SHIN HAR YANZU AKWAI SHARIFAI?

*SHIN HAR YANZU AKWAI SHARIFAI ???*
➖➖➖➖➖➖➖➖➖
مجلس خلفاء الراشد‎ين وعلى منهج سلف الصالحين
Daga
Majalisin
Khulafa'ir-rashidiin, bisa fahintan magabata na kwarai (salaf)
*::::*
Assalamu alaikum Tambaya ta itace
Shin har yanzu akwai sharifai Kuma menene ingancin tofin da sharifai suke yiwa wanda ya kone?
:
                     *****
:
Wa'alaikumussalam warahamatullah

Tabbas akwai sharifai kuma suna nan a Inda suke insha Allahu ta'ala sannan kuma nida nasan akwai masu da'awar cewa suma sharifai ne kuma sunayin wannan topi da sunan bada magani amma kuma qarya sukeyi su ba sharifan bane domin hanya mafi sauqi da zaki gane sharifi shine an haramta musu cin sadaka amma abun takaicin shine masu da'awar shariftaka din mafi yawansu cima zaune ne ana musu kirari cewa daga Allah se kanku ana basu sadaka kuma suna ci mafi wallahi mafi yawansu bokaye ne
.
Sanan basu tasirantu da wata dabi'a ba ta gidan manzon Allah Alaihissalam ba gingima gingiman 'yan Bid'a be kuma matsafa kaga mutum yana kunna wuta wai tahakane ake gane cewa sharifine naji kokuma wai wuta bazata qonashi ba wanna duk suna amfani da maganin wuta ne irin na maqera kabawa mutum sabulu yayi wanka a gabanka idan ya Isa Seya zo ya shiga wutar kaga yadda ze banqare.
.
Wannan musifar yayi yawa a garin kano domin unguwa ce damu guda da ake cemata sharifai kenan Kowa ka ganshi a unguwar shi sharifine kawai kuma duk gidajensu manne yake da hotunan wasu fasiqan mutane a kofar gidan bayan hadisi yana can acikin Sahihaini Annabi sallallahu alaihi wasalam yace mala'ikun rahama basa shiga gidan da yake akwai kare ko hoto a gidan.
.
To gameda topin da suke Allahu a'alam ban saniba.
.
*:::::*
_Almajirinku ne kamar koda yaushe_
 ```SANI ILYAS YAKASAI ```
_(Dan mama-Assalafy)_
________________________________
Yau
04-01-1440
13-09-2018
 Wats app
        +2349033206238
       +2347035269582
+2348063796175

🆓www.facebook.com/khulafaurrashidun
🌐 www.khulafau.cf
سُبْحَانَكَ اللَّهُمَّ وَبِحَمْدِكَ، أشْهَدُ أنْ لَا إِلَهَ إِلاَّ أنْتَ، أسْتَغْفِرُكَ وأَتُوبُ إِلَيْك
In-kaga gyra kasanar damu, inbaka ganiba, kana iya turawa awasu, dansu amfana !
Post a Comment (0)