*_💑ZAN QARA AURE // 03🙆🏼🕺🏼_*
.
*_ME YA KAMATA SU GANE?_*
Gaskiya ko shago mutum ya samu yana sayar da kaya shi kadai in wani ya ce zai bude kusa da shi dole ya ji wani iri, don komai yanzu za a raba 2, dole ya fara qoqarin kawo duk abinda ake nema, ya iyakance farashin kayan, ya sami wani salo na magana da masu sayensu, ya gyara ma'amallarsa da kowa, in ma ba ya jawo hankalin mutane kusa da shi dole ya fara, in aka dauki gidan aure a matsayin wurin samun abubuwan more rayuwa ko mallake namiji to mace ba za ta so kishiya ba don za su fara sanya gasa a tsakaninsu, in ta so wace ta fi iya abinda ake so ta riqe gida, idan kuwa mutum ya zama mai taimakon jama'a ta wurin hidimar da yake yi musu, kuma bai neman komai a hannunsu, tabbas zai buqaci mai taimako a lokacin da aka ce za a kawo masa wani.
.
A bisa wannan fahimtar in mace ta fahimci aure a matsayin ibada, tana neman dacewa a wurin Allah ba ta damu da wani abu na duniya ba tunaninta zai koma can wajen ladar ne, mace ba ka raba ta da kishi, matan Annabi SAW sun yi kishi, amma ba don zai auro wata ba, ko don qwace wa wata gida, kowa so take ta sami ladar hahira, wannan kuwa dabi'a ce, sai dai in wata ta tsaya kan ba za a auro mata kishiya ba, kuma ta ce matan Annabi SAW ma sun yi kishi gaskiya ba su yi adalci ba, don ba a kan haka suka yi ba.
.
Wanda ya zauna a qasashen Larabawa ya zo kuma ya ga 'yammatammu a Nigeria wadanda suke neman miji zai ce Alhamdu lillah, abu ne da ba sai an gaya maka ba, mata sun yi yawa yanzu a duniya, makarantu, kasuwanni, motocin sufuri da sauran wurare duk mata ne, ga kashe-kashen da muke fama da su na maza, yaqoqi, bama-bamai, ko a tara su ma a bindige, hatta hatsarin mota yanzu maza sun fi mutuwa a ciki, kenan banda qaruwar hayayyafar mata, akwai mutuwar maza, yawan mata na rubanya ta maza in har ba za a ci gaba da auren mata biyu zuwa hudu ba, wasu matan za a haramta musu aure har abada, ba wai ba sa son yi ba ne, saboda mazan ne ba sa son su aure su.
.
Na taba miqo tambayata inda na ce macen da ta wuce shekara 35 ba miji meye sunanta? Gaskiya babu wani suna sananne wanda mutane suka saba aiki da shi, da wannan za a ce babu jinkirin aure har zuwa rabin rayuwa a al'adarmu, in ma akwai to yanzu ne yake faruwa, dole masana su natsu su samar da sunan macen da ta tsufa ba ta sami miji ba, a hirar da muka yi da wata Balarabiya ta tambaye ni sunan macen da mijinta ya mutu, da wace aka sake ta, na ce sunansu Bazawara , tana ta jin dadi, ta ce "Kun yi sa'a" su a wajensu in dai aka saki mace qila sai dai a nemo wani dan uwa a hada ta da shi, amma samun miji na wahala.
.
Na taba jin wani dan ajimmu yana magana da wata Balarabiya tana gaya masa cewa damar da ta samu kenan na aure, matar ta shafe shekara 45 ba miji, tana roqonsa da cewa in dai ya tsaya a kan wani mutuminsa har aka yi auren za ta ba shi wani kaso mai yawan gaske daga cikin sadakinta, ni kaina lokacin da nake da shekar 35 wani likita ya taba cewa zai tsaya min na auri wata 'yar shekara 45, ya kuranta cewa yarinya ce qarama kuma ko auren fari ba ta taba yi ba, kai har an kai ga cewa a yi auren ni ina Nigeria ita kuma tana qasarta, in na sami kudi na kawo mata ziyara, ita ma in ta samu ta zo ta yi 'yan shekaru ta koma, duk da wannan matsalar ta wahalar samun miji mata sun kasa fahimtar cewa su suke haifar wa kansu da matsalar, mace na da 'ya'ya mata har 6 a gabanta amma tana cewa ba shegiyar da ita isa ta aure mata miji.