ZAN ƘARA AURE... 07


*_💑ZAN QARA AURE // 07🙆🏼🕺🏼_*
.
*_GASKIYA MAI DACI_*

Mace ba ma ita kadai ba duk wanda ya rabu da abokin zamansa dalilin saki ko mutuwa bayan da yana jin dadin zama da shi zai so a ce ya kuma samun kamarsa ko ma sama da shi, zai yi kyau mace ta sa idon lura sosai a batummu na yau, yana da wahala amma shi ne gaskiya, na taba yin wannan maganar a baya sai zawarawan suka zaci ban son riqon dan wani ne, sam ba haka take ba, na dai nuna kuskuren da 'yan uwan miji suke yi na barin mace da yaran dan uwansu, ko na macen da take dagewa sai an bar mata yaran, a qarshe ta yi ta zagin an qi taimaka mata.
.
Wani sa'in tabbas macen ke hanawa, qila abinda 'yan uwan mutum ke hangowa kenan su dage kan ba zai auri 'yar gidan wane ba don ba su da mutunci, in mutum ya koma ga Allah kamata ya yi 'yan uwansa su kula da tarbiyar yaransa, mace ba za ta iya ba da duk abinda ake buqata na tarbiyya ba, matsalar ba ta kudi ce kawai ba, akwai gudummuwar da namiji ke badawa game da tarbiyyar yara, mace ba ta iya ba da shi, kamar dai yadda namijin bai iya ba da na macen.
.
Yanzu in mutum ya rasu sai ka ga mace ta kwaso yara kab dinsu ta nufi gidan ubanta da su, wata ma ko rabuwa ta yi da mijin abinda ke faruwa kenan, wai ba za ta bar su a cutar da su ba, tana ganin za ta tarbiyyantar da su ita kadai har su zama mutane, sai dai da yake ba aikinta ba ne takan sha mugunyar wahala har a kai ga ta fitar da abinda yake cikinta, wata ta yi zagin 'yan uwan mijin wai sun qi taimaka mata, babban abin haushi ma wace mijin na da rai ta kwashe yaran ta tafi da su, shi ya auro wata matar tana haihuwa masa suna rayuwa cikin kwanciyar hankali, ke kina ta famar wahala da yara sun hana ki yin wani auren, ga mummunar tarbiyyar qin mahaifinsu kin dasa musu.
.
Ba abinda macen da ta kwaso yara take so sai ta sami namijin da zai riqe su tsakani da Allah, ya kuma sa ido a kan yaranta, sai dai ba nan gizo yake saqa ba, duk wanda zai zo neman aurenta za ka iske yana da wasu yaran a gabansa, akwai buqatar samun yalwataccen matsuguni na yaranta da nasa gaba daya, sai abinci da sutura, 'yan matsalolin yau da kullum duk suna ciki, ga kudin makarantar yara na boko da Islamiya, qila makarantar ma sai sun hau mota.
.
Abin lura a ciki wadannan yaran lokaci guda kika taho masa da su, kin ga akwai matsala in bai shirya yadda zai gwama zarafin tarbiyyan ba, za ki ga maza da dama suna tambayar in bazawarar da suka gani tana da yara a gabanta, ba qyamar ruqon dan wani ba ne, damar da za a riqe din ne, wani yana da shi wani babu, ni dai na taba ganin wanda ya auri wata mai da daya babba, ya shigar da shi cikin iyalansa a qarshe ya aura masa qanwarsa ya ajiye su a gidansa, sannan na taba ganin wanda maqwabcinsa ya rasu ya bar mata 3, ya tambayi ta farkon, babbar kenan, dake da 'ya'ya 6 ko za ta aure shi, ta qi, ya tambayi ta biyu mai 'ya'ya 4, ita ma ta qi, sai yarinyar mai jini a jika ga hasken fata da yara biyu, bai neme ta ba, don ba ta da abinda yake nema, wato taimakon marayun.
.
Ba labari aka ba ni ba, na rayu da shi wuri guda na san shi ba sanin shanu ba, 'yar uwa zan ba ki shawara; ki yi haquri ki bar yarannan a wurin mahaifinsu in auren ne ya rabu, zancen kishiya sau nawa tana azabtar da yara su zo su taimake ta da ma yaranta a qarshe? In ma mutuwa mijinki ya yi ki bar wa 'yan uwansa, wallahi ba mai hana wani arziqin da Allah ya tsaga masa, kuma ke ma kina tare da yaranki a duk inda suke, lokacin ne ma za su so ki sosai, don in sun zo inda kike za su daban, kuma za ki yi musu duk abinda za ki iya. 
.
Abin sirri ne, in kika bar su a gidansu wanda duk ya zo tambaya za a ce kina da yara amma suna gidan ubansu, nan da nan za ki sami miji, dole dai uwa ta amsa sunanta koda uwar gwaza ce, kamar yadda na ce ne kina gidan mijinki za ki riqa taimakonsu sama da yadda suke gabanki, sannan za su riqa zuwa wurinki kullum kina ganinsu kina kwantar musu da hankali, wannan fa in kin yi niyyar sake aure kenan, ba mazan ne babu ba dabara ce ba ki da ita, wani namiji ne zai zo gidanku ya gan ki da yara a gaba kuma ki ce gidansa za ku duka? Wallahi na ga wace mutanen kirki suke ta zuwa mata amma duk in suka bincika suka ji tana da yara kowa sai ya kama gabansa, ita kuma tana ta kukan ba sa zama, bayan abinda ke koransu na tare da ita.
Post a Comment (0)