuciyarta take ji tana sanar da ita irin kalubalan da zata fuskatan tun a yanzu a daren farkonta an fara yi mata rashin mutunci da wulakanta wanda suka kawo ta ina ga kuma an barta ita kadai ta san Huzaif da su Assama'u romanta ne kawai kila ba za su sha ba...
 *Kamala Minna*💞💞😘😘😘
Post a Comment (0)