HANYOYI GOMA DON FITA DAGA BALA'I DA ƘUNCIN RAYUWA


HANYOYI GOMA DON FITA DAGA BALA’I DA KUNCI
DA DAMUWA

_(Sheikh Muhammad Rabi’u Rijiyar Lemo)_

Babu ko shakka kowa a yau ya san al’ummar
musulmi a duniya suna cikin halin kunci da
damuwa,don haka wajibi ne malamai da daliban
ilimi su ci gaba da haskawa al’umma hanyoyin da
ya kamata su bi don samun mafita daga wannan
bala’i da musifa.
Ga wasu hanyoyi goma da zamu runguma da izinin
Allah,Allah zai yaye mana wadannan musifu:


1-Kyautata imani da Allah da nisantar abin da yake
tauye imani.
Allah ya yi alkawarin
taimakon bayinsa muminai, da basu nasara akan
abokan gabarsu.Don haka matukar akwai imani da
Allah a zukatan bayi to Allah ba zai tozarta su ba.

2-Tuba da Istigfari
da Komawa zuwa ga Allah.

3-Yawaita ayyuka na kwarai,saboda ayyukan
kwarai sukan kawo wa zuciya nutsuwa,kamar
yadda munanan ayyuka sukan kawo wa zuciya
bakin ciki da damuwa da kunci.

4-Yawaita Sadaka : musammam ma a boye
ba tare da an sani ba,ya tabbata a hadisi Manzon
Allah S.A.W ya ce “Aikata kyawawan ayyuka suna
kawar da munanan abubuwa,sadakar boye tana
kawar da fushin Ubangiji,sada zumunci yana kara
tsawon rayuwa, dukkan aikin alheri sadaka
ne, masu aikin alheri a duniya,su ne ma’abota
alheri a lahira,masu munanan ayyuka a duniya, su
ne masu ma’abota mummuna a lahira,farkon
wadanda za su shiga Aljannah su ne masu aikata
kyawawan ayyuka”.Dabaran i ne ya rawaito shi.

5-Addu’a:
ba don addu’a ba da mutane da yawa sun
halaka.Allah
madaukakin Sarki yana jarrabar bayinsa da bala’i
don su koma gare shi,su kaskantar da kai da
addu’a, idan suka koma zuwa gare shi,suka
kasakantar da kai sai ya yaye musu.

6-Umarni da kyakkyawan aiki da hana mummuna :
Allah ba zai halaka al’umma ba,matukar akwai
masu umarni da kyakkyawan aiki da hana
mummuna.

7-Nisantar Zalunci Allah ya halakar da al’ummu da
yawa saboda zalunci.Mafi
girman zalunci shi ne shirka da kafirci,sai
zaluntar bayin Allah a cikin dukiyarsu da
mutuncinsu da jininsu,mu nisanci zalunci mu
zauna lafiya.

8-Zikiri wato ambaton
Allah,da baki da zuciya da gabbai.Da ambaton
Allah ne zukata suke nutsuwa.

9-Neman ilimin addinin musulunci :Al’umma
tana tsira daga halaka idan akwai malamai a
cikinta, wadanda za su kama hannunta daga duhu
zuwa haske, daga shirka zuwa
tauhidi,daga bidi’a zuwa sunnah.Duk al’ummar da
ta bar ilimin addini ta shagala
da na rayuwa to tana tare da kunci da bakin
ciki da rashin kwanciyar hankali.

10-Hakuri da Juriya : Hakuri wajen bin Allah,hakuri
wajen barin sabon Allah, hakuri akan abin da Allah
yabkaddara,samun nasara yana tare da hakuri. .

*Allah ka kara mana hakuri wajen yi maka da’a, da
barin abin da ka hana, ka yafe mana
kurakuranmu*.


*_Gabatarwa_*:- Yusuf Ja'afar Kura

Daga 
Zauren
*Miftahul Ilmi*

Ga masu sha'awar shiga zauren *MIFTAHUL ILMI* a Whatsapp sai a turo da CIKAKKEN SUNA Zuwa ga lambar mu (07036073248) ta whatsapp.
Post a Comment (0)