ZAN ƘARA AURE... 01


*💑ZAN QARA AURE // 01🙆🏻🕺*

Aure a rayuwar malam Bahaushe na nufin wata rayuwa da ake kullawa tsakanin namiji da mace, wace ake sa rai da cewa mutuwa ce kadai za ta iya raba tsakaninsu, tare da sanin cewa in wani zarafi ya datso kowa na iya kama gabansa, ko dai shi maigidan ya sauwaqe mata, ko kuma ita ta kai shi inda za a shiga tsakaninsu. Da zarar an daura aure komai na amaryar ya tashi daga kan mariqinta ya koma kan maigida, hada da ci da sha, matsuguni da wasu abubuwan rayuwa da suka zama dole, ciki har da ilimi da addini.

A duk inda aka ji cewa ana daura aure za ka ji ala-san-barka ga ma'auratan guda biyu, koda kuwa mutum bai san daya daga cikinsu ba, ango da amarya da uwayensu da sauran tarsashin jama'a duk sukan yi ta murna, sashin ango na farin cikin cewa dansu ya zama babba, shi ma yanzu ya zama magidanci, uwayensa ko ba su fadi ba dai dayan abubuwa biyu ne ke bayya musu: Kodai yanzu zai taimaka musu a kan al'amuran rayuwa, ko kuma zai kama gabansa su ji da sauran qanninsa.

Duk da haka fahimta kan bambanta a lokacin da mutum ya ce zai qara aure:-

1) 'Yan boko wadanda ba qanin iya bare na baba, su ke fara tofin ala-tsine da kawo wa angon talauci kusa, wasu har da maganar karatun yaran da za a haifa da kama musu hayar dakin da za su riqa kwana da gazawa wurin tarbiyantar da su duk da cewa ko auren ba a daura ba bare ta sami ciki bare kuma a kai ga wadannan abubuwan da suke zayyanowa.

2) Wasu daga cikin yayyin angon, maza kenan, masamman ma wadanda suke da mace guda, su ma sun kasu kashi biyu, wasu suna kallon zarafin angon ne, da kuma irin qarfinsa na qara auren ko gazawa, wasu kuma sun kulle idanunsu kan cewa bai isa ya qara aure a wannan lokacin ba, koda kuwa ba su da wata kataimaimiyar hujja a hannunsu.

3) Sai yayyin angon wato mata, su ma sun kasu zuwa kashi biyu, wasu kamar mazan ne ta wurin lura da yadda mutum yake riqe da ta gida, in gazawarsa ta bayyana sai ka iske suna yin fito na fito da qarin auren, wasu kuwa shaquwarsu da matarsa take sawa su taya ta kishi, a irin wannan yanayi angon kan jima kafin ya shawo kansu, wani sa'in lamarin kan kai ga murje idanu don dai ya isa zuwa ga manufarsa.

4) Sai 'yan sa ido, wadanda ba wani abinda ya hada su da mutum, amma su shiga tsakiya su nemi bata komai, koda kuwa ba wata riba da za su ci.

5) Uwargida kuwa (sai daidai) samsam ba ta qaunar ta ji an ce za a yi mata kishiya, duk kuma wani bayani da za ka yi mata don ka gamsar da ita cewa auren zai iya zama alkhairi a gare su bata lokacinka kawai za ka yi, ko fahimtarka ba za ta yi ba, in ka ji mace ta tsani wani malami, ko ta kira shi munafuki, qila ya kwadaitar da maza ne kan qarin aure, qiyayyar mata da qarin auren ya kai ga yi wa uwargida jaje na masamman kamar ta rasa wani, a hankali ya bayyana a matattararsu cewa qarin aure ko yin kishiya tamfar wata fitina ce wace ba yadda za a yi da ita.

6) Uwayen uwargida kan tsaya a gefen diyarsu ne, shahararriyar hujjarsu ita ce ba a san abinda amaryar za ta shigo da shi ba, koda kuwa yarinya ce qarama wace ba ta ma gama sanin duniya ba, ko wata saliha da maqwabta suka shede ta kan zama lafiya, wasu uwaye mata ba sa maganar cewa amaryar za ta kore su, matsalolin gida ne suke fitowa da su, masamman inda mijin diyarsu ya gaza, in ba a yi sa'a ba nan za su rada wa diyarsu yadda za ta bata auren ta wajen fadin gaskiya da qarya a kan maigidan don dai su bata sabon auren, in shedan ya sanya wa aikinta albarka sai ka ga sun ci nasara.

7) Akwai halin da mutum kan yi jinkirin qara aure har 'ya'yan da suka haifa tare da uwargidan su girma, a irin wannan hali in lamarin ya zo da matsala sai yaran su goya wa uwarsu baya a yi ta kwasan rigima, ita da yaranta a hannu guda, maigidan kuma a daya hannun, yaran kan tsaya kai da fata kan cewa uban bai isa ya kawo wata matar cikin gidansu ba, na taba ganin wadanda suka saka masa sharadin sai dai ya auro sa'ar mahaifiyarsu, wasu kuma suka turje kan cewa ba za a yi wa mahaifiyarsu kishiya ba, a kan ci nasara wani lokaci, amma ba kullum ake kwana a gado ba, galibi idan namiji ya yi niyyar qara aure zai yi abinsa, koda kuwa zai yi fito na fito da kowa.

A cikin wannan dan littafi da za mu bi, muna so ne mu ga wasu dalilai da suke sanyawa mutum ya yi sha'awar qara aure, tare da sanin cewa abubuwan da yawa matuqa, duk yadda ka lissafa wa mutum dalilan qara aure in ba ka yi sa'a ba sai ya ambato maka wani abin daban wanda bai da alaqa da abubuwan da aka lissafa, mu dai za mu lissafo su, amma mun sani cewa namiji in ya rasa dalilin da zai ce dominsa ne zai qara aure hakan ma wani dalili ne mai qarfi da zai yi din, a taqaice komai ma na iya zama dalilin da zai sa namiji ya qara aure, kenan wannan rubutu zai taimaki mata sosai ta wurin sanin yadda za su kare gidansu.
Post a Comment (0)