SHARHIN FIM ƊIN ZERO 0⃣


SHARHIN FIM ƊIN ZERO 0⃣ 


Zero fim ɗin soyayya ne da aka shirya shi a cikin harshen Hindi a Ƙasar Indiya a shekara ta 2018 . Shirin yana ɗauke ne da labarin wani Wada mai suna Bauua Singh tare da irin yadda rayuwa ta sauya masa ba tare da tsammaci hakan ba. 


MA'AIKATAN SHIRIN 

Bada Umarni: Aanand L. Rai

Ɗaukar Nauyi: Gauri Khan

Rubuta Labari: Himanshu Sharma

Tsara Labari: Himanshu Sharma

Taken Shiri: Ajay−Atul
Tanishk Bagchi

Mai Horar da 'yan wasa: Manu Anand

Tacewa: Hemal Kothari

Kamfanin Da Suka Shirya: Red Chillies Entertainment & Colour Yellow Productions

Yaɗawa: Various & Yash Raj Films

Ranar Fita: 21 December 2018

Tsayin Shirin: mintuna 164

Ƙasa: India 🇮🇳 

Harshe: Hindi 

Kasafi: ₹200 crore

Kasuwanci: ₹186crore

 Zero shi ne fim ɗin Shah Rukh Khan da aka fi kashewa kuɗi fiye da kowanne a tarihin Fina Finan Jarumin. Tun cikin shekarar 2012 Anand ya soma tunanin yin wannan fim, amma ba'a fara komai na shirin ba sai a 2016. Da fari an sa wa wannan fim suna Katrina Meri Jaan ne yayin da ake aikin sa, daga baya kuma aka yi ta canja masa sunaye har dai daga Ƙarshe aka tsaya a kan Zero.

An fara ɗaukar wannan shiri ne a garin Mumbaai a cikin watan Mayu na 2017, kuma wannan shiri shi ne fim na Ƙarshe da Fitacciyar Jaruman nan wato Sridevi ta fito a cikin sa, domin kuwa ta kammala ɓangarenta na fim ɗin ba da jimawa ba ta mutu. An kammala ɗaukar fim ɗin ne a birnin Orlando a 2018. 

An saki Zero a ranar 21 ga watan Disamba na 2018, shirin ya samu yabo da suka a lokacin da ya fito. Masu sharhi da yawa sun yaba wa kayan aikin da aka yi amfani da su a cikin shirin, sannan sun kuma yaba wa irin kafcen da Shah Rukh Khan da Katrina Kaif suka kafta. Yayinda a gefe kuma suka yi wadai da irin yadda labarin ya zo. Shirin ya kawo kuɗi kimanin ₹90.39 a cikin kwanaki bakwai da fitarsa kasuwa, amma daga nan sai ya kasa taɓuka wani abin azo a gani. Shirin ya samu damar shiga guraben gasa na Filmfare Awards har waje bakwai, ciki har da Best music direction, Best Actor wa Shah Rukh Khan da kuma Best Supporting Actress wa Katrina. Kamfanin Red Chillies VFX ya samu nasarar lashe gasar Best Special Effects da wannan shirin 

LABARIN FIM ƊIN 

Bauua Singh wani Wada ne ɗan kimanin shekaru 38 a duniya da ke zaune a Meerut. Duk da iya ƙoƙarin da wannan Wada yayi na son ganin yayi aure, ya gaza auruwa. Yayi aiki da mahukuntan Hukumar ɗaura aure har ya gaji, amma duk babu sa'a. who has trouble finding a marriage partner. A Ƙarshe dai ya samu soyayya a tattare da wata mace mai suna Aafia Yusufzai Bhinder. Aafia ta kasance tana aiki ne a hukumar kuma tana fama da lalurar cerebral palsy. Bayan Soyayya ta watanni biyar, sai Bauua ya fita harkar Aafia, amma ita Aafia saboda son da take yi mishi har gida ta biyo shi, hakan yasa iyayensa suka shirya auren su kai tsaye. 

A ranar da za'a ɗaura auren ne abokin , Bauua mai suna Guddu ya bashi labarin cewa sunansa ya fito fa a cikin jerin sunayen waɗanda za su shiga wata gasar rawa, kuma duk wanda ya lashe gasar zai samu damar haɗuwa da Babita Kumari tare da sauran wasu Jaruman Bollywood. Kasancewar Bauua ya sha alwashin haɗuwa da Babita, nan take ya gudu daga wajen bikin ya tafi wajen wannan gasa ya bar mutane kasaƙe cikin rashin sanin me ya kamata su yi. 

Bauua ya samu nasarar lashe wannan gasa kuma ya haɗu da Babita a wani shagali inda wasu fitattun Jaruman Bollywood suke tare da ita. Bayan ya nuna ƙwarewarsa a fagen iya cankar abinda ke zuciyar mutune ta hanyar nazarin fuskokinsu, sai Babita ta samar masa aiki. Daga nan kusan duk inda zata ce su kan tafi tare ne, kuma har ya taimaka mata sun shirya da tsohon saurayinta mai suna Aditya Kapoor, wanda a da can ta zarge shi da cewa yana cin amanarta. 

Watarana sai Bauua ya baiwa Babita labarin Aafia. Ita kuma sai ta faɗa mishi cewa ita ma iyayenta Wadanni ne, kuma mahaifinta ya yaudari mahaifiyarta ne ya tafi ya bar su. Ta faɗi hakan ne domin ta bayyanawa Bauua Kuskurensa na rabuwa da Aafia. Da dai ya fahimci shirmen da yayi, sai ya tada balli a wajen wani shagali da Babita ta shirya, hakan yasa Babita ta kore shi kuma ta yanke duk wata alaƙa da Aditya domin ta gano cewa har yanzu yana cin amanarta. 

Bauua da Guddu sai suka tafi birnin New York inda Aafia take halartar wata Semina a can. Bauaa sai ya hargitsa taron saboda ya haɗu da ita. A nan ne mahaifin Aafia ya bayyana mishi cewa tana ɗauke da juna biyu kuma nashi ne, hakan ne ma yasa yake son aurar da ita. 

Hankalin Bauua ya Matuƙar tashi har ma ya yanke shawarar barin gari, amma duk da haka sai ya yi ƙoƙarin sake jaraba sa'ar sa. Bayan sun sake haɗuwa da Aafia a NSAR nan ma sai ta ƙi karɓar sa, daga nan sai Bauua ya shiga cikin mutanen da ke neman gurbin shiga tawagar waɗanda za'a aika daular Mars. Bayan ya wahala Matuƙa, a Ƙarshe dai ya samu an zaɓe shi Yayinda shi kuma guddu ba'a zaɓe shi ba. 

A ranar da za'a yi wannan tafiya ne Aafia wacce ake sa ran zata auri abokin aikinta Srinivasan ta rabu da shi. Sannan ta isa wajen da su Bauua za su tashi, a nan ne ya tabbatar mata da cewa yana son ta a koda yaushe. Atisayen yayi kyau kuma sun samu damar tashi lafiya. 

A wani labari da Aafia ta bayar, ta tabbatar da cewa Bauua ya samu damar isa daular Mars, har ma ya turo saƙon bidiyon kansa daga can. Amma a hanyarsa ta dawowa sai jirgin ya ɓace a sararin samaniya. Kasancewar Aafia ta kashe aurenta, sai ta kasance mai tsumayarsa. Bayan shekaru 15 da da faruwar hakan, wani ofishin samaniya na birnin Sin ya samu sigina daga jirgin da Bauua ya tsere a cikin sa, tare da bayyana cewa Bauua yana raye.

JARUMAN SHIRIN DA MATSAYIN DA SUKA FITO DA SHI A CIKIN SA 

* Shah Rukh Khan = Bauua Singh

* Anushka Sharma = Aafia Yusufzai Bhinder

* Katrina Kaif = Babita Kumari

* Mohammed Zeeshan Ayyub = Guddu Singh

* Tigmanshu Dhulia = Ashok Singh

* Sheeba Chaddha = Beena Singh, 

* Brijendra Kala = Pandey

* Abhay Deol = Aditya Kapoor

* R. Madhavan = Srinivasan

MASU FITOWA TA MUSAMMAN 

* Salman Khan

* Sushrii Shreya Mishraa  

* Kajol

* Rani Mukerji

* Sridevi

* Alia Bhatt

* Karisma Kapoor

* Juhi Chawla

* Deepika Padukone

* Ganesh Acharya

* Remo D'Souza

* Arjun Kapoor 

* Javed Jaffrey 

* Mallika Dua 

* Ditya Bhande 

* Natasa Stankovic 

* Rajat Sharma 

WAƘOƘIN FIM ƊIN 

1. "Mere Naam Tu" 
2. "Issaqbaazi" 
3. "Husn Parcham" 
4. "Ann Bann" 
5. "Tanha Hua"
6. "Heer Badnaam" 
7. "Duma Dam Mast Kalandar" 

# HappyBirthdaySrk
# NASRUN MINALLAAHI ƘAREEB
# SRKUNIVERSENIGERIA
# SHAHRUKHKHANFANSNIGERIA 

<••••••••••••••••••••••••••••>
      ɧãımãŋ Řâééʂ  
<••••••••••••••••••••••••••••>
       08185819176
Twitter: @HaimanRaees 
Instagram: Haimanraees 
Infohaiman999@gmail.com

Miyan Bhai Ki Daring 
Post a Comment (0)