ZAN ƘARA AURE... 08

*_💑ZAN QARA AURE // 08🙆🏼🕺🏼_*
.
*_KAFIN KA FARA TUNANIN_*

Auren fari abu ne mai sauqi, haka ma in mutum ya rasa matarsa a dalilin rasuwa ko rabuwa, duka dai zai zauna da mace guda ne, in za ka iya ba ta haqqoqinta na ci da ciyarwa kamar yadda ake fadi a dunqule, kuma ka ba ta sutura da matsuguni shikenan ka gama komai, sabanin a ce akwai wata matar da za ka qaro, galibinmu maza ba mu san wannan ba, gaskiya ga namiji mai son qara aure ba kawai in yana da abincin da zai ba su da sutura da za suka, da matsuguni shikenan ya gama komai ba.
.
Dole sai yana da zarafin da zai iya daidaita su a zauna lafiya, da yawan maza na qara aure bayan ba su da qudurar da za su iya daidaita zamantakewar matansu, masamman wadanda fitinar ta farkon ta sa ya yi tunanin qarin auren, rarrabuwar kan mata kan haifar da rugujewar gida gaba daya, ya bata tarbiyyar yaran, a sami tabkekiyar baraka tsakanin maigida da 'yan uwansa masamman uwayensa, in ba a yi dace ba matan duk su shiga bokaye, in har hakan ta faru, to 'ya'yanka sai a hankali, sai dai a nemi kariyar Allah kawai amma an riga an yi nisa.
.
Wata rana na ji wasu mata suna hira kan wani gida yadda maigidan ya kasa riqe gidansa, nan da nan wata a cikinsu take cewa "Ragon maza ne wallahi, da a ce maigidammu ne wallahi kulle qofar zai yi ya yi mana dukan tsiya, tabbas da gaske ne, don an taba cewa ta yi wani abinda bai so ba ya mare ta, ta zage shi, yana miqewa ta bazama cikin daki ta leqo ta taga tana cewa in ya san ya isa ya shigo ya tabe ta, ta hada da cewa " Ban yafe ba mugu kawai Allah zai saka min marin da ka yi min, kuma wallahi ba ka daki banza ba, a jikin yaranka zan rama ai za su dawo makaranta!".
.
Irin wadannan matan kamar zuma ce, shanta sai da wuta, in ya yi lagwas gidan sai ya gagare shi, wallahi akwai matan da suka shafe shekara 15 ba wace ta taba taka dakin wata, koda mutuwa aka yi bare haihuwa, hadin-kan yara kuma kai ka sani, kenan samun abinda za ka ba matan ba shi ne kadai ba, dole ka tabbatar kana da qarfin zuciyar da za ka iya tafiyar da gidanka, ka zaunar da su lafiya, in babu to ka kalli abinda tashin hankalin zai haifar.
.
Na zauna da wasu 'yan qasar Somalia in da suke mamakin yadda mutum yake qara aure kuma ya bar sabuwar matar a gari guda, har ya ce ya ji ana yin haka a Nigeria, na ce tabbas hakan na faruwa na ja bakina, ya ce wallahi a qasarsu sai wata ta kashe wata, abinda ya zo raina mu a Nigeria ai kusan a daki daya ma zan ce, don wasu matan sukan hadu a ne falo ne, wato "two bedroom flat" akwai masu madafa daya, ban-daki daya, komai tare suke yi in ba uwar-daka da kowa ke da nata daban ba.
.
Na taba jin wata Bamisriya a BBCarabic tana hira da Nuruddeen Zurgiy da jin muryarta za ta kai shekara 48-53, take cewa amaryarta ba ta san ta ba , ba su taba haduwa da juna ba, kuma ba ta fatar Allah ya hada su, da ya tambaye ta dalili sai ta ce "Gaskiya ni kyakkyawa ce! In muka hadu dole ta ji zafin hakan a zuciyarta!" Na yi dariya na ce to an gaya mata cewa kishiyar tata mummuna ce ko tsabar yarda da kai ce? Sannan ya maigidansu zai hada kan 'ya'yansa? Kuma ba a sha'ani a babban gidan ne da ba sa haduwa? Ko ba rashin lafiya ba a rasuwa ne? Akwai dai abubuwan tambaya da dama.
.
Na taba zama da 'yan qasar Ethiopia, ni ne ma wakilin angon, dan Nigeria ne, ya musluntar da ita ya aure ta, soyayya ba kama hannun yaro, kullum tana jikinsa, ba ta yarda ta yi nesa da shi, kai ko titi za a tsallaka ba za ta yarda ya tsallaka ya bar ta ba, sai dai su tafi tare, an kai yadda wurin aikinsa ma tare suke tafiya, malami ne, duk ajin da zai shiga sai dai su shiga tare, irin alaqar malami da dalibannan sam ba ta yarda ba kuma ba ta daga masa qafa ko kadan, na raba fada har na gaji, a qarshe na yi watsi da su, to kai a jinka ta ina zai sami sarari bare har ya yi tunanin zai qara mata? Ita kadai din ma ya aka qare bare ya auro wata? In dai zai qara auren to dole ya yi tunanin yadda za su rayu tare a qasa daya ma ba gari daya ko gida daya ba.
.
Rauni kan bayyana qarara a wurin wasu mazan, wanda kai da kanka ka san ba su shirya zama da mata biyu ba tsakani da Allah, wata matar take fadi da kanta cewa "Mu wallahi in shedan ya buga mana tambari dambacewa muke yi, ko maigidan yananan ba abinda yake iya yi, sai ma ya kulle mana qofa ya yi zamansa, haka za mu kekketa kayanmu, mu tottana wa kawunanmu asiri wallahi ko qala ba ya cewa bare mu sa rai zai shiga tsakanimmu, sai dai in mun gaji mu bari don kammu" abin takaici suna da yara kuma yaran suna ganin abinda yake faruwa, su ma babu cikakken hadin kai a tsakaninsu.

Post a Comment (0)