Tambaya :
Slm
Dan Allah mlm mene Hukunci wadda take karin gashi
Amsa :
Alhamdulillah wassalatu wassalamu ala Rasulillah wa'ala ahlihi wasahbihi waman walah.
Bayan haka :
Haramun ne yin ƙarin gashi , sabida faɗin Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam : ( Allah ya tsinewa Mai ƙara gashi da wadda ta nemi a ƙaramata , da mai yin wushirya da wadda ta nemi ayimata.)
Bukhari ya rawaito
Daga Jabir Radiyallahu anhu yace : ( Manzon Allah ya tsawatar akan waɗanda suke ƙara wani abu a jikin gashinsu )
Muslim ya rawaito.
Kuma koda gashinta ne Wanda ta taje idan ta ƙara ta shiga ƙarƙashin wannnan hukuncin.
Malamai Hanafiyya da Malikiyya da Shafi'iyya sunyi bayani ƙarara akan haka.
" Yin ƙarin gashi da gashin ɗan Adam haramun ne , koda kuwa mutum gashinsa ya ƙara dashi ko gashin wani"
الفتاوى الهندية 5/358
حاشية ابن عابدين 6/372
Malam Adawiy yace : " faɗin Manzon Allah ( Allah ya tsinewa mai ƙarin gashi) yana nufin wadda take ƙara wani akan gashinta , nata ko na wani ..."
حاشية على شرح كفاية الطالب الرباني 2/459
Malam Sharwaniy yace : " koda kuwa gashinta ne da ta cire daga jikinta , ko na wani. An naƙalto daga masu sharhi yin hakan ya haramta , ..."
حاشية تحفة المحتاج 2/128
Al -Majd Ibn Taimiyya yace : " bai halatta mace ta gashinta ba , koda gashin ɗan Adam ne ko wani.."
تصحيح الفروع 1/159
Wannan haramcine tabbatacce ga kowane nau'i na mata yara da manya , buduri da masu aure .
Mata masu aure baza suyiwa mazajensu biyayya koda sun umarcesu su ƙara gashin.
Daga Nana A'isha Radiyallahu anha tace : wata mata daga cikin mutanen Madina ta aurar da ƴar'ta , sai tayi rashin lafiya , sababin rashin lafiyar gashinta ya zube , sai mahaifiyar yarinyar taje gurin Manzon Allah , tace : mijin ƴa'ta yana son gashi , zan iya ƙara mata? Sai Manzon Allah yace : Allah ya tsinewa mai ƙarin gashi.
Bukhari da Muslim ne suka rawaito wannan lafazin Muslim ne.
A lafazin Bukhari cewa yayi : matar tace : mijinta ya umarceni na ƙaramata gashi. sai Manzon Allah yace : a'a , kada ki ƙara , haƙiƙa an tsinewa masu ƙarin gashi.
Imamun Nawawiy yace : wannan hadisin yazo da bayyani a fili cikin haramcin ƙarin gashi...
A wani gurin yace : wannan hukuncine da babu banbanci cikinsa tsakanin mace mai uzuri da Amarya ko waninta.
Abinda ya dace shine asami masa harkokin gashi su bada magani insha Allah za'a dace , domin Allah bai saukar da wata cuta ba saida ya saukar da maganinta , wanda ya sani ya sani , wanda bai sani ba bai sani ba.
Wallahu Aalamu