ROWA

**** *ROWA✊🏼* ****


👉🏼 Rowa yana daya daga cikin abubuwan da su ke halakar da Dan Adam.
     Manzon Allah (S A W) ya ce: Bakar rowa wanda ta yi katutu a cikin zuciyar mutum, wanda kuma mutum ke biye mata.
   Duk abin da ka samu na rayuwa ka dauki wannan abin ba za ka yi wa Allah rowa da shi ba, ba za ka yi wa bayin Allah rowa da shi ba.
   Duk abin da ka mallaka ko wani musulmi yana iya amfanan wannan abin, ba tare da ka masa rowar wannan abin ba.

   Allah (S W T) ya ce, zan taimaka wa bawa matukar bawa zai taimaka wa dan uwansa.
   Duk wanda ya damu da damuwan wani to wallahi Allah bazai ta6a wulakanta shi ba.
   Amma ka dauka cewa, numfashinka da rayuwarka, da abin da kake samu naka ne da "yayanka, to da kai da "yayankan sai sun gagareka, kuma wallahi ku duba haka ne.
   Allah (S W T) yace, ku bautawa Allah karku hada shi da wani wajen bauta, ku kyautatawa mahaifa, ku mutunta musu, kar ka bari kana da abin da za ka rayu dashi mahaifanka su shiga halin ha ula'i, yan uwanka na jini Allah yace ka tallafa musu, kar ka bari wani dan uwanka ya shiga halin qaqani-qayi wai don kana tinanin qarshen wata yaya za ka yi.
  Maraya Allah yace ku taimake su, kar kubar wani maraya ya dai-daice a tsakaninku, kuma kun rayu da mahaifinsa da alheri, don mutuwar mahaifinsa yasa ya zama sanadiyar lalacewarsa da ta6ewarsa a tsakaninku.
  Allah yace da miskinai ku taimaka musu da makwabcinka na jini, saboda shi wannan dan uwanka ne na jini kuma makwabcinka ne.
   Annabi (S A W) ya ce, Ba da sadaka wa dan uwanka na jini sadaka ne kuma zumunci ne,
  Da kuma dan uwanka wanda unguwa ko office ya hada ku. Da abokinka ko matarka Allah ya ce ka taimaka mishi.
  Da matafiyi wanda guzurinsa ya kare, ko abin da damarku ya mallaka muku, Allah yace ku kyautata musu.
   Duk wani mai takama da alfahari da abinda Allah ya bashi, Allah ba ya son shi, Allah ya tsane shi.
  Allah yace wadanda ke rowa kuma suke umurtan mutane da yin rowa, suke 6oye abinda Allah ya basu na falala ba su so ma wani yasan suna da shi, Allah yace wadannan sun shiga uku ranar _(Alkiyama)._ Mun yi tanadi wa _(Kafirai)_ azaba na wulakanci a ranar _(Alkiyama)_ domin rowa dabi'ace ta *arna.*

   _Saboda haka yan uwa muyi kokari abinda muka karanta muyi aiki da shi domin mu samu tsira a duniyarmu da lahiranmu. Allah ya rufamana asiri yasa mu dace Ameen._



✍🏻 *Rubutawa*
_Ibraheem Khalil_

{08094000845}
Post a Comment (0)