BURABUSKO


*BURABUSKO*


KAYAN DA ZA KI TANADA

1. Gero 
2. Mai 
3. Gishiri

YADDA ZA KI HADA
Ki sami gero ki wanke shi ki rage domin tsakuwar ta fita, sai ki shanya ya bushe. Idan ya bushe sai ki kai a barzo miki a inji. Ki dora ruwa a kan wuta kamar rabin tukunya, sai ki kawo madambaci ki dora akan tukunyar, ki shimfida buhun algarara ko kuma jarida akan madambacin. Sai ki kawo barzazzan geronki da kika bakace kika fitar da dusar ki zuba a cikin madambacin, ki yayyafa ruwa akai. Idan kina so ma kina iya jika kanwa ‘yar kadan ki yayyafa ruwa akan geron saboda ya yi laushi sosai. Sai ki bar shi ya turaru. Idan ya dauko turaruwa zaki ga ya fara curewa, sai ki sauke daga kan wuta ki zuba mai da gishiri ko magi ki mitststsika domin ya warware. Sai ki rage ruwan daya ke cikin tukunyar ki bar shi dai-dai yadda zai yi miki. Sai ki dauko turarren geronki ki zuba a cikin ruwan, sai ki dan juya kamar kina rude, amma wannan da kauri. Sai ki kawo leda ki rufe, sannan ki kawo murfin tukunyarki ki dora akai. Idan ya yi zaki ji gidanki ya turare da kamshi, kuma idan kin taba zaki ji yayi laushi.

Umman amir and minaal👩🏻‍🍳👩🏻‍🍳👩🏻‍🍳
Post a Comment (0)