SIGN OUT


*▪SIGN OUT 👩🏽‍🎓👨🏽‍🎓*
.

Haqiqa mafi wayau daga cikin masu tafiya shi ne wanda yake waiwayen bayansa, mafi hikimar abin guzuri shi ne yin guzurin haďuwa da Mahaliccina da kai/ke.

Tabbas Allah Ya bambanta halittar ďan adam daga sauran dabbobi ta hanyar sanya masa hankali da tunani, ta hakan ne zai iya gane iyakokin dokokin Allah don kada ya qetare, ya san ayyukan alkhairai don ya ankare, sannan aka ba shi istigfari wanda idan ya yi zunubansa ne za a kankare. Amma na kan rasa inda a ka jefar da tunani idan na yi dubi zuwa ga rayuwar matashi ko mashiyar da ta kwashi shekaru tana neman ilimi, cikin iko da yarda ta Ubangiji sai Ya ba ta damar kammala karatunta (it might be ND, diploma, NCE or DEGREE etc), maimakon a yi wa Allah godiya, sai aka biye wa kiraye-kirayen shaiďanu ta hanyar kokarin koyi da kafirai maqiyanmu. 
.

Wannan salo da aka fito da shi wanda ake yi wa laqabi da *Sign out,* wallahi idan muka dube shi da idon fahimta sam sam be dace da tsarin rayuwa ta musulmi ba, domin qazantar dake cikinsa ta yi yawa, kuma har yau babu wata fa'ida da masu yin wannan abu za su samu wadda za ta amfanar da duniyarsu da lahirarsu. *Sign out* yanayi ne da ya qunshi cuďanya tsakanin maza da mata, ga wani salo na almubazzaranci da yake cikinsa, ga koyi da kafirai, da sauran abubuwa waďanda addinin musulunci ya kyamata, abin tir! Wai sai ka ga wata sakaryar budurwa ta ba da jikinta ga wani gardi wai ya yi sign, ku ji ballagaza fa, wai kuma hakan ana yi ne da sunan wayewa, ayyah, wallahi kin yi kuskure 'yar uwa, me ya mantar da ke daga yin sadaka don nema wa rayuwarki albarka? Wallahi ki tara almajirai ki yi masu sadaka shi ne alkhairi a kan ki tsaya wasu sakarkaru suna 6ata maki riga da rubutun da ba zai amfanar da ke ba. 
.

Musulunci addini ne wayayye, there are so many legal means in which you can express your happiness and also show your gratitude to the almighty God Whom is out of His mercy you got the chance to be a graduate, ba laifi bane ki tara walima a ci a sha, za ki iya min azumi, sadaka, sallah ko wani aikin alkhairi don godewa Allah, a kullum so ake a ga canji daga zuci har wajenki, ka/ki bambanta daga waďanda ba musulmai ba.
.

Musulunci ya kyamaci koyi da kafirai 'yan uwa, mu tuna fa za mu mutu mu je mu haďu da Mahaliccinmu, kada neman suna ko yabo ya sa mu jefa kanmu zuwa ga halaka. 
.

Kada ka yi asarar albarkar karatun da ka yi shekaru kana nema a cikin sa'o'i kaďan, domin tabbas dayawa daga cikin graduates a wajen murnar kammala karatunsu suke kore albarkar karatun, sai ka ga ga dai certificate amma be amfanar da komai ba, ko kuma Allah Ya jarrabe su ta wani fannin. 
.

'Yan uwa mu ji tsoron Allah, wannan sign out ba namu bane mu musulmi, nasu ne don haka mu bar masu abinsu. 
.


Allah Madaukakin Sarki Ya qara tsarkake mana zukatanmu. 
.

*✍🏾Ayyub Musa Giwa.*
*(Abul Husnain).*
.

*🕌Islamic Post WhatsApp.*
*08166650256.*
Post a Comment (0)