CINIKI DA KASUWANCI A SHARI'A 01

CINIKI DA ABINDA YAYI KAMA DA CINIKI/KASUWANCI AH SHARI'AN CE. 

       Fitowa Na (001)

Allah Mai Girma Da Daukaka Ya Halatta Yin Ciniki, Ko da Ga Mahaifiyar Ki Ne Ko Mahaifin Ki, Zaki Iya Ciniki Da Shi Ki Siyar Mai Da Wani Abinda Ya Gani Kuma Yake Bukatan Siye, amma Ya Haramta Kudin (RUWA). Kudin Ruwa a Zamanin Jahiliyya Ana Sa Su Ne akan Bashi, Wato ko Dai Mutum Ya Biya Bashin idan Lokacin Yayi, Tare da Kudin Ruwa da Aka sa Masa Ko kuma a kara Masa Lokaci Kuma a kara masa Wani Ruwan akan Na Farkon da Ya Karba, Ko ah Yanzu Ma Ana Yin Haka( Wannan ita ake Kira Riban Nasa'i, Wato Riba Ta Jinkirtawa). Misali Kene Kina Son a Baki Bashin Dubu Daya(1000) Sai Kika je Wajen Wata Yar Uwan Ki, Kika Ce Don Ta Taimake Ki da Bashin 1000, Sai Tace Zaki Samu, amma fah Idan Kin Tashi Biyanta Bashin Zaki Biyata 1500/1200/1100,Sannan Idan Kin Yi Jinkiri Baki Biya Ba Har Lokacin da Kukayi Ya Wuce, Nan Kuma Sai Tace Toh, Zaki Kara mata 1600/1700, akan wannan Shirin Ku Na Da Kenan, ko Kuma 1150/1250, toh Duk Wanna Riba Ne, Kuma Allah Ya Tsine ma Masu Yin Haka, Kuma Azabar Allah Ya Tabbata Gare Su Matukar Basu Tuba Sun Daina ba Har Allah Ya Dauki Rayuwar Su ah Haka, Maza Da Mata Duk Yanzu Kasuwancin Da ake Yi Kenan, toh Yar Kiyi Gaggawan Tuba Zuwa Ga Allah Kuma ki Daina Alaka a Cikin Kasuwancin ki da Riba
              Yana Daga Nau'in Riba, Wato Ruwa Ban da wadda ta gabata: Cin Riba Haramun Ne Babba, duk Mai Yin Shi Wallahi Yayi Gaggawan Tuba Zuwa Ga Allah Kuma Ya Daina Tun Yanada Sauran Numfashi, Karamin Zunubin Mai Cin Riba, Shine Kamar Misalin Namiji Ya Yi Jima'i Da Mahaifiyar Shi, Kenan Wannan Yakai Babban Laifi Mai Girma a Wajen Allah, Wajibi Ne Mata Da Maza Masu Yin Wannan abun suyi Gaggawan Tuba Zuwa Ga Allah Kuma ki Daina tun Kinada Sauran Numfashi ah Rayuwar Ki Na Duniya, 

Musayar Azurfa da Azurfa Hannu da Hannu a wajen Yin Wannan Musayar, amma wani yafi wani, Haka Nan Ma Musayar Dinare da Dinare, Musayar Dinare da Dinare ko Azurfa da Azurfa Wannan Bai Halatta Ba Sai Dai ayi Musayar Daidai da Daidai, Kuma Hannun Kuturu da Makaho a Wajen Yin Wannan Musayar( Wato Ba Tare Da Wani Jinkiri Ba ace Kibani Naki, amma Nawa kuma Sai anjima A'a Hannu da Hannu) 
            Nau'in Abinci, Na Kwayoyi, ko Masu 'bawo Da Makamantansu Na Duk Irin Abinda Za'a Iya adana Shi Da Abincin Yau da Kullum, ko Abinda Ya Shafi Dangin Kayan Miya, Toh Kowane Nau'in Guda Bai Halatta a Musanye Shi Da Irin Sa, Sai Dai ayi Daidai da Daidai ah Wajen Yin Wannan Musayar Kuma Hannun Kuturu da Makaho, Bai Halatta a Sami Wani Jinkiri a ciki ah Lokacin ba, 

Gyararren Abinci ba a Bisa Cewa Sai Zuwa Wani Lokaci Ko Da Nau'in Su Ba 'daya Ba Ne, ko Kuma Wanda Za'a ajiye ne ko Wanda ba Zai Ajiyu Ba, 
     Abubuwan Marmari da Masu Bunku a Kasa da Abin da Ba a ajiyarsa Duk Babu Laifi Ayi Musanyarsu Tare Da Fifiko, ko da Nau'in 'daya ne, amma ayi Musayar Hannun Kuturu da Makaho a Wajen Yin Wannan Musayar, amma kayan Marmari Busasshe Wanda Zai Ajiyu, da Kayan Miya da Abin Sha, Ban da Ruwa, Duk Wadannan Bai Halatta ba a Sami Fifiko a Cikin Musayar Su idan Nau'i Guda Ne________________

Ku Biyomu Ah Fitowa Na Gaba In Allah Yakaimu. 

Daga Zauren Muslim Woman Mata Zallah 
WhatsApp Group. 

MUHAMMAD TUKUR JALINGO 
Domin Shiga Wannan Group Zaki Iya Turo Mana Da Cikakken Sunan Ki Da Jihar Ku Kai Tsaye Ta WhatsApp Number Namu Kamar Haka 
08164223447. 
This Group Is Only For Woman Please.

Post a Comment (0)