JIKIN ƊAN ADAM 02


*بسم الله الرحمن الرحيم*
*_وصلى الله على سيدنا ونبينا محمد وعلى آله وصحبه ومن سلك طريقهم إلى يوم الدين. صلوات الله عليه فى كل الأوقات عدد رماد الأرض أعدد المخلو قات_*

*🍉🍅JIKIN DAN ADAM // 02🍍🍊*

*(Fitowa ta Biyu)*

*Rubutawa: Baban Manar Alqasim*

Babu ko shakka jikin dan adam ta kowanne hali yana buqatar abu hudu:

Abinci, barci, motsa jiki da wofinta ciki na wasu lokuta, in mutum ya bar tumbinsa ba abinci har na wani lokaci zai iya kamuwa da wasu cututtuka, haka in ya qi ba cikin hutu ko sau daya, tanan ma wata cutar tana iya shiga jikinsa, shi ya sa Allah (SWT) Ya farlanta azumi a kan kowa sai wanda ya qi, ko kuwa wanda wani uzuri na dole ya auka masa.

Allah (SWT) Yana cewa:-

‏ﻳَﺎ ﺃَﻳُّﻬَﺎ ﺍﻟَّﺬِﻳﻦَ ﺁﻣَﻨُﻮﺍ ﻛُﺘِﺐَ ﻋَﻠَﻴْﻜُﻢُ ﺍﻟﺼِّﻴَﺎﻡُ ﻛَﻤَﺎ ﻛُﺘِﺐَ ﻋَﻠَﻰ ﺍﻟَّﺬِﻳﻦَ ﻣِﻦْ ﻗَﺒْﻠِﻜُﻢْ ﻟَﻌَﻠَّﻜُﻢْ ﺗَﺘَّﻘُﻮﻥَ

Ku da kuka yi imani An wajabta muku yin azumin kwanaki kamar yadda Aka wajabta wa wadan da ke gabaninku don lallai ku ji tsoron (Allah).

Kenan ba mu ne kadai Aka aza wa yin azumi ba, hatta wadan da suke gabanimmu ma Allah (SWT) Ya wajabta musu yin azumin don dai su bauta maSa da shi, a daya hannun kuma su sami lafiyar da za su tsayu da ita don fuskantar sauran ibadun.

Sai Ya ce:-
" ﻭَﺃَﻥْ ﺗَﺼُﻮﻣُﻮﺍ ﺧَﻴْﺮٌ ﻟَﻜُﻢْ ﺇِﻥْ ﻛُﻨْﺘُﻢْ ﺗَﻌْﻠَﻤُﻮﻥَ "

In da kun sani, yin azumin shī ne ya fi muku.

Domin azumin zai ba mutum kariya ta fuskoki daban-daban, haka Annabi SAW ya ce:-
ﺍﻟﺼِّﻴَﺎﻡُ ﺟُﻨَّﺔٌ

Azumin garkuwa ne... Bukhari

I tabbas kuwa, don zai kare mutum daga munanan maganganu, da munanan cututtuka, gami da muggan shedanu na mutum da aljani.

Idan mutum ya quduri yin azumi yana da kyau ya san cewa akwai manyan abubuwa na amfani da azumin yake yi masa:

Na farko yakan ba wa cikinsa cikakkiyar damar da zai markade abincin da aka saka masa, na biyu kuma ya hana a qara masa wani sabon aikin, koda kuwa na ruwa ne ko hayaqi, ba kuma zai ba da damar kwashe abin da aka zuba din ba ta wajen saduwar aure ko haraswa in ba rashin lafiya ne ba.

Wasu ma da ba musulmai ba sun yi magana game da yin azumi, kamar dai wani malami daga makarantar Colombia mai suna Tom Prince a yayin da yake magana da 'yan jaridu yake cewa "Ina ganin azumi wani abu ne da yake tare da ruhin mutum a addinance sama da yadda muka dauke shi a matsayin hanyar nema wa kai lafiya, duk da cewa na fara yin azumi ne don na rage qiba, sai dai kuma na gano cewa azumi yana bude qwaqwalwa matuqa, yana ba wa mutum damar da zai ga lamurra a haqiqaninsu, ya kuma iya cirato sabbin abubuwa, da samun natsuwa, ban jima ba sai da na gano cewa matsayina a addini ya qaru".

Ya ce "Zuwa yanzu na yi azumi da dan dama, kimanin kwana daya zuwa shida, babban dalilina na yin azumin shi ne tsarkake jiki daga yamutsin abinci kala daban-daban, amma yanzu ina yin azumi ne don tsarkake zuciyata daga matsalolin rayuwa, masamman wani dan bala-guro da na yi na zagaye duniya na ga yadda ake zaluntar mutane, sai na ji kamar ni ne ma dalilin wannan aika-aikar, sai na fara azumi don yin kaffarar wancan zunubin.

Tabdi, ka ji fa, arne ma kenan to ina ga musulmi?

Wanda shi yana yi ne don ibada a matakin farko, Allah SWT Ya sanya azumi ne a matsayin daya daga cikin shika-shikan muslunci, koda yake shi ne na hudu a qidaya, amma za mu ga cewa Allah da kanSa Yake cewa azumi naSa ne, kuma Shi ne zai yi sakamako da shi, sannan ko kaffara za a yi ta galatsi ce ko rantsuwa ko kisan kai, ba a sallah ko zakka ko hajji sai dai azumin.

Ga shi nan a sarari muna gani cewa Allah SWT ya wajabta mana azumi ne don mu taimakantu da shi wajen tsoronsa, ba shakka in mutum yana azumi ko da kuwa na tadauwa'i ne da wahala ka ga ya tura kansa cikin sabon Allah, ko masallacin qauye ka je a cike za ka same shi, mai cire dai dai ma ya tafi masallaci bare wanda ba ya sallar jam'i?

A lokacin mutane suke komawa ga Allah, wajen karanta Qur'ani da sararon ma'anarsa.

Zamu ci gaba insha Allah.

*Gabatarwa: Zauren Sunnah*

*Gamasu Sha'awar Bibiyar Karatukanmu Akan Shafukan Sada Zumunta Kamar WhatsApp da Facebook Zasu iya Bibiyarmu ta Wannan Hanyar*

*_Sai kuturo da Cikakkiyar Sallama. Da Cikakken Suna Tare da Adreshi ta Wadan nan Numbobin_*

_*WhatsApp Number*_
 +2348039103800.
 +2347065569254

_*Facebook @Zauren Sunnah*_
https://www.facebook.com/groups/552998655501583/

*اللهم لا تواخذنى بما نقولوا واجعلنى خيرا مما نظنون. فقلت ما قلت. إن تك حسنة فمن الله وإن تك سيئة فمن نفسك والشيطان. وسبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن لا اله إلا أنت. وأستغفر الله 
لى ولكم ولسائر جميع المسلمين من كل ذنب و استغفر وه إنه هو البرو الوبركاته

*والسلام عليكم ورحمة الله وبركاته*
Post a Comment (0)