IDAN KWANAKIN KAFFARA SUKA FAƊO A RANAR IDI

IDON KWANAKIN KAFFARAR KISA SUKA RATSO A RANAR IDI, MENE NE HUKUNCI?


Tambaya:

Assalamu Alaikum. Allah ya karama rayuwa albarka. Malam don Allah a taimakamin da amsar tambayarnan.
Mutumin da yake azumin kaffarar mutuwa ya zaiyi da ranar sallah. Shin zai aje azumin na ranar ne koko zai wuce kawai da azumin shi. Allah ya bada ikon amsawa.

*Amsa:*

Wa alaikum assalam, Amin Allah ya amsa adduarka.
Malamai sun yi sabani game da azumin kaffara idan ya ratso ranar idi zuwa maganganu guda biyu :
1. Ba za'a tsaya ba saboda ranar idi za'a cigaba da azumin saboda aya ta (92) a suratun Nisa'i ta shardanta yin azumin kaffarar Kisa a jere, dakatawa saboda idi kuma zai Kore wannan sharadin, wannan ita ce maganar mafi yawan malamai.
2. Ya wajaba ya sha azumi a ranar idi, saboda yin AZUMI haramun ne a wannan ranar kamar yadda hadisin Umar dan khaddabi ya tabbatar, wannan yasa ba shi da laifi idan ya sha tun da Sharia ta yi masa izni.
Zance mafi inganci shi ne na Biyu, saboda idan hani da umarni suka ci karo da juna ana gabatar da hani, saboda haka mai kaffarar Kisa zai sha saboda Idi ko tafiya ko haila.Allah ne mafi sani.
Don neman Karin bayani duba: Al-Muntaka min Fataawa Alfauzaan 1/152


*Dr. Jamilu Zarewa*
31/08/2017.

Kukasance Damu a shafin mu na Facebook ta wannan link dake kasa👇🏿👇🏿👇🏿
http://www.facebook.com/Islamicsunnah . Ga masu Sha'awar shiga group din ISLAMIC SUNNAH a whatsapp saisu aiko da suna da state ta wannan number +2348060618481

Post a Comment (0)