ABOKAI NAGARI

✍🏻 *SHEAKH AMINU IBRAHIM DAURAWA KANO*

ABOKAI NA GARI 

Abokai iri uku ne :

1- Abokin tayi daɗi, abinda ya kawo shi abota da kai domin ya amfana da kai, ranar da yaga babu amfanin zai kama gabansa. 

2- Abokin aiki, wannan abota da shi, iya wajan aiki ne da zarar am gama aiki shi kenan sai kowa ya kama gaban sa. 

3- Abokin mai daraja mutunci, wanda zai kasance tare da kai, a dukkan mawayacin hali, ko kana da shi ko babu, shi yana kaunar ka saboda Allah kawai, ba domin wani abu na duniya ba. 
Wannan irin abokin yana da wahalar samu, idan ka samu irin sa ka riƙe shi da kyau. 

Idan za kayi abota kayi da masu hankali
Domin 
idan baka nan zasu kare mutunci ka. 
Idan basu ganka ba zasu nemeka. 
Idan ka samu zasu tayaka murna. 
Idan kayi kuskure zasu gyara maka. 
Idan za suyi addu'a ba zasu manta da kai ba. 
Idan baka da lafiya zasu duba ka suyi maka addu'a. 
Idan ka shiga wani hali zasu nuna damuwa da alhini. 
Idan sun ganka suna murna. 
Idan kayi kuskure za su yi maka gyara, cikin hikima. 
Idan zaa cuce ka zasu taimake ka.
Idan ka mutu zasu yi maka addua, kuma su taimaki iyalanka a bayanka.
Wanda ya rasa abokai na gari yayi asara. 
Allah ka bamu abokai na gari.

Shin muna da irin waɗannan abokan?

Post a Comment (0)