WAƘAR MOTA

WAK'AR MOTA
1. So samu kome zan yi,
farko ILAHU na furta.
2. duk mai hakan ba shakka,
aikinsa zai inganta.
3. Alk'alami na fek'e,
yau zan yi wak'en mota.
4. kar dai kuce min don me?
ku dai kawai ku biyo ta.
5. amfanukan zan zano,
nan ban barin hatsarin ta.
6. mota da dad'in harka,
sai dai akwai ILLAR ta.
7. nau'i da nau'i tabbas,
kala kala jinsinta.
8. akwai ta d'aukar kaya,
har ta haya da akwai ta.
9. akwai ta 'yan K'WALISA,
biyo cikin shi'iri ta.
10. akwai ta yak'i ba wai,
KACA KACA tayunta.
11. tayu hudu take dassu,
in ba guda k'i shigarta.
12. sannan da GAS ko FETUR,
mota ake tashinta.
13. yin tafiyar kwanukka,
cikin yini ta yi ta.
14. motar shiga da mazaunai,
kushin kushin a cikinta.
15. akwai GILAS ya ka re-
iska da dad'i mota.
16. motar wata hada A/C,
amfanuwar na cikinta.
17. Abdulhamid Malumma,
wak'ar ga ni na rubuta.
08037868097
Post a Comment (0)