SIRRIN SAURAYI ARANAR DA KUKAFARA
HADUWA
Rayuwar ‘Ya mace na tattare da Hadari muddan tun Ranar Farko da ta hadu da saurayi batayi kokarin Fahimtar wasu abubbuwa ba.
Abu na farko a kowace Ibada a Musulunci shine Niyya wanda kuma abu ne mai mahimmanci sossai a Rayuwar dan Adam, dan Haka idan a matsayinki na ‘ya mace kina da Niyyar yin aure ya kamata ranar da kuka fara haduwa da Saurayi har ya nuna Yana Bukatar ki bashi dama ki kula da wannan abubuwan kamin ki bashi dama.
Kamin ki fara neman fahimtar waye shi ki fara duba kanki tukunna, shin Wane irin shiga kikayi a wannan lokacin, sannan kuma a ina ne ma kuka hadu?
Idan har kinada Niyar yin aure ne kuma Saurayi ya same ki ya nuna bukatar shi na ki bashi dama toh a gaskiya fa Aure ba abun wasa bane ya kamata tun a wannan lokaci ki fara fahimtar da wane niya yazo, idan har kinyi shiga ce wacce ta nuna tsiraicin ki toh ki tabbatar maza da dama zasu neme ki ne domin sha’awa ba dan SO na asali ba.
Idan kuma har kun hadu ne a gidan Party ko Club toh ki tabbatar da ba a nan ake samun mazan aure ba, koda ya nuna miki ai da aure yake sonki kisa a ranki wannan zancen a baki kawai yake. Amma idan har kun hadu ne a Makaranta wanda kila yasan ki a aji ko kuma ya saba ganin ki a makaranta ya fahimci wasu abubuwa akan ki kamin ya nemeki toh ki tabbatar da irin wannan nema yafi haifar da abun azo a gani akan wanda ya bukaci ki bashi dama bayan kun hadu a gidan party ko dan ya ganki da wasu kayan da suka bayyana Tsiraicin ki.
Abu na gaba shine ki duba kiga wane irin Mutun ne shi
Zaki fahimci wane irin mutun ne daga natsuwarsa, Natsuwar mutun kuma ba abu bane na boye musamman idan kikayi al’akari da wane irin shiga yayi, Saboda a koda yaushe Sutura itace mutun. Ba wai anan ina nufin ko yasa kaya masu tsada ba, ina nufin yayi shigar kamala ne ko kuma shigar da ba ta kamata ba. Tun daga nan ya kamata ki fara dubawa kiga ko zakiyi alfahari da irin wannan saurayin a matsayin Saurayinki ko kuma Uban Yayan ki.
Dan Haka Mata ina kira da Mu kula sossai a lokacin da muka hadu da saurayi a ranar Farko da Muka fara Haduwa domin kuwa tun daga wannan ranar ake fara samun Kuskuren Zaben Abokin Zama. Sannan tun daga Ranar farko zaki fada mishi kin bashi dama amma bazaki sake sauraren shi ba sai yaje ya nema Izinin Iyayen ki.