BABA INA MAMA?


*🌹BABA INA MAMA?!🌹*

بسم الله الرحمن الرحيم.

_🌹Lokacin labari, 😊, gaskiya duk wnda be karanta ba to an bar shi a tafiyar se de ya kalle mu a can kawai ☺_

🌹Bayan ya binne matarsa a kabari, se ya dawo gida, ya sami ɗan karamin yaronsa yana kuka yana kiran mama! Mama! Yana ta zagaye yana neman mamansa a cikin gidan.

🌹Da karamin yaron ya ga babansa ya shigo yana tsaye a jikin kofa, se ya taho da gudu zuwa gurinsa yayi tsalle ya rike babansa yana tambayarsa - "Baba ina mamana?" - Sai ya kalli fuskar ɗan nasa tare da ajiye dogon numfashi yace "Tana Aljanna". Se yaron ya tambayi babansa cikin hawaye da shasshekar kuka - "Baba ina ce hanyar zuwa Aljanna?" Baba bashi da amsa, kawai se ya kalli sama cikin nutsuwa, yaro ya sake tambaya, "Baba ina ne hanyar zuwa Aljanna?" Ina so naga Mama, Ina so na ganta, ina so zan je hurin ta, ina ce hanyar Aljanna?

🌹Se baban yace - Ya kai ɗa na, hanyar zuwa Aljanna itace bin hanya madaidaiciya. Hanyar Annabawa da Manzanni, da Sahabbai da Tabi'ai. Hanyar Zuwa Aljanna shine tsayar Tawheedi, da zuwa masallaci da yin salloli biyar a rana cikin jam'i.

🌹Hanyar zuwa Aljanna shine yin Azumi, karatun AlQur'ani, aikin hajji idan ka sami iko, jihadi, da haquri da tsare mutuncin kai, da yin imani da Allah da aiyuka na kwarai. Hanyar Aljanna shine bin hanyar neman ilimi, da taimakon marayu, zama lafiya da mutane da yin biyayya ga iyaye.

🌹Se karamin yaron ya goge hawayensa, tare da murmushi a fuskarsa ya rungume babansa tare da sumbatarsa yace - Baba ina so na haɗu da mama sosai, ta tafi ta barni, nayi alkawari - zan zama mutumin kirkir, zan bi dukkan maganganunka don naje na samu mama acikin Aljanna kuma na ce mata - ɗan ta yayi kewarta sosai, ina ƙaunarki mama. Mama zata ji dadi soaai idan ta ganni a can mu rayu cikin farin ciki dani da kai da ita. 💘

🌹Ya Allah ka dora mu kan hanya madaidaiciya zuwa Aljanna madaukakiya, mu hadu da masoyan mu. Amin 💞

_*🌹Godiya ta musamman ga malamata kuma my sister حبيبتى 😘 cikin rayuwata, ina matuqar ƙaunarki sbd Allah "Muhazzabin" 💘*_

✍Rubutawa:- *Abdullah A Abdullah Abu Khadeejat (أنصار السنة)*
08/Shawwal/1440
12/06/2019.

+2348060027244

https://www.sirassalafeey.wordpress.com

*ZAUREN FADAKARWA A SUNNAH* 08108685876
Post a Comment (0)