INA MASU ZAGI DA CIN MUTUNCIN MUTANE???!!!
Anas Bn Malik, Radhiyallahu anhu, ya ce: Manzon Allah, sallallahu alaihi wa sallama, ya ce:
*_"Lokacin da aka hau da ni sama, na shude da wasu mutane suna da kumba (farce), su na kartan fuskokinsu, da kirjinsu; sai na ce: su wane ne wadannan Yaa Jibril?, sai ya ce: Wadannan su ne wanda suke cin naman mutane kuma suke keta mutuncin su"_*. Abi Dawud ya riwaito 4/269.
Don haka sai a yi hattara.
✍🏼Dan uwanku a Musulunci:
*_Umar Shehu Zaria_*
15/06/2018.
Daga: *ZAUREN FIQHUS SUNNAH*