TARIHIN BIRNIN AUYO


Tarihin Tsohon birni 'auyo'.
Daga
Gaddafi Hussain Auyo
08149217486 da
Sadiq Tukur Gwarzo.
Garin Auyo tsohon gari ne, domin kuwa tarihi ya bayyana mana cewa Auyo na É—aya daga cikin tsoffin birane kuma mashahurai a wannan kasa waÉ—anda sukayi sharafi har kuma ya zamo suna cin gashin kansu tun tsawon zamani daya gabata.
Haka Kuma birnin Auyo ya jima yana É—auke da tsarin masarauta wadda sarakuna ke tafiyarwa cikin ka'idoji gami da lura.
Dangane da daÉ—ewar Auyo, tarihi ya bayyana mana cewa ko lokacin da fir'auna Remesis II na zamanin Annabi Musa (A.S) yayi yekuwa tare da gangami daga manyan birane yana mai neman waÉ—anda suka kware akan sihiri da surkulle, a wannan karawar da tarihi ya ruwaito Firaunan yayi da Annabi Musa A.S, an samu cewa tabbas akwai matune a Auyo, har kuma wasu shahararru akan sihiri daga kasar Auyo sun halarci wancan taron tare kuma da jarraba tsibbace-tsibbacen su a wurin, amma daga bisani da Annabin Allah Musa yayi galaba akan É—aukacin Masihirtan, ance suna cikin waÉ—anda suka gaskata Annabi Musa (A.S) kuma sukayi masa mubayi'a.
Har ila yau, akwai zance na gaskiya mai nuna cewar lokacin da tawagar wakilai daga kasar Borno a zamanin wani Sarkinsu da ake kira 'Maidinama' suka tafi birnin Madina domin su karɓo addinin musulunci a wajen Shugaba, Manzon Allah (s.a.w) har kuma suka tarar Manzon Allah yayi wafati sai Sayyadina Abubakar R.A ne ke Halifanci, har da mutanen Auyo acikin tawagar.
A wancan lokacin ance shima Sayyidina Abubakar ɗin yana fama da yakuna, don haka yace su zauna kafin a samu natsuwa, har kuma Allah ya karɓi rayuwar sa. Amma da fara Halifancin Sayyidina Umar R.A sai ya taso da maganar, ya haɗo rundunar sahabbai da littattafai suka taho Borno..
Kasar Auyo ta kasance mai daÉ—aÉ—É—en tarihi, domin kuwa anyi imanin cewa duk wasu garuruwa da ake alakantawa da hausa bakwai ko banza bakwai, to kuwa Auyo ta girme su.. A ciki harda Daura, domin dai abisa kiyasi na bincike an gano cewa Auyo tafi shekara dubu biyar da kafuwa.
Ance wani mutum mai suna 'Auya' shine ya kafa garin na Auyo, don haka daga sunan sane aka samo kalmar 'Auyo', kuma shi É—an kabilar 'Bagirmine' waÉ—anda akace tun da jimawa suna zaune a arewaccin kasar Sudan.
Kasar Auyo tana da mashahuran malamai masanan addinin musulunci. Tarihi ya bayyana mana cewa daga cikin malaman da sukayi fice a kasar kano akwai da yawansu waÉ—anda asalinsu Auyakawane.
Garin Auyo yana É—aya daga cikin garuruwan da anan baya-baya aka haÉ—e aka samar da masarautar Hadejia. Amma wannan gari sam ba koma baya bane acikin tarihin kasar Hadejia, kasancewarsa tsohon gari wanda ya daÉ—e da wanzuwa zamuna masu tsawo da suka shuÉ—e, gashi kuma sanan-nan gari daya tattara mutane masu baiwa iri daban-daban kama daga dakaru da baraden yaki zuwa uwa uba malamai mahardata alqur'ani mai girma.
Auyo ta jima É—auke da masana masu ilimin taurari dana bugun kasa da masu lakkuna da sauran iliman asararu na tsaron kai da tsaron kasa, haka ma suna da mutane wadanda suka shahara wajen sihiri da surkulle irin na wancan lokacin. Don haka muna iya cewa ita tunjimin gari ne wanda kome mutum yaje nema yana iya samu..

1 Comments

  1. Masha Allah!
    Amma ba wata shaida ko alama ta ɓurɓushin tarihi kamar tuta ko Masarauta ko wata alama da tarihi ya bari ?

    ReplyDelete
Post a Comment