YAƊUWAR BIDI'A YANA KASHE SUNNAH

YADUWAR BIDI'A YANA KASHE SUNNAH

الإمام الشاطبي رحمه الله تعالى:
Yana cewa;-
"Babu wata Bidi'a da za'a qirkiro face sanadiyyarta an kashe wata Sunnar Manzon Allah ﷺ saboda yakin da wannan Bidi'ar take da Sunnar Manzon Allah ﷺ".

*Kashedin da Magabata akan bidi'a ya ishi mai hakali ya nisanci bidi'a dan raya sunnar Manzon Allah ﷺ*.

*1-اﺑﻦ ﻋﺒﺎﺱ ﺭﺿﻲ اﻟﻠﻪ ﻋﻨﻬﻤﺎ*
Yana cewa;-
*"Babu wata shekara da zata zowa mutane,face sun kirkiro wata bidi'a kuma sun kashe wata Sunnah sanadiyyar kirkiro wannan bidi'ar,har sai an wayi gari sun sun raya bidi'a suna kashe sunnah"*.

*2-Awani bangaran yana cewa*
"Babu wani mutum da zai kirkiro wata Bidi'a face ya bar aiki da wata sunnah wadda tafi alkhairi akan wannan bidi'a da ya kirkiro".

*3-ﻟﻘﻤﺎﻥ ﻋﻦ ﺃﺑﻲ ﺇﺩﺭﻳﺲ اﻟﺨﻮﻻﻧﻲ*
Ya kasance yana cewa:
"Babu wata al'umma da zata kirkiro wata bidi'a aciki addininta, face wannan bidi'ar ta dauke masu wata Sunnah ta Manzon Allah ﷺ".

*4-ﺣﺴﺎﻥ ﺑﻦ ﻋﻄﻴﺔ*
Yana cewa;-
*"Babu wasu mutane da zasu kirkiro wata bidi'a acikin addininsu,face Allah ya cire masu wata Sunnah kwatankwacinta sannan wannan Sunnar bazata dawo garesu ba har zuwa Ranar alqiyama"*.
@الاعتصام ج1ص33-34
 عبدالرحمن الربعي دارالحديث بالحسينية ١٤٣٩/٢/١٥.

*Rayuwa mai dadi da kwanciyar hankali yana ga wanda yake koyi da Manzon Allah ﷺ a dukkan rayuwar,babu mai rayuwa acikin kunci kamar mai aiki da bidi'a domin dukkan bidi'a batane*.

Allah ya shiryemu baki daya.
Post a Comment (0)