FASSARAR WAƘAR SAWARE

Fassarar WaΖ™ar Saware

Sunan WaΖ™a: Saware

Sunan Shiri: Phantom

Shekarar Fita: 2015 

Sauti: Pritam

Rubutawa: Amitabh Bhattacharya

Kamfani: T-Series

Rerawa: Arijit Singh

Fassarawa: Haiman Raees 🌹 

MATASHIYA: kalmar Saware ko Saanware a haΖ™iΖ™aninta tana nuni ne zuwa ga mutum mai Ι—an duhun fata. Kamar ace baΖ™i-baΖ™i kenan. Sannan ana amfani da wannan kalma wajen kiran sunan ubangiji Krishna wanda ya kasance Ι—aya daga cikin ababen bautar Hindu saboda ya kasance yana da duhun fata. Amma idan ka ji marubuta WaΖ™a ko na rerawa ko kuma na zube sun yi amfani da kalmar, to a mafi yawancin lokutta suna magana ne akan masoyi, abin Ζ™auna, masoyiya, ko kuma abar Ζ™auna. Wannan kuma ya samo asali ne duba da irin yadda suka amintu cewa Krishna abin so ne ga kowa. 

* Pehle Kyun Na Mile Hum, Tanha Hi Kyun Jale Hum
  
Me yasa ba mu haΙ—u da wuri ba? Me yasa zukatanmu ke gasuwa da kaΙ—aici? 

* Milke Muqammal Hue Hain, Ya They Tanha Bhale Hum

Shin mun haΙ—u ne domin zama cikakku ko kuma dai gara mu kasance cikin kaΙ—aici? 

* Saware... (x3)

Ya abar Ζ™auna 

* Na Humaara Hua Na Tumhara Hua

Da abinda na yi fata har abinda kika yi fata babu wanda ya faru 

* Ishq Ka Yeh Sitam Na Gawaara Hua

Soyayyar mu ta gaza kaiwa zuwa ga bigirenta 

* Na Humaara Hua Na Tumhara Hua

Da abinda na yi fata har abinda kika yi fata babu wanda ya faru 

* Ishq Ka Yeh Sitam Na Gawaara Hua

Soyayyar mu ta gaza kaiwa zuwa ga bigirenta 

* Sun Bairiya Saware… (x2)

Ki Saurara ya ke Muguwar Masoyiya 

* Pal Pal Ginke Guzara Maano Karza Utaara

Na kansace mai tafiyar da lokuta na ina mai Ζ™irga kamar ina rage bashin da ke kaina 
  
* Tum Se Munaasib Hua Hai Phir Se Jeena Humaara

A dalilin ki, na samu dalilin yin rayuwa 

* Saware... (x3)

Ya abar Ζ™auna

Hmm…

* Na Humaara Hua Na Tumhara Hua

Da abinda na yi fata har abinda kika yi fata babu wanda ya faru 

* Ishq Ka Yeh Sitam Na Gawaara Hua

Soyayyar mu ta gaza kaiwa zuwa ga bigirenta 

* Sun Bairiya Saware… (x2)

Ki Saurara ya ke Muguwar Masoyiya 

* Dhalti Raat Ka Ik Musaafir Subah Alvida Keh Chala

Matafiyin dare yayi bankwana da sanyin safiya 

* Jeete Jeete Raah Ho Saka Na Marke Haq Ada Kar Chala

A lokacin da yake raye, ya gaza zama hanyar da mutane za su bi, amma yayin mutuwarsa, aikin ya kammala 

O...

* Na Humaara Hua Na Tumhara Hua

Da abinda na yi fata har abinda kika yi fata babu wanda ya faru 

* Ishq Ka Yeh Sitam Na Gawaara Hua

Soyayyar mu ta gaza kaiwa zuwa ga bigirenta 

* Sun Bairiya Saware… (x2)

Ki Saurara ya ke Muguwar Masoyiya 


<••••••••••••••••••••••••••••>
      Ι§Γ£Δ±mΓ£Ε‹ Ε˜Γ’Γ©Γ©Κ‚  
<••••••••••••••••••••••••••••>
       08185819176
Twitter: @HaimanRaees 
Instagram: Haimanraees 
Infohaiman999@gmail.com

Miyan Bhai Ki Daring 

Post a Comment (0)