A MATSAYIN KI NA BUDURWA YA KAMATA KI SANI CEWA...

MATSAYINKI NA MACE BUDURWA
INDAI KINSAN KINA SOYAYYA KIKULA
DA WANNAN SAQO KI KARANTASHI.

Daga Sister KHADIJA

(1) ki tsayar da saurayi guda daya tak
na kirki bisa la akarai da ayyukan sa
da halayensa na zahiri.

(2) kitabbata kina sonsa sosai kuma
shima yana sonki sosai.

(3). Kada ki yarda kidade da saurayi,
ko kishaqu dashi ko ki nuna masa
tsananin so batare da iyayensa sun
gana da iyayenki ba. In yaqi turosu
kirabu dashi tunkafin yagama sace
zuciyarki.

(4). Kizama mebin shawarar iyayenki,
da neman shawararsu a harkar soyayya, kada kibi shawarar Qawaye ko saurayi kobin shawarar zuciyarki.

(4). Kada kiyarda a kawo miki gulmar
saurayinki ke kuma kidauka koki kama zargin sa. A’a sai kinyi bincike na adalci ko kingani da idonki.

(5). Kada ki kuskura kiyiwa saurayinki
qarya kizama me fada masa gaskiya ,da
yimasa bayanin komai iya saninki.

(6). Kizama me yawaita addu’ah da
bawa Allah zabi a dukkan lamarinki..

(7). kikiyaye zargi da binciken laifinsa
matuqar ya sanar dake komai bai 6oye miki gaskiya ba.

(9). kidauka dan adam tara yake bai
cika goma ba, kinga zai iya kuskure, dan haka sai kiyi masa afuwa.

(10). kizama me kare mutuncin kanki
,da kuma kulada matsayinki batare da girman kaiba ko jan aji ga masoyi…

JAN AJI A SOYAYYA YANA DAKYAU

idan saurayinki ya tsaneki ko yagudu
yabarki ko kin rasa wani abu da yake baki, kiyi haqury kada kijuya masa baya, kisa masa shakka a ransa yadinga tunanin anya kuwa kina son sa da gaske ???

KEDAI KAWAI KI KARE MUTUNCINKI
DA IYA TAKUNKI

(11). Kada kiyarda ki sakarwa saurayinki fuska yana shigo miki da kalmomin da basu daceba ko dabi’u. kamar yace zai samiki zobe, ko zaiga awar waronki ko zaisa miki jaka, ko zaiga fulawarki ,ko
zai auna kaurinki dadai sauransu.

SABODA HAKA KIZAMA ME BATA RAI
ADUK SADDA KIKAGA HAKA, KODA YATAFI KIRABU DASHI, DAMAN BA NAGARI BANE, SOYAKE YA BATAKI.
Wakilin shaytanne.

(11). Kizama me yiwa saurayinki Al-
qawarin nuna masa soyayya bayan aurenku, sannan dayi masa biyayya dai dai gwargwadon iyawarki.

KISANI DAYAWAN SAMARI AKWAI
MAKIRCI.

Wani yasan ba aure zaiyi ba amma
zaizo yabata miki lokaci. Wani soyake yakoyi zance sai kawai yazo wajenki yayi tayi miki qarya batare dakin fargaba
zai dasa miki ciwon so,

YA KORAR MIKI SAMARIN KI NAKIRKI.

Wani kuma kawai so yake yana zuwa
wajen fati dake. Saboda haka zaina saya miki kaya kala kala yana fira da ke zai fake da cewa SAI YAGAMA School
KO SAI BAYAN YAGAMA KARATU ZAI
TURO KUYI AURE.

Duk fati ko fikines zai daukeki kutafi.
Wani kuma soyake kawai yana taba
jikinki yaji dadi koda bai kwanta dakeba, saboda haka zaita binki sauda qafa yana
soyayya dake.

Wani kuma so yake ya bataki. Irin wadannan samarin sunfi kowanne
hatsari. Idan yaganki yana sonki yana fara
karantar halayenki 

IDAN YAGA KE USTAZIYACE TO ZAIYI
SHIGAR USTAZAI HARDA LITTAFIN SA A HANNU ,HAKA ZAITA KAFA MIKI TARKO HARSAI KIN FADA.

Idan yaga ‘yar BOKOCE zai fito miki a
dan boko. Idan yaga ke yar duniya ce toshima a hakan zai fita. Irin wadannan samarin har kayan mungani munaso suna kaiwa budurwa, har iyayensu suna turowa daga qarshe daya kwanta dake shikenan
yabiya buqatarsa, bazai bari kisami cikiba zaibaki qwaya da zarar yaga baki da ciki
yasan yayi free tunda yasami abinda yake nema, zai Qirqiri laifi yalaqa miki domin ku6ata a karbo kayan sa daga gidanku, koma yabar miki kayan…

Irinsu akwai makirci da nuna tsagoran
soyayya ga budurwa, domin sukanyi kukan hawaye a gaban budurwa duk da sunan so amma yawanci domin ya raunana zuciyar kine. Yakan maqale miki har unguwa yana rakaki koda yaushe.

YAR UWA IN SOYAYAYYA TAI GARDAMA WAYE YAFI SHAN WUYA DA TOZARTA ???

SHIN ANAIWA NAMIJI CIKIN SHEGENE
KO BUDURWA AKEWA ??? IDAN ABIN KUNYA YAFITO WAYE ZAI ZAUNA A GIDA KO MAQOTA BAI ZUWA DAN KUNYA NAMIJI KO MACE ???

MEYASA NAMIJI ZAI IYAYIWA YAN MATA BIYAR CIKI BATARE DA AURE BA AMMA
INYAZO NEMAN AURE SAI ABASHI ???

IDAN KUWA MACE TAYI CIKI SAU DAYA DA KYAR TAKE AURUWA KOMA SAI TABAR GARIN ???

MEYASA MACE INTAI CIKI AGIDAN SUMA TSANARTA AKEYI ,AMMA NAMIJI
DAYA KAWO RAGO DA KUDIN ICE SHIKE NAN ???

MATA NAWANE SABODA CIKIN SHEGE
SUKABAR GARINSU KO RAYUWARSU
TA GURBATA AMMA SHI NAMIJI
KAMARMA BAIYI KOMAI BA ???

KO KAMUWA KIKAI DA MUGUN CIWO
WAZAI KULA DAKE YABAKI KUDIN
MAGANI DUK WATA ???

KINTABA GANIN ANSA WUQA A WUYAN NAMIJI ANCE INBAKA FADI WACCE
KAYIWA CIKIBA SAINA YANKAKA ???
AMMA WA AKEWA HAKA ???

‘Yar uwa kada dadin soyayya, ko dan
kudin da saurayi zai baki kodan zai saki a
gaban mota ,kodan wasu yan riguna dazaina saya miki

HAKAN TASA KIBASHI DAMA HAR YASANKI

DON ALLAH KUYI SHARING, KOSAQON ZAI ISO SAURAN MATA


Post a Comment (0)