*KAYATATTUN GIRKE GIRKE GROUP*🥐🥐🥐🥐
*STROMBOLY*🥐🥐🥐🥐
*KAYAN HADI*
Kwai
Butter
Sugar
Yeast
Gishiri
Fulawa
Man gyada
Baking powder
Madara mai dumi
*YADDA ZA KIYI*
Yar uwa da farko ki zuba fulawa, sugar, gishiri, yeast da baking powder a waje guda sai ki juya su da kyau, sannan ki sa butter da kwai ki juya dan ya hade jiki, ki dauko madara mai dumi ki juye a ciki ki kawo ruwa mai dumi kina zubawa kina juyawa, idan kwabin ya fara dan'ko sai ki dai na zuba ruwa ki cigaba da bugun sa kina juyawa, idan kika ga yayi tauri sai ki kara ruwa ki cigaba da kwabawa, sai kisa murfi ki rufe ki bari ya taso sannan ki yanka ki murza da kwalba dan yayi fadi (kamar shape din rectangle mai kusurwa hudu) sai ki zuba jajjagen kayan miya da dakakken nama ko kaza a ciki, sannan ki nannade shi kamar taburma, sai ki kama bakin biyu ki hade su (yayi kamar shape din doughnut)kisa hannu ki mammanna yadda zai kama sosai sai ki dauko wuka ko kitchen scissors ki tsatstsaga saman ki dauko kwai ki shafa mishi sama sama sai ki kunna oven idan ya fara zafi sai ki saka a farantin gashi ki gasa.... 😋😋😋
*KAYATATTUN GIRKE GIRKE GROUP*🥐🥐🥐🥐
Maman Usman
+2348032629076
Ban hana a tura wa yar uwa ko kuma group ba amma duk wacce ta canza min post ban yafe ba