KURAKURAI 40 NA SALLAR DARE

KURAKURAI 40 A SALLAR DARE

1. Cakudedeniyar maza da mata

2. Daga ido sama a lokacin adduar wutiri

3. Dagewa wajen yin sallar dare bayan barci ya galabaici mai yi

4. Daukan hoton video na sallar dare ko recording din adduar wutiri

5. Dauke-dauken hotunan sallar dare (selfie da makamantansa) da yada su a social media

6. Fifita yin sallar dare (a watan Ramadan) a gida maimakon bin jam’i a masallaci

7. Fita daga masallaci kafin a gama sallar dare ko kafin a yi wutiri

8. Fitar mata zuwa wajen sallar dare ba tare da bin qa’idar sharia wajen fitar ba

9. Gabatar da wa’azi na musamman a tsakanin raka’o’in sallar dare

10. Gaggawar yi wa liman gyara kafin ya tabbata ya yi kuskure ko ya manta

11. Karanta Al-Qur’ani da sauri (ba tare da tajweed ba) don a yi marmaza a sauka

12. Kasancewar karatun wani masallaci yana shiga cikin wani saboda karan loudspeaker

13. Kin bin sallar dare da gangan har sai an gama karatu ko an kusa ruku’u

14. Kin yin sallar dare a masallacin anguwarku da tafiya wani masallaci na nesa

15. Kiran sallah ko fadin (الصلاة جامعة) don sanar da lokacin sallar dare  

16. Kirkirar zikirori kala dabam-dabam wadanda ake yi bayan kowace sallama

17. Kokarin yin kuka da karfin tsiya don nuna tsoron Allah
18. Lazimtar yin saja’i a adduar wutiri

19. Maishe da sallar dare wajen neman taimako da tara sadaka

20. Qudurce cewa a daren LAILATUL QADRI ba a ganin komai sai Ka’abah!

21. Qudurce cewa bai halasta mata su je sallar dare ba

22. Qudurce cewa dole sai an sauke Al-Qur’ani a cikin kwanakin sallar

23. Qudurce cewa sai masallaci ‘kaza’ ko bayan limami ‘wane’ kawai zan yi sallah

24. Qudurce cewa sallar dare bidi’a ce kyakkywa

25. Rage yawan fitillun masallaci da tunanin wai in akwai duhu an fi samun natsuwa

26. Rashin sanin fiqihun yi wa liman gyara a tilawa

27. Rera addu’ar wuriti kamar yadda ake tilawar Al-Qur’ani

28. Rike Al-Qur’ani a lokacin sallah ga mutumin da ba 
limami ba

29. Sakaci da sallar asuba bayan an tashi sallar dare

30. Sanya sautin amsa kuwwa (loudspeaker) fiye da bukata

31. Sanya wa limamin sallar dare albashi ko biyan sa kudin jan sallar dare

32. Tsawaita addu’ar wutiri fiye da misali

33. Watsi da sallar dare bayan Ramadan sai Allah ya kai mu badi!

34. Wuce iyakar da sharia ta gindaya a wajen adduo’i

35. Yin adduar da aka fi sani da suna (دعاء ختم القرآن) watau (Adduar sauka)

36. Yin sallar dare a daren sallah (bayan an ga wata)

37. Yin sallar dare fiye da adadin raka’o’in da ya tabbata a sunna

38. Yin sallar wutiri ta yi kama da yanayin sallar magriba

39. Zaman fira (ana cikin sallah mutum ya yanke ya kafa fira da na kusa da shi ko buga waya)

40. Zuwa wajen sallar dare da darduma ko sallaya ta musamman

      Dr Kabir Asgar

Post a Comment (0)