KAN MAI UWA DA WABI


KAN MAI UWA DA WABI


Bismillahir Rahmanir Raheem.

Assalamu Alaikum Warahmatullah wabarakatuhu.

Yaku ƴan uwana ina yi mana Barka Da Warhaka. Sannan ina mai neman afuwar duk wanda wannan muƙala tawa zata ɓatawa rai, domin yau kam in shaa Allaah babu sauran ɗaga ƙafa. Haka kuma zan so kuyi min aikin gafara idan kuka ji na saki layi a wasu wuraren, kamawa tayi ne shi yasa. Sannan kowa ya sani, babu batun nuna ɓangaranci yau, Gaskiyar abin da na fahimta zan faɗa ba tare da ɗagawa wani ko wata ƙafa ba, ko da kuwa ni ne da kaina.
 Allaah Ya azurta mu da Kyayyawar fahimta Aameen.

Wato wata Matsala wacce na lura da cewa ana yawan magana a kanta, kuma har wa yau babu wani ci gaba da zan iya cewa an samu akai. Wannan dalili yasa na yanke Shawarar yin bayani akanta tare da kawo mafita a Ƙarshe in shaa Allaah.

Matsalar ita ce,; da zaka tara Mata tun daga ɗaya har zuwa ɗari zaka samu kusan kowacce daga cikin su tana zargin maza da cewa sun faye kallon mata da yawa, matan nan kuwa ko da na aure ne, ko da zawarawa ne, ko da ƴan mata ne, ko da ƙwwilaye ne, ko da Berori ne kuma ko da Tsoffi ne.
A ɓangaren maza kuma, da zaka tara su suma tun daga ɗaya har zuwa ɗari (ciki har dani) mafi yawancin su suna yiwa matan irin kallon da ya wuce na Shari'a, da zarar kayi magana sai su ce ai laifin matan ne saboda irin shigar da suke yi.

A taƙaice dai kowane ɓangare yana zargin ɗan uwansa. Wannan dalili yasa na yanke Shawarar fitowa domin inyi fiɗar bayanai dangane da matsalar da kuma hanyar da nake ganin za'a bi domin a magance wannan matsala.

Da Farko dai zan fara da iyaye na mata. Mata halittu ne masu wuyar Sha'ani, ana son su amma suna da wuyar mu'amala a mafi yawancin Lokaci, sai dai ba duka aka taru aka zama ɗaya ba. Amma fa, mata sun san cewa Allaah da Manzon Sa Sun yi hani da shigar da bata dace ba yayin fita daga gida a wurare da dama a cikin alƙur'ani da Sunnah, sai dai Kaico! Yawancin iyayen mu mata basa amfani da duk nasihohin da ake musu. Ga ka ɗan daga cikin halayen wasu Iyeye mata dangane da wannan matsala.

*. Wata tana shigar da bata dace bane saboda neman Samari kai tsaye, domin wata gani take yi in ba haka tayi ba bata da hanyar jawo hankalin wani da har zai zo ya neme ta.

*. Wata tana shigar da bata dace bane saboda ta jahilci girman laifin aikata hakan a musulunce.

*. Wata tana aikata hakan ne saboda yahudanci ya riga ya ratsa ta.

*. Wata tana yin Hakane saboda ita tafi ƙarfin kowa, ƴar bariki ce ba mai tsayawa ma yayi mata Nasiha tunda ba ɗauka zata yi ba.

*. Wata dama da gangan take yi don a kalle ta a san cewa ta tara abubuwa saboda wasu DALILAI nata na musamman.

Kaɗan kenan, wasu matan fa kuyi min aikin gafara suna fitowa yawo ba tare da ko ɗan Kamfai ba a jikin su, face doguwar riga kawai ko Hijabi, wanda da zarar iska ta kaɗa, to komai kawai yana waje ne dama. Wani abin mamaki kuma shi ne, yawancin matan nan sukan yi irin shigar da su kansu sun san cewa tabbas in suka fita fa dole sai an kalle su, amma kuma ana kallon nasu sai su koma suna zage-zage da cewa maza karnuka ka ne, ko Mayu ne ko Muzurai ne. To ke kuma fa?

Wata ko Hijabi zata sa sai ta sa shi yadda zata ja hankalin mazaje kanta, kuma da zarar sun kalle ta tace wai Tsinannu ne sun faye shegen Kallo, to ke kuma fa?

Wata fa in tana tafiya har bouncing take yi tana kallon yadda jikinta yake kaɗawa tana alfahari da irin Surar da Allaah yayi mata, ita fa da kanta kenan, amma a haka sai kaji in an bita da kallo tana cewa shegu sun ga kaya, to ke kuma fa?

Maza na dawo kan mu, da yawan maza suna jawa sauran zagi duk kuwa da cewa mu ma ba a taru an zama ɗaya ba. Amma feesabilillah abinda wasu mazan suke yi ko kare bai yi sai dai bunsuru. Wasu mazan fa ko tsohuwa ce In suka bita da kallo sai taji kamar ta faɗi don kunya.

* Idan kuma ƙwaila ce sai kaji ana 'hmm wannan in ta girma za'a yi mace a wajennan.

* In kuma matar aure ce sai kaji ana cewa,' ho ɗan nema wance fa har yanzu da sauran ta. Ko wane fa yayi dace malam, har yanzu ana gurzawa.

* In kuwa ƴan mata ne, haba malam ana magana ma wannan. Sun manta da cewa Addini ya gargaɗesu da cewa su kame ganin su kuma su kasance masu kau da Kawunan su daga irin waɗannan mataye.

Kuma da zarar kai magana sai kaji ance 'ai laifin matan ne, wa yace suyi shigar da bata dace ba? To in sunyi, kai kuma wa yace ka biye musu?
Maza da yawa sun ɗauki Ɗabi'ar kallon matan mutane da ƴan mata kamar wata Sana'ar kirki, shi yasa unguwanni da yawa zaka ga ƴar ƙungiya an zauna kawai ana faman yi da mutane, kaɗan ne suke iya sauke haƙƙin zaman bakin titi.
Kenan idan muka lura da waɗannan bayanai, zamu iya fahimtar cewa kowane ɓangare suna da nasu irin matsalar. To mecece mafita?

Mafita anan ita ce kowa yaji tsoron Allaah Ya tsaya inda aka iyakance shi kada ya ƙetare iyaka. Ke a matsayin ki na mace Musulma wacce ta san mutuncin kanta kiyi iya ƙoƙarin ki wajen ganin kin rufe tsiraicin ki yayin fita, ba ki dinga fita kamar yadda aljifan baya suke fita ba.
Kai kuma a matsayin ka na namiji musulmi wanda ya san mutuncin kan sa, ka yi iya ƙoƙarin ka wajen kare ganin ka daga abin da bai kamata ba.

Sannan kuma dukkanmu mu yi wa junan mu adalci, tunda kowa yana da nashi laifin, me zai hana muyi ƙoƙarin gyara namu kura-kuran a maimakon ci wa juna zarafi da kuma aibata juna? Me zai hana mu dinga yiwa juna Addu'a tare da fatan shiriya a maimakon zagi da tonawa juna asiri?


Ina fatan Zamu ji kuma za mu gyara.
Allaah Ya Shirye mu baki ɗaya, ya Shiryi Zuri'armu. Ya gafarta mana laifukan mu kuma ya ɗora mu akan abinda yake shi ne dai-dai.

Subhanak Allahumma wabi hamdika ash hadu anla ila ha illah anta astagfiruka wa atubu ilaika. Assalamu Alaikum Warahmatullah wabarakatuhu.

<••••••••••••••••••••••••••••>
  ɧãımãŋ Kɧâŋ Řâééʂ <••••••••••••••••••••••••••••>
       08185819176
Twitter: @HaimanRaees
Instagram: Haimanraees
Infohaiman999@gmail.com
Post a Comment (0)