SARKIN SARAKAI BOOK 1 - 9

 SARKIN SARAKAI BOOK 1. 09
DUK DA kasancewarsa bakin fata saiyaga ya zamo farar fata kuma ya juye zuwa kyakkyawar budurwa hatta gashin kansa anmaidashi dogo.
kuma baki sidik mai kyalli kirjinsa ya cika fam irin na mata ita kanta rigar da aka sanya masa irinta sarakaice abar a tsaya a kalla haluf ya dubi kansa da kyau sai yace a ransa lallai ashe inda mace aka yoni da na kasance daya daga cikin kyawawan duniya koda kuwa an barni a matsayin bakar fata koda aka kammala sauyawa haluf kamanni daga da namiji izuwa ya mace sai jamhas ya tafi dashi izuwa keken dokin gimbiye shukura tunkafin su karasa gareta ta zubo musu idanu tana murmushi gami da yiwa haluf wani irin kallo mai cike da alamomin tambaya bisa dole ya tsargu cewa lallai wannan mace nada wata babbar manufa a kansa ba tare da ya bata lokaci ba gimbiya shukura ta umarci haluf daya shiga cikin keken dokinta haluf ya waiga gaba da baya yaga gaba daya jama ar ayarin shi suke kallo cikin tsananin mamaki kawai saiya shiga cikin keken dokin ya zauna a gefe daya suna fuskantar juna shida shukura koda isowarsu bakin kofa sai suka iske kofar a balle a kasa makera na ta aikin kokarin gyarata don mayar da ita inda take koda ganin haka sai gimbiya tabada umarnin a tsaya a gaban sarkin kofa A lokacin da sarkin kofa da wadansu sababbin abokan aikinsa suka risina ga gimbiya suna masu yi mata barka da zuwa gimbiya shukura ta dubi sarkin kofa tace menene kuma ya faru naga kofar birnin nan a balle shin giwace tayi mana wannan barnar? Sarkin kofa ya risina yace ranki ya dade ai wannan ba aikin giwa bane wani shahararren mayakine waishi sarki sahibul hairi yazo don ya rabamu da gatarin mu na sihiri yanzu haka ya zama gawa domin sarki ya jefashi cikin gidan masifa na karkashin kasa dake fada koda jin wannan batu sai hankalin bawa haluf ya tashi bai san sa adda gumi ya tsatstsafo masa ba nan da nan fuskarsa ta cika da alamomin tashin hankali yayinda gimbiya shukura ta dubi fuskar haluf ta lura da sabon yanayin daya shiga sai kawai tayi murmushi tayi umarnin aci gaba da tafiya nan take kuwa aka kara nausawa cikin birnin askandariyya lokacinda su gimbiya shukura suka iso fada sai suka iske an gama walimar da ake yi har sarki ya mike ya shiga gida jama a sun fara watsewa kowa na kama gabansa koda aka ga zuwan gimbiya sai aka rabe aka bata hanya kuma ana kwasar gaisuwa gaba daya dawakai suka iso wajen tsayuwarsu aka tsaida su sannan su gimbiya da bakuwarta suka fara gitowa daga cikin keken doki amma bakuwar tasha lullubi ba a iya gane ko wacece nan dai su gimbiya suka shige izuwa cikin gidan sarautar kuyanginta da barorinta na take mata baya su kuwa su jamhas sai suka watse koya ya tafi izuwa nasa gidan A ka ida duk sa adda gimbiya shukura tayi tafiya ta dawo saita aikawa da sarki cewar ta dawo yana jin haka zai tako da kafarsa yazo har turakarta su zauna ta bashi labarin abubuwan da suka faru yayin tafiyarta da dawowarta in banda irin wannan lokaci sarki barusa baya zuwa bangaren gimbiya shukura A wannan karon kuwa sai al amarin ya sauya domin tana shiga cikin turakarta bata zauna hutawa ba sai kawai ta tafi izuwa bangaren da kanta amma kafin ta tafi ta umarci kuyangi dasu yiwa bawa haluf wanka su cire masa tufafin da aka sa masa na mata a takaice dai adawo masa da siffarsa ta dai dai kamar yadda yake a matsayinsa na da namiji sarki barusa ya kishingide a cikin turakarsa cikin nishadi yana hutawa kawai sai yaga gimbiya shukura ta taho gareshi cikin tsananin mamaki ya mike tsaye ya tareta cikin tsananin farin ciki suna annashawa gaba dayansu A duniya babu abinda sarki barusa keso sama da gimbiya shukura don haka ko kadan baya son abinda zai bata mata rai komai kankantarsa sarki barusa ya dubi gimbiya shukura cikin murmushi yace yake abarkaunata yau kuma menene dalilinda ta hanaki turo a sanar dani dawowarki domin na taho turakarki mu zauna kamar yadda muka saba? Koda jin wannan tambaya saita maida masa martanin murmushin tace yakai rabin raina rabin jikina kayi sani cewa ba komai bane ya haddasa hakan ba face tsabar farin ciki domin wannan karon nazo ma ka da labari mai dadi ka sani cewa a wannan tafiya da nayi na ziyarci wani mashahurin boka wanda ya bani magani yace indai na sha wannan magani lallai zan samu ciki dakai na haihu a cikin shekara guda koda barusa yaji haka saiya cika da farin ciki ya sake kankame shukura a kirjinsa yana dariyar murna yau shekara goma sha biyar kenan da yin auran gmbiya shukura da sarki barusa amma basu taba samun haihuwa ba bayan shekara daya da yin auransu sukaga basu samu juna biyu ba sai hankalinsu ya dugunzuma suka bazama neman magani amma ba a dace ba saboda ganin yadda barusa ya damu matuka da neman haihuwa saita bashi shawarar ya sake yin wani auren ya gani domin babu mamaki matsalar daga gareta ne da farko da barusa yaki yarda da wannan shawara sbd sonda yake mata amma data matsa saiya amince saida sarki barusa ya auri mata goma sha daya lokaci guda amma da aka shekara yaga babu haihuwa duk ya koresu ya rungumi kaddara.......
TUN daga wannan rana shukura ta cigaba da yin tafiye tafiye izuwa kasa kasa da ziyarar manyan bokayen duniya akan neman masalaha ranar da taje wajen wani mashahurin boka waishi KUMATU saiya yi bincike ya gano cewa matsalar haihuwarna tare da sarki barusa har abada bazai taba haihuwa ba ita kuma gimbiya shukura bazaata taba samun juna biyu ba face ta kwanta da namiji saurayi wanda shekarunsa basu kai talatinba wanda bai taba tarawa da ya mace ba kuma doleneya kasance bakin fata lokacinda gimbiya shukura taji wannan batu saita kamu da tsananin bakin ciki ta fashe da kuka saida ta dade tana kuka sannan tayi shiru ta dago kai tana mai duban boka kumatu hawaye na zuba a idonta.yace yakai wannan boka ina sonka sanar dani yadda zan gane saurayi mai wadannan suffofi duk sa ar da na hadu dashi boka kumatu yace duk ranar da kika hadu da wannan saurayi kina yin arba dashi zakiji ya kwanta miki a rai ma ana nan take zakiji sonsa to lallai in kikaji haka sine kadai saurayinda zaki tara dashi ki samu haihuwa in kuwa ba hakaba harki mutu ba ke ba samun da gimbiya shukura bata da wani buri wanda yafi ta haifi danda zai gaji mijinta wato sarki barusa domin ta san cewa duk ranar da sarki barusa ya fadi ya mutu dolene ta bar gidan sarautar domin wanine daban daga cikin fadawansa zai karbi mulkin bayan gimbiya shukura da sarki barusa sun gama murnar wanann labari datazo dashi sai tayi masa sallama akan cewa zata tafi dakinta ta kwanta domin ta huta gajiyar tafiya ba tare da gardamar komaiba yayi mata izinin tafiya, lokacinda gimbiya shukura ta iso cikin falon turakarta ta iske bawa haluf a zaune an caba masa ado kyawunsa yakara baiyana kururu a baiyane saita kamu da matukar sha awarsa kai tsaye ta nufo inda yake da zuwa saita yunkura da nufin ta rungumeshi cikin tsananin tsoro ya zame jikinsa ya mike tsaye ya koma can gefe daya ya dubeta cikin biyayya yace haba ya shugabata shin kin mantane cewar ke matar sarki ce sokike a tsireni idan aka kamani da laifin yin wani abu dake? Sa adda taji wannan batu saita kyalkyale da dariya sannan tace yakai wannan ma abocin kyau da kwarjini ka saki jikinka ka sani cewa duk abinda zamuyi a nan babu mai ganinmu yanzu dai kafin wani abu ya wakana a tsakaninmu ina son ka amsa min tambayoyin nan guda biyu da nayi maka tun farkon haduwarmu' kodajin haka sai haluf ya kirkiri karya ya shara mata yace ai shi bawane ya gudo daga hannun ubangidansa da ga can wata kasa da ake kira SHUBUR kuma ba komai bane ya sa ya gudo ba sai don tsananin aikin wahalar da ake sa shiyi kullum lokacinda ya gama wannan jawabi sai gimbiya shukura ta dubeshi ta kyallkyale da dariya tace haba dan samari ka dubeni da kyau kai kasan cewa ni ba yarinya bace karama kuma ina da kaifin tunani da lura ai fatar jikinta mutum ya duba ya san cewa a dduk inda kake baka shan waahala tun da dai ba zaka gaya min gaskiya ba ni yanzu zan sanar dakai ko kai waye . Yakai haluf ka sani cewa tundazu da muka dawo gida kafin naje ga mijina saida na shiga cikin wani daki na na sihiri inda nake tafiyar da harkokin sihirina yi bincikena na gano cewa kazo wannan birni namu ne tare da maigidanka sarki sahibul hairi na birnin misra domin ya rabamu da gatarinmu na sihiri sbd da wannan gatari ne kadai zai iya balle kofar gidan boka SHAMZUBUL AZWAS wanda ke can tsuburin tekun bahar zallus domin ya dauko karamar yarinya Alfila wadda ta kasance yace ga wani gagarumin sadauki waishi Awaisu yakai haluf kayi sani cewa nima na dade ina neman wannan yarinya alfila na rasa yadda zanyi na sameta saboda na kwashe sirrikan tsafin dake jikinta na dawo dasu jikina don cika burina na biyu a duniya burina na farko shine na haifi da wanda zai gaji sarautar birnin Askandariyya bincike ya nuna mini cewa kaine kadai namijin da zan kwanta dashi na samu haihuwa don haka ina bukatar hadin kanka ayanzu sa adda shukura tazo nan a zancenta saitaga hawaye na zuba a idanun bawa haluf al amarinda ya matukar bata mamaki kenan ta dubeshi tace kai kuwa menene dalilin zubarda wannan hawaye a idanunka? Haluf yace aini yanzu bani da sauran buri a duniya face mutuwa tunda babban masoyina mutumin da nafi shakuwa dashi fiye da kowa babu shi wato sahibul hairi naji dazu sarkin kofa yana bayanin cewa an jefa shi cikin dakin masifa na karkashin kasa ya hallaka bisa wannan dalili nake ganin cewa rayuwata bata da sauran amfani don haka kashe kaina zanyi koda gama fadin haka sai bawa haluf ya sa hannu cikin rigarsa ya dauko wata zuka ya daga sama da nufin ya caka a cikinsa aman sai gimbiya shukura tadubi hannunsa da kwayar idanta take wata irin iska mai karfi ta rike hannun haluf ya kasa cakawa kawai saiji yayi an fisge waukar daga hannunsa anyi jifa da ita can gefe cikin tsananin firgici da mamaki haluf ya zauna kasa dirshan yana mai kallon gimbiya shukura ita kuwa saitayi murmushi ta tako kafafunta tazo daf dashi ta tsugunna suka fuskanci juna tace........
Zan Cigaba Insha Allah
Post a Comment (0)