SHARUƊƊAN AMSAR AYYUKAN BAWA A WAJEN ALLAAH


SHARUDDAN AMSAR AIYUKAN BAWA AWAJAN ALLAH TA'ALA

Aiyukan bawa na fili da na boye basu samun karbuwa har Allah ya bashi sakamakonsu sai sun cika sharudda guda biyu-2:-

1-SHARADI NA FARKO:
"IKHLASY"
Shine tsarkake aikin zuwa ga Allah shi kadai,da kuma kyakkyawar niyya zuwa ga Allah alokacin gabatar da aikin. 

Allah yana cewa:
‏( وَمَا أُمِرُوا إِلَّا لِيَعْبُدُوا اللَّهَ مُخْلِصِينَ لَهُ الدِّينَ حُنَفَاءَ وَيُقِيمُوا الصَّلَاةَ وَيُؤْتُوا الزَّكَاةَ ۚ وَذَٰلِكَ دِينُ الْقَيِّمَةِ ) البيِّنة (5) Al-Bayyina

(Kuma ba a umarce su da kome ba fãce bauta wa Allah suna mãsu tsarkake addinin gare Shi, mãsu karkata zuwa ga addinin gaskiya, kuma su tsai da salla kuma su bãyar da zakka, kuma wannan shi ne addinin waɗanda suke a kan hanyar ƙwarai).
 
IKHLASY:
Shine manufar bawa acikin dukkan maganganusa da aiyukansa na fili da na boye yana yinsune da neman yardar Allah shikadai. 
Allah yana fada:
( ﻭﻣﺎ ﻷﺣﺪ ﻋﻨﺪﻩ ﻣﻦ ﻧﻌﻤﺔ ﺗﺠﺰﻯ ﺇﻻ ﺍﺑﺘﻐﺎﺀ ﻭﺟﻪ ﺭﺑﻪ ﺍﻷﻋﻠﻰ ‏) ﺳﻮﺭﺓ ﺍﻟﻠﻴﻞ 19/

(Alhãli bãbu wani mai wata ni'ima wurinsa wadda ake nẽman sakamakonta. Fãce dai nẽman yardar Ubangijinsa Mafi ɗaukaka).

ﻭﻗﺎﻝ ﺗﻌﺎﻟﻰ : ‏( ﺇﻧﻤﺎ ﻧﻄﻌﻤﻜﻢ ﻟﻮﺟﻪ ﺍﻟﻠﻪ ﻻ ﻧﺮﻳﺪ ﻣﻨﻜﻢ ﺟﺰﺍﺀً ﻭﻻ ﺷﻜﻮﺭﺍً ‏) ﺍﻹﻧﺴﺎﻥ 9/

(Suna cẽwa): "Munã ciyar da ku ne dõmin nẽman yardar Allah kawai, bã mu nufin sãmun wani sakamako daga gare ku, kuma bã mu nufin gõdiya".

ﻭﻗﺎﻝ ﺗﻌﺎﻟﻰ : ‏( ﻣﻦ ﻛﺎﻥ ﻳﺮﻳﺪ ﺣﺮﺙ ﺍﻵﺧﺮﺓ ﻧﺰﺩ ﻟﻪ ﻓﻲ ﺣﺮﺛﻪ ﻭﻣﻦ ﻛﺎﻥ ﻳﺮﻳﺪ ﺣﺮﺙ ﺍﻟﺪﻧﻴﺎ ﻧﺆﺗﻪ ﻣﻨﻬﺎ ﻭﻣﺎ ﻟﻪ ﻓﻲ ﺍﻵﺧﺮﺓ ﻣﻦ ﻧﺼﻴﺐ ‏) ﺳﻮﺭﺓ ﺍﻟﺸﻮﺭﻯ 20/
(Wanda ya kasance yanã nufin nõman Lãhira zã Mu ƙãra masa a cikin nõmansa, kuma wanda ya kasance yanã nufin nõman dũniya, zã Mu sam masa daga gare ta, alhãli kuwa bã shi da wani rabo a cikin Lãhira). 

ﻭﻗﺎﻝ ﺗﻌﺎﻟﻰ : ‏( ﻣَﻦْ ﻛَﺎﻥَ ﻳُﺮِﻳﺪُ ﺍﻟْﺤَﻴَﺎﺓَ ﺍﻟﺪُّﻧْﻴَﺎ ﻭَﺯِﻳﻨَﺘَﻬَﺎ ﻧُﻮَﻑِّ ﺇِﻟَﻴْﻬِﻢْ ﺃَﻋْﻤَﺎﻟَﻬُﻢْ ﻓِﻴﻬَﺎ ﻭَﻫُﻢْ ﻓِﻴﻬَﺎ ﻻ ﻳُﺒْﺨَﺴُﻮﻥَ ﺃُﻭْﻟَﺌِﻚَ ﺍﻟَّﺬِﻳﻦَ ﻟَﻴْﺲَ ﻟَﻬُﻢْ ﻓِﻲ ﺍﻵﺧِﺮَﺓِ ﺇِﻻ ﺍﻟﻨَّﺎﺭُ ﻭَﺣَﺒِﻂَ ﻣَﺎ ﺻَﻨَﻌُﻮﺍ ﻓِﻴﻬَﺎ ﻭَﺑَﺎﻃِﻞٌ ﻣَﺎ ﻛَﺎﻧُﻮﺍ ﻳَﻌْﻤَﻠُﻮﻥَ ‏) ﺳﻮﺭﺓ
ﻫﻮﺩ 16-15/
(Wanda ya kasance yã yi nufin rãyuwar dũniya da ƙawarta, Munã cika musu ayyukansu zuwa gare su a cikinta, kuma a cikinta bã zã a rage su ba. Waɗannan ne waɗanda bã su da kõme a cikin Lãhira fãce wuta, kuma abin da suka sanã'anta a cikinta (dũniya) yã ɓãci, kuma abin da suka kasance sunã aikatãwa ɓãtacce ne).

Annabi s.a.w yana cewa:
(Lallai dukkan aiyukan sai da niyya suke tabbbata,kuma lallai kowane mutum Ida abinda yayi niyya,......)
@ﺭﻭﺍﻩ ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ‏( ﺑﺪﺀ ﺍﻟﻮﺣﻲ 1/ ‏)

Kuma Annabi s.a.w yana cewa:
"Allah Wanda Albakarsa ta yawaita kuma shi madaukakin sarki ne yace:
(Ni Allah ni nafi wadatuwa da abinda masu shirka suke hada tarayya da ni acikin bauta,duk wanda ya aikata wani aiki,wanda ya hadani da wani acikinsa,zan bar wannan aikin da wanda yayi aiki). 
@ﻣﺴﻠﻢ 

2-SHARADI NA BIYU-2
"Aikin ya dace da abinda Allah ya shar'anta kuma yayi umarni wato, kada mutum ya baitawa allah sai abisa bin koyi da Annabi s.a.w.  

Dukkan abinda yazo daga allah da Manzonsa s.a.w da shine kadai ake bautawa Allah abisa koyi da sunnar Annabi s.a.w. Dukkan ibadar da bata cika wannan ba,bata samun karbuwa awajan Allah Ta'ala. 
Manzon Allah s.a.w yace:
 " ﻣﻦ ﻋﻤﻞ ﻋﻤﻼً ﻟﻴﺲ ﻋﻠﻴﻪ ﺃﻣﺮﻧﺎ ﻓﻬﻮ ﺭﺩ " ﺭﻭﺍﻩ ﻣﺴﻠﻢ

"Duk wanda ya aikata wani aiki, wanda babu umarninmu acikin wannan aikin to an mayar masa da aikinsa". 
‏( ﺍﻷﻗﻀﻴﺔ 3243/‏) ،

ﻗﺎﻝ ﺍﺑﻦ ﺭﺟﺐ ﺭﺣﻤﻪ ﺍﻟﻠﻪ:
Yana cewa:
"Wannan Hadisin wani tushene mafi girma daga cikin Tushen musulinci, kuma da shi ake banbance aiyukan bayi..". 

 " ﺇﻧﻤﺎ ﺍﻷﻋﻤﺎﻝ ﺑﺎﻟﻨﻴﺎﺕ:
Tana banbance aiyukan boye, tana tabbatar mana da dukkan aiyukan da akayi su badan Allah ba,ko badan Allah shi kadai ba,wannan aikin baya samun karbuwa da lada awajan Allah. Haka kuma dukkan aiyukan da babu koyi da Annabi s.a.w abin mayarwane baya samun karbuwa awajan Allah. 
@ﺟﺎﻣﻊ ﺍﻟﻌﻠﻮﻡ ﻭﺍﻟﺤﻜﻢ ﺝ 1 ﺹ 176 .

Kuma Annabi s.a.w yayi Umarni da bin shiriyarsa da koyi da sunnarsa acikin dukkan Ibada: sai yake cewa:
" ﻋﻠﻴﻜﻢ ﺑﺴﻨﺘﻲ ﻭﺳﻨﺔ ﺍﻟﺨﻠﻔﺎﺀ ﺍﻟﺮﺍﺷﺪﻳﻦ ﺍﻟﻤﻬﺪﻳﻦ ﻣﻦ ﺑﻌﺪﻱ ﻋﻀﻮﺍ ﻋﻠﻴﻬﺎ ﺑﺎﻟﻨﻮﺍﺟﺬ " ﻭﺣﺬَّﺭ ﻣﻦ ﺍﻟﺒﺪﻉ ﻓﻘﺎﻝ : "

Ina umarnin ku da roko da sunnata da kuma sunnar Khalifofina shiryayyu,ku rike sunnata da Hakoran gaba. 
Kuma yayi Hani da tsawatarwa akan aikata bidiya. 

Kuma ina maku gargadi akan aikata fararrun al'amura acikin Ibada,domin dukkan Bidi'a bata ce. 
ﻭﺇﻳﺎﻛﻢ ﻭﻣﺤﺪﺛﺎﺕ ﺍﻷﻣﻮﺭ ﻓﺈﻥ ﻛﻞَّ ﺑﺪﻋﺔ ﺿﻼﻟﺔ " ﺭﻭﺍﻩ ﺍﻟﺘﺮﻣﺬﻱ ‏( ﺍﻟﻌﻠﻢ 2600/‏) ﻭﺻﺤﺤﻪ ﺍﻷﻟﺒﺎﻧﻲ ﻓﻲ ﺻﺤﻴﺢ ﺳﻨﻦ ﺍﻟﺘﺮﻣﺬﻱ ﺑﺮﻗﻢ 2157

Ibn Qaiyim Allah yayi masa Rahama yana cewa:
"Allah ya sanya Ikhlasy da Koyi da Bin Annabi s.a.w sune Sharudda karbar aiyukan bayinsa,idan kuma bawa yayi wani aiki na ibada babu wadan nan sharuddan,wannan ibadar bata samun karbuwa awajan Allah". 
@ﺍﻟﺮﻭﺡ 1/135

Allah yana cewa:
 ‏
( الَّذِي خَلَقَ الْمَوْتَ وَالْحَيَاةَ لِيَبْلُوَكُمْ أَيُّكُمْ أَحْسَنُ عَمَلًا ۚ وَهُوَ الْعَزِيزُ الْغَفُورُ )
الملك (2) Al-Mulk

Shi ne Wanda Ya halitta mutuwa da rãyuwa domin Ya jarraba ku, Ya nũna wãye daga cikinku ya fi kyãwon aiki, Shi ne Mabuwãyi, Mai gafara.

ﻗﺎﻝ ﺍﻟﻔُﻀَﻴْﻞ : ﺃﺣﺴﻦ ﻋﻤﻼً ،
ﺃﺧﻠﺼﻪ ﻭﺃﺻﻮﺑﻪ . 
Aiki mafi kyau shine wanda ya cika sharadi guda biyu:
1-Anyi shi dan Allah kadai da ikhlasy. 

2-Anyi shi daidai wato bisa ga koyi da sunnar Annabi s.a.w.  

Allah bamu ikon cikasa wadan nan sharuddan acikin aiyukan mu baki daya.
Post a Comment (0)