ZAN ƘARA AURE... 02


💑 *_ZAN QARA AURE // 02_* 🙆🏼🕺🏼
.
*_ME YA SA SUKE QIN AUREN_*
.
Wani sa'in in ka nemi ku tattauna da mata kan dalilin da ya sa ba sa qaunar su ji mutum ya ce zai qara aure hujjoji biyu za su ba ka, ta farko dai za su ce maka "Kana cikin zaman-zamanka da mijinka da 'ya'yanka lafiya wata shegiya daga waje za ta zo ta bata maka gida" wato dai akwai tsoron cewa ta wajen in ta shigo ba abinda za ta yi sai qoqarin korar ta ciki, shi ya sa ma za ka ji suna cewa "Sai ki qara da haquri don yanzu za ki ga abubuwa" wannan maganar za a yi ta ne koda kuwa mai yin ba ta taba ganin amaryar ba ba ta ma san ta ba.
.
1) Na biyu kuma za a fara fadin cewa "Wanda bai iya daukar nauyin mace guda ba ma wai shi ne yake neman wani auren?" Ko matar da kanta ta fado irin dawainiyar da take yi da karatun yaranta ko abin ma da za su ci, wanda maigidan ba abinda ya dame shi da gidan, ba wannan ne babban abinda yake damun mata ba gaskiya, koda yake sun fadi ne a babin cewa bai iya riqe daya ba ta yaya zai ce zai qaro wata? Kamar dai suna taimakon wace za ta shigo ne don kar ta sami kanta a cikin matsala, amma a zahiri wani qoqari ne na barin uwargidan ita kadai a cikin gida, in ma wahalar ce ta kashe ta, mata ba sa son kishiya, wata za ta gaya maka baro-baro duk abinda kake so za ta yi maka amma kar ka kawo maganar kishiya, shekara 3 kenan da suka wuce inda wata 'yar boko take ce wa maigidanta bai da dalilin da zai qara aure, in kuma don ta tsufa ne ai yana yara, ko qaramar za ta yi masa duk abinda yake so bare sauran.
.
Idan uwar 'ya'ya za ta yi akuyanci da 'ya'yan cikinta a kan qara aure, to kuwa abin ya kai yadda ya kai, wannan dabbanci ne babu ko tantama, koda yake dan boko zalla ga addinin amma bai da rabo ko na sisin kwabo, ina Sudan wani abokina ya ce zai yi aure, yayyinsa mata suka yi masa ca! Har wata take cewa zai tsofar da kansa a banza, ta qara da cewa in matan ne suke tsole masa ido ga sunan bar jak a gari kamar jamfa a jos, dole ne sai ya yi aure? Kar ka yi mamakin irin wadannan matan, kusan wallahi gwara su da wadanda za su dauki wuqa su burma wa namiji don ya ce zai qara aure, galibi ko kaza mace ba ta iya yankawa, in za ta yi kisan kai don qin kishiya, kuma wanda take tutiyar qaunarsa saman kowa a duniya lallai qiyayyarta da hakan ta shahara.
.
Lamarin qarin aure abu ne da mutum zai duba zarafinsa ya yi bitar kansa sannan ya yanke hukuncin ci gaba ko dakatawa, a jiya 17/10/2019 nake tattauna irin wannan matsalar da abokan aikina, suke cewa zama da mace daya kashe namiji yake yi, domin ba zai sami cikakkiyar damar da zai nuna mazantakarsa ta fuskar dabi'a ba, kowa ya fadi hujjarsa da dalilinsa wanda za mu tattauna wannan a hankali in Allah ya yarda, amma abin tambaya anan: Me ya sa mata ke canjawa gaba-dayansu a lokacin da namiji ya sake sabon aure?
Post a Comment (0)