LUGUDEN LUGWIGWITA AGWALUMA
A kwanaki kaÉ—an da suka gabata ne dai masu ruwa da tsaki na wani sabon shirin Masana'antar bulbula soyayya gami da sambaÉ—e-SambaÉ—e ta birnin in-da-yaya mai suna Talala-da-biye-biye suka saki hoton farko na wannan shi wanda yake É—auke da hoton shahararriyar masifaffiyar jarumar nan watau Kan-gwangwani. A hoton farkon dai da aka fitar an nuno jarumar ta canja siffarta gaba É—aya daga sanda zuwa AGWALUMA.
Sai dai a maimakon a yaba wa jarumar a matakin farko dangane da irin wannan ƙoƙari nata, sai ga shi mutane daga ko'ina suna ta yi mata luguden laƙumar agwaluma gami da latse-latsen lemo. Babu irin tofin ala-tsinen da bata sha ba. Sai dai wani rahoto da ke yawo ya bayyana cewa mafi yawancin masu suka da caccakar yanayin da jarumar za ta fito a cikin shirin wai masoya Jarumi hantaru ne. Jummai gantali dai da Hantaru kusan shekaru uku kenan suka ɗauka suna bata kashi da cece-kuce.
Mu dai anan sai dai mu ce Allaah shi sauƙaƙa.
<••••••••••••••••••••••••••••>
ɧãımãŋ Řâééʂ
<••••••••••••••••••••••••••••>
08185819176
Twitter: @HaimanRaees
Instagram: Haimanraees
Infohaiman999@gmail.com
Miyan Bhai Ki Daring