ITA MACE TAURIN KAI, KAI KUMA NAMIJI GIRMAN KAI

*ITA MACE TAURIN KAI, KAI KUMA NAMIJI GIRMAN KAI*

🍂 Dole ne sai Mace ta ajiye taurin kan ta, kai kuma namiji ka ajiye girman kan ka, a lokacin da sabani yashiga tsakaninku, tukunna afara samun zaman lafiya .

🍂 Wasu lokutan idan mace tana yimaka magana, to kasani fa daga zuciyarta maganar nan take. Kuma sai kaga ta doge akan hakan, saboda ita zuciyar mace idan har tana bukatar abu, to fa sai ahankali. 

🍂 Kamata yayi kai kuma karika yimata magana da hankalinka, domin gudun biye mata sai abu kuma yazama tashin hankali. Kanuna mata kai namiji ne, kana da zuciyar da zata iya daukar hakurin nauyin bacin rai.

_Allah yakara tabbatar da zaman lafiya atskanin ma'auratanmu._


✍🏻 *Idris M Rismawy*
Rismawy86@gmail.com

Post a Comment (0)