HAƘURI A ZAMAN AURE

HAKURI A ZAMAN AURE (‘YAN UWA MATA)

HAKURI yana da matukar riba a rayuwa (bama a zamantakewar aure kadai ba) abun da yake damun wasu ma’auratan shine gaggawa da rashin hakuri, zaka ga mutum yana fadin cewa yana cikin matsala amma kuma abun mamaki shine bazai iya hakuri akan matsalar ba. Musamman a banganen mata ki sani cewa wani abun fah dole take kamawa idan kika kasa hakuri na kankanin lokaci wallahi hakan sai ya jawo miki shiga matsalar da sai kin dauki tsawon lokaci bki fita a ciki ba.

‘YAR UWA kiyi tunani ki gani lokacin da za’a kawo ki gidan ki kowa idan ya gama miki huduba a bun da yake cike hudubar dashi shine a rinqa hakuri, kada kiyi zaton dan su basu samu soyayyar mijinsu bane (su wadanda suke miki nasihar) a’ah wallahi wata a cikinsu soyayyar da mijinta ke gwada mata ke koh rabinta bazaki samu ba, amma da zaki tambaye ta meye jagoran wannan zaman nasu sai tace miki hakuri, haka shima ta bangaren mijin. http://sirinrikemiji.blogspot.com/2018/07/hakuri-zaman-aure-yan-uwa-mata.html#.XloRWVxAIAs.whatsapp

https://sirinrikemiji.blogspot.com/

Post a Comment (0)