SAURAYI ƊAN GANGANCI


SAURAYI DAN GANGANCI

Wani saurayi ne yaje wajen budurwar sa hira. Suna cikin hirar sai NEPA suka kawo wuta. Sai ya tambaye ta yace yanaga ko'ina da wuta amma banda gidan ku? sai tace wlh lokacin ana ran sama shine iska ta tsinke WAYAR. Sai yace to meyasa baku kira Yan NEPA sun gyara ba? sai tace wlh mun kira su sunce zasu zo gashi yau har kwana 2 shuru. Sai yace bakomai, abinda za'aji shiga gida kisa YARA SU FITOMIN DA TSANI DA Kuma FILAYA. Sai tace haba kawai ka barshi za'a gyara, SWEET HEART kaga ba aikin ka bane. Sai yace haba MY LOVELY ai abin duk bogi ne. Aka fitomai da TSANI DA SAURAN KAYAN AIKI ya hau FALWAYA ya fara aiki. Can zuwa wani dan lokaci sai budurwar sa taji yayi wani MUGUN IHU HADE DA KARA wuta ta jashi ya fado cikin KWATA A SUME. bayan ya farfado daga suman da yayi, ya tashi zaune yana daga kansa sai yaga budurwar sa da baban ta da babarta da yaran gidan gaba 1 da kuma sauran yaran unguwar suna mai sannu. can saiji yayi wata karamar yarinya kanwar budurwar sa tace: LAAAAAA, AUNTY SAURAYIN KIYAYI KASHI A WANDO.

HAHAHHAHAHAAHHAHAHA

Wai idan kaine yazakayi????
Post a Comment (0)