JIKIN ƊAN ADAM 01

*بسم الله الرحمن الرحيم*
*_وصلى الله على سيدنا ونبينا محمد وعلى آله وصحبه ومن سلك طريقهم إلى يوم الدين. صلوات الله عليه فى كل الأوقات عدد رماد الأرض أعدد المخلو قات_*

*🍉🍅JIKIN DAN ADAM // 01🍍🍊*

*Rubutawa: Baban Manar Alqasim*


Masu ilimi masamman ilimin da ya shafi tsarin halittar dan adam, bayan dogayen bayanan da suka bayar a kan sassan jikinsa, sun yi wani tsokaci dangane da yadda mutum zai ririta rayuwar tasa, ta wajen bin abin da Allah SW ya tsara masa, da irin nau'o'in abincin da suka dace da shi, gami da wadan da zai kau da kansa, har ma da lokutan da suka dace a ci din, sai dai shi dan adam din ne a wautarsa ko rashin ilimi bai iya tantance abubuwan da zai ci din ba.

Wasu lokuta za ka ga Qur'ani ne ma ya fito qarara ya haramta wasu nau'o'i na abinci, amma rashin samun shiriyar muslunci sai ka ga mutum ya ci abinsa, tamkar dai alade, kare, jaki da mushe, ko kuwa ka ga ya bar zuma mai zaqin gaske da qara lafiya, ya koma yana shan giya, wace take fatattaka rayuwa, ta nade mutumcin mutum -in har yana da shi din- ta watsar.

Wani sa'in kuwa, mutum musulmi ne ma, amma bai bar dibar barasa ba, tare da saninsa cewa haramun din ne, wannan zai iya karkatar da tunaninsa, ya raunata zumuntarsa, ya zubar masa da qimarsa, ya nisantar masa da abokan qwarai wadan da za su iya ba shi shawarar da za ta taimake shi, galibin irin wadannan barasa sun kasu kashi uku ne, wasu sukan qara wa mutum kuzarin da ba ya buqata ne, wasu kuwa kishiyantar wadancan suke yi wajen sanya mutum kasala, da barci mai nauyi.

Kashin qarshe kuwa ba abin da suke yi sai sanya mutum ya yi marisa, wato ya fita hayacinsa gaba daya, wata qila ma ya fara sumbatu alhali shi ba mahaukaci ba duk da cewa ya shiga hanya dodar wace za ta miqa shi zuwa ga haukar, wasu kayan barasan qwayoyi ne ake hadewa, wasu ganyayyaki ne, in mutum ya ci ko kashi sai ya yi maka a zaune, ba ya iya ko motsawa, sai ya yini a wurin ba tare da ya iya tashi ba, shi kuwa ba barci yake ba.

Akwai ma barasar ruwa tsinkakkiya tamkar ruwan kwakwa wato bammi da saran ruwan kwalba, wasu ma kauri ne da su kamar kunu, wadan da aka yi da hatsi wato burkutu, ko wadan da ake shaqa misalin koken, maganin sauro, ashana da sauransu, da ma wadan da iskarsu kawai ake ja, su wadannan Allah ya yi yawa da su, ka taras fetur ne, ko kwatami, masai, sukudaye, shalisho, da ma na hayaqi irin wiwi, garin zogale da makamantansu, sai magungunan mura, ga su birjik sai wanda mutum ya so ya halaka kansa da shi.

Allah SW dai ya gina jikin dan adam bisa mafificin tsari, sai dai ko shi din ya wulaqanta kansa gwargwadon yadda yake so ya gani, a tunaninsa wayewa ce ko hanya mafi sauqi wajen kawar da damuwa, ko kuwa yin abota da mutanen banza, ba wanda ba a yi, kuma ba wanda yake da sakamako mai kyau, a qarshe dai rayuwar takan zama mummuna, har ta kai ga cewa mai rayuwa a cikinta ma wanda shi ya shigar da kansa ba ta ba shi sha'awa bare mai kallonsa, wanda ga aibun a sarari yana kallo.

Kar ka yi tsammanin cewa baki shi ne kadai hanya mafi girma wajen shigo da albarkatun da Allah SW ya yi don gina jiki da qarfafa qwayoyin da suke zama garkuwa ga jikin dan adam, ko saduwannan da kake gani ta aure, masana ko na ce masu bincike sun gano cewa tana ba da gagarumar gudummuwa wajen gyaran fata, masamman a wajen mace, tana kau da damuwa, ta qarfafa qwayoyin cikin jini, ta sanya nishadi da kuzari mai dorewa, amma abin mamaki sai ka ga ana qyamar wannan hanya madaidaiciya a koma zina ko mutu'a wato holewa.

Bincikemmu gaba daya zai kai ya komo ne bisa dan adam, ko nace abubuwan da dan adam din yake buqata don qarfafa jikinsa, abin da zai ci, yadda zai ci din, da kuma lokacin da zai ci, gami da sanin kimanin da ake buqata ya cin, da kuma abubuwan da zai guda don gyaran kansa, koda kuwa addininsa bai haramta masa ba, to amma kafin mu kai ga wadannan abubuwan da za mu ci, shin barin ciki ba komai wato yin azumi yana da amfani ga jikin dan adam?

*Gabatarwa Abulfawzhaan*

*Gamasu Sha'awar Bibiyar Karatukanmu Akan Shafukan Sada Zumunta Kamar WhatsApp da Facebook Zasu iya Bibiyarmu ta Wannan Hanyar*

*_Sai kuturo da Cikakkiyar Sallama. Da Cikakken Suna Tare da Adreshi ta Wadan nan Numbobin_*

_*WhatsApp Number*_
 +2348039103800.
 +2347065569254

_*Facebook @Zauren Sunnah*_
https://www.facebook.com/groups/552998655501583/

*اللهم لا تواخذنى بما نقولوا واجعلنى خيرا مما نظنون. فقلت ما قلت. إن تك حسنة فمن الله وإن تك سيئة فمن نفسك والشيطان. وسبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن لا اله إلا أنت. وأستغفر الله لى ولكم ولسائر جميع المسلمين من كل ذنب و استغفر وه إنه هو البرو الرحيم*

_*والسلام عليكم ورحمة الله وبركاته*_

_*🖊Abulfawzhaan Ibn Zubair Ahmad*_

Post a Comment (0)