MUNANAN KALAMAI

    💧💧💧💧💧💧💧💧💧💧
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

     DARUSSAN RAYUWA


  ࿐​ ​PRODUCTIVE WRITERS ASSOCIATION࿐​

༄༄ PWA ༄༄

 ➖➖➖➖➖➖➖➖➖
                ✹••✹••✹••✹••✹••✹••✹
     ʂɬơrყ/wrıɬɛɛŋ     
            ɮʏ✍🏻:
👉🏻© ɧãımãŋ Řâééʂ ✹••✹••✹••✹••✹••✹••✹
 ➖➖➖➖➖➖➖➖➖

                    Fitowa ta 04 
   
          MUNANAN KALAMAI 

Wannan wani ɗan gajeren labarin wani shugaba ne da aka taɓa yi a Ƙasar Indiya, shi ne ya bada labarin sa da cewa:

"Watarana, lokacin da nake ɗan ƙarami, Mahaifiyata ta dawo daga aiki a gajiye, sai ta fara ƙoƙarin haɗa mana abin da zamu cit. A yayin toya abinda take toyawa ne ta ƙona abincin. Ni kuma lokacin ina zaune a gefe guda ina jiran inji irin ƙorafin da babanmu zai yi idan yaga an kawo mishi abinci a ƙone. To amma bisa mamaki, sai naji bai ce komai ba kuma ya cinye abincin duka. Ina ji Mahaifiyata tana bashi haƙuri bisa ƙonewar da abincin yayi, amma sai yace mata babu komai, dama can yana son ƙonannen abinci. 

Yayinda dare yayi naje zan masa sai da safe, sai na tambaye shi dangane da batun da yayi na son ƙonannen abinci. Anan ne yace dani: "ya kai ɗana, mahaifiyarka a gajiye take Yayinda ta toya abincin nan, ba lallai bane ƙonannen abinci yayi min illa a cikin jikina, amma munanan kalamai suna iya tarwatsa zuciya". 

Yace tun daga wannan ranar ya koyi saita harshensa akan jama'a, domin ya fahimci cewa kalma ɗaya tak tana iya tarwatsa duk son da mutum yake yi maka a cikin zuciyarsa. 


Don haka ya kamata mu dinga nuna godiya da yabawa ga mutanen da suke ƙoƙarin ganin sun kyautata mana, kuma mu basu uzuri Yayinda suka yi kuskure domin Ɗan Adam ajizi ne 

<••••••••••••••••••••••••••••>
      ɧãımãŋ Řâééʂ  
<••••••••••••••••••••••••••••>
       08185819176
Twitter: @HaimanRaees 
Instagram: Haimanraees 
Infohaiman999@gmail.com

Miyan Bhai Ki Daring 


Post a Comment (0)