A TUBA ZUWA GA ALLAH


A TUBA ZUWA GA ALLAH !!!

Allah madaukaki yana cewa : "Babu wata musiba da za ta same ku, face sai ta kasance daga abin da hannunku ya aikata ne" suratush Shurah aya ta 30.

Zunubai suna jawo bala'oi da yawa, wadanda suke cutar da zuciya da jiki, a Duniya da Lahira, ba wanda ya san adadinsu sai Allah, ya kamata mu koma ga Allah mu tuba zuwa gare shi, mu kusance shi da aiyuka nagari, mu dinga umarni da kyakkyawan aiki, muna hani da mummuna, saboda idan bala'i ya zo ba zai takaita kawai akan wadanda suka aikata alfasha ba, domin ba za'a dora maka wani ya dinga cutar da kai ba, sai idan akwai wani zunubi da ka aikata, ka san zunubin ko ba ka san shi ba, wani daga cikin magabata ya hadu da wani mutum sai ya aibanta shi, sai ya ce masa : jira ni na shiga gida na fito, sai ya shiga gida yayi sallah ya tuba zuwa ga Allah, bayan ya fito sai mutumin ya ce masa: me ka yi, sai yace : na tuba zuwa ga Allan da ya dora ka akaina.

Rubutawa✍🏻

DR. JAMILU YUSUF ZAREWA
20/1/2012
Post a Comment (0)