SHAYE-SHAYE A TSAKANIN MATAN HAUSAWA

SHAYE SHAYE A TSAKANIN MATAN HAUSAWA. 

Yawaitar ta'ammali da kayayyakin gusar da hankali da mata ke yi a yanzu, na daya daga cikin manyan matsalolin da al'ummar Hausawa ke fuskanta.
Yara mata da shekarunsu suka kama daga 18-45 ne suka fi aikata wannan mummunar dabi'a. Akwai dalilai masu yawa da ake ganin sune musabbabin haddasawa matan Hausawa tsunduma cikin wannan mummunar hanya ta shaye-shaye. Daga cikin wadannan dalilai akwai:
Rashin aure
Tsantsar damuwa
Auren dole
Damuwar da auren ke haifarwa. 

Wannan dabi'a ta shaye-shaye a tsakanin matan Hausawa, a iya cewa bak'uwar aba ce, wadda a 'yan shekarun da suka gabata sam ba a santa ba, akwai tabbacin cewa kwanan nan ta kutso kai cikin al'ummar ta Hausawa, sakamakon su ne suka fi kowa matsalolin aure a tsakankanin takwarorinsu wato k'abilun Yoruba, Igbo, Kanuri da kuma Fulani.
Duk da kasancewar matsalar shaye-shayen mata ta zamo ruwan dare game duniya, sakamakon babu wata al'umma a yanzu da za ta bigi k'irji ta ce ta tsira daga wannan mummunar dabi'a, sai dai ace wata ta fi wata.

WANE DALILAI NE SUKA FI SA MATAN HAUSAWA SHAYE-SHAYE? 
Shaye-shaye na nufin shan dukkan wani abu da zai iya jawo buguwa, ko daukewar barci, ko karin wani karfi na musamman ko gusar da hankali. Jaridar Vanguard News ce ta rawaito hakan a wani gangamin wayar da kan matasa da hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta k'asa (NDLEA) ta gabatar a jami'ar Bwari a watan March na wannan shekarar. 

Wani bincike da Medlineplus ta k'asar Amurka ta gabatar, ya nuna cewa binciken National institute on drug abuse ta k'asar Amurka ya baiyana cewa, shaye-shayen magunguna ba bisa ka'ida ba, babban tarnak'i ne ga lafiyar kowacce al'umma. Miliyoyin mutane suna rasa rayukansu, ko su kamu da cututtuka masu yawan gaske.

Dalilai da yawa ne dai ake ganin su ne suka sanya mata tsunduma cikin harkokin shaye-shaye. Daga cikin manyan dalilan akwai:

RASHIN YIN AURE A KAN LOKACI
Sanannen abu ne yadda Hausawa suka dauki aure, hasali ma aure shi ne abu mafi muhimmanci a bahaushiyar al'ada.
Rashin samun mijin aure a lokacin da mace ta kai minzalin yin auren na zama babban sanadin haifar da shaye-shaye ga mata. Wannan matsala ce babba da ke tunzura rayuwar 'yan mata su fara ta'ammuli da kayan gusar da hankali. Damuwar da al'uma kama daga iyaye, 'yan uwa, kawaye da sauran jama'a da suke d'orawa macen da bata yi aure ba na saka matan su fara amfani da kayan gusar da hankali. Haka kuma mata da yawa da ba su da aure kuma ba sa so su fada cikin harkokin zinace-zinace, su kan yi amfani da magungunan gusar da hankali domin ya taimaka mu su wajen rage sha'awar maza da za su iya ji. Shan kayan maye na ba su damar mancewa da kuma tsai da duk wani yanayi da za su iya ji a jikinsu.

DAMUWA
Tsantsar damuwa sakamakon rashin wani abu na jefa mata cikin shaye-shaye. A wannan rukuni an fi samun matan aure a ciki, wadanda yawanci ba sa samun kulawar da ya kamata daga wajen mazajensu, wato ba su da lokacin yin hira da su ko jin wasu matsalolinsu. Hakan ya kan tunzura matan su fara shan kayayyakin da za su gusar musu da hankali, domin su samu damar mance kaso da yawa na matsalolin da suka addabi rayuwarsu.

GASA/KWAIKWAYO

Jinsin mata a dabi'ance jinsi ne ma su gasa da kwaikwayo, wato hanya ce mai sauki na samun yawaitar mata ma su shaye-shaye, sakamakon wata ta ga wata kawarta ko makociyarta ta na yi. A nan akwai buqatar bayar da kulawa ta musamman ga mata da sa ido koyaushe akan hanyoyin da mata ke bi don gudanar da rayuwarsu.

NAU'O'IN KAYAN MAYE DA MATA SUKA FI AMFANI DA SU
Mata ba su cika amfani da kwayoyi ba, sai dai magunguna na ruwa wato syrup. Wadannan magunguna sun hada da: Emzolyn
Benelyn
Coplin
Codin, da kuma wasu kad'an da su kan yi amfani da tabar wiwi da k'wayoyi kamar su Tramol da sauransu.

ILLOLIN DA SHAYE-SHAYE YAKE YIWA JIKIN MACE
Daga cikin manyan matsalolin da shaye-shaye ke haifarwa ga mata sun had'a da:

HANA HAIHUWA
Mata ma su shaye-shaye na fuskantar barazanar rashin haihuwa, domin kuwa ya na raunata mahaifarsu yarda ko da ma ciki ya shiga ba ya iya zama. 

HAIHUWAR YARA MARA SA LAFIYA
Akwai barazanar haihuwar yara marasa koshin lafiya, idan ma har an samu haihuwar kenan, ana haifar yara da wani nak'asu a jikinsu ko kwakwalwarsu.

RAUNANA GARKUWAR JIKI
Shaye-shaye na matukar raunana garkuwar jikin mace, da hana su kuzari ta hanyar haddasa musu cututtuka iri-iri.

RAGE DARAJA A CIKIN AL'UMA
Shaye-shaye na rage darajar mace a cikin al'uma, ya na sawa a gujeta a kyamaceta. Idan budurwa ce yana hanawa a aureta, idan kuma mai aure ce yana jawo rabuwar aure. 

RASHIN SON KUSANTAR NAMIJI
Matan da suke shaye-shaye ya na rage mu su sha'awa, ya na sa su ji ba sa so maza su taba su ko su kusancesu da gaske. Ya na hana garkuwar jikinsu karbar duk wani sako da namiji zai aika gareta. 

SAUYAWAR GABOBIN JIKI
Ana gane mata ma su shaye-shaye ta hanyar kankancewar idanuwansu da canzawar launin idon, labbansu na bushewa kuma hakoransu na lalacewa har ma su rube wani lokacin. Ya na sa rama da bushewar jiki, yana saukar da gashin mace, ya lalata kyakkyawar surarta. 

YAWAN RASHIN LAFIYA
Matan da suke shan kayan maye su na da yawan laulayi, ko yaushe cikin ciwo suke, sabo da sun riga sun raunata garkuwar jikinsu. K'ashinsu kuma yana rage k'wari, dan haka akwai yiwuwar saukin samun karaya a k'ashinsu. 

A karshe zuwa ga duk wanda abin ya shafa, akwai bukatar d'aukar kowane irin mataki da ake ganin ya dace, domin yak'ar wannan mummunar d'abi'a da ta kutso kai cikin al'umarmu.

Aysha Bilkisu Umar 
8/6/18.

Post a Comment (0)