JIKIN ƊAN ADAM 04


*بسم الله الرحمن الرحيم*
*_وصلى الله على سيدنا ونبينا محمد وعلى آله وصحبه ومن سلك طريقهم إلى يوم الدين. صلوات الله عليه فى كل الأوقات عدد رماد الأرض أعدد المخلو قات_*

*🍉🍅JIKIN DAN ADAM // 04🍍🍊*

*(Fitowa ta Hudu)*

*Rubutawa: Baban Manar Alqasim*

Baya ga wadancan azumummuka da suka wajaba ga dan adam masamman ma azumin Ramadan, akwai kuma wadan da ba su zama dole ba, su kam ya danganta ne da neman kusancin mutum ga Ubanjinsa, ta iya yuwuwa na kwana daya ne rak kamar azumin Arfa, ko Tasu'a ko kuma Ashura, ko na kwana biyu a mako, wato Litini da Alhamis, ko na kwanaki uku a wata, ko ranakun da ake farin wata 13, 14, 15, akwai kuma na watanni masu alfarma, hadisai sun tabbata cewa Annabi SAW yã riqa yin azumin Sha'aban sama yadda yake yi a sauran watannin in ba Ramadana ba.  

Ga kuma azumin kwana shida na Shawwal, sai kuma azumin tsallake kwana guda-guda wanda ake yi wa laqabi da azumin Dawoud AS, wannan yana nuna yadda mutum zai iya kasantuwa a cikin azumi koda yaushe domin neman qarin kusanci da mahalicci, ya kuma iya hutawa alabashi wani lokacin ya ci gaba, sai dai duk da cewa muslunci ya kwadaitar da bayin Allah kan yin azumin, amma ya yi hani da matsanta wa kai, ba laifi mutum ya shawarci likitoci in zai iya jimirin yin azumin kullum, shari'a ta yi umurni na kai tsaye da cewa: Ku tambayi masu ilimi in ku ba ku sani ba.

A rayuwar Annabi SAW iyalinsa sun fadi cewa yakan yi azumi har a yi zaton ba zai huta ba, yakan kuma huta har a zaci ba zai yi azumin ba, dan adam yana da kyau ya yawaita yin azumi, masamman don kankare zunubbai da gyara lafiyar jiki, amma komai aka yi shi yadda zai wuce misali akwai matsala, masamman in ba a gudanar da shi a mizanin da ya kamata ba, duk fa'idojin da azumi yake kawowa idan aka sami akasi har yunwa ta wuce qima, haqiqa ana iya samun akasin fa'idojin da ake nema, jiki zai iya yin rauni matuqa sabo da rashin samun abin da zai qarfafa shi ya gina shi, haka sauran gabobin jiki gaba daya ciki har da qwaqwalwa qarfinta zai iya raguwa.

Anas bn Malik yake cewa ya ji Annabi SAW yana cewa wasu mutane uku sun tafi gidajen Annabi SAW suka tambayi matansa yadda Annabin SAW yake gudanar da Ibada, ya yin da suka ji sai suka raina tasu, suka ce to ina mu ina Annabi SAW shi da aka gafarta masa zunuban da ya yi da wadan da bai yi ba? Wani ya ce: Ni zan yi ta tsayuwar dare ne har qarshen rayuwata, wani ya ce: Azumi zan yi na tsawon rayuwata ba zan huta ba, dayan kuma ya ce: Ni zan nisanci mata ba zan yi aure ba har abada.

Sai Annabi SAW ya zo yake cewa:
 ﺃَﻧْﺘُﻢْ ﺍﻟَّﺬِﻳﻦَ ﻗُﻠْﺘُﻢْ ﻛَﺬَﺍ ﻭَﻛَﺬَﺍ ﺃَﻣَﺎ ﻭَﺍﻟﻠَّﻪِ ﺇِﻧِّﻲ ﻟَﺄَﺧْﺸَﺎﻛُﻢْ ﻟِﻠﻪ ﻭَﺃَﺗْﻘَﺎﻛُﻢْ ﻟَﻪُ ﻟَﻜِﻨِّﻲ ﺃَﺻُﻮﻡُ ﻭَﺃُﻓْﻄِﺮُ ﻭَﺃُﺻَﻠِّﻲ ﻭَﺃَﺭْﻗُﺪُ ﻭَﺃَﺗَﺰَﻭَّﺝُ ﺍﻟﻨِّﺴَﺎﺀَ ﻓَﻤَﻦْ ﺭَﻏِﺐَ ﻋَﻦْ ﺳُﻨَّﺘِﻲ ﻓَﻠَﻴْﺲَ ﻣِﻨِّﻲ 
Ku ne kuke cewa kaza da kaza? To wallahi na fi ku tsantseni da tsoron Allah, amma nakan yi azumi na huta, na yi sallah kuma na kwanta, sannan na auri mata, duk wanda ya yi kwadayin barin sunnata to ba shi tare da ni. Bukhariy.

An gaya wa Annabi SAW cewa Amr bnl As RA yana cewa: Zan riqa tsayuwar dare, na yi azumin yini na tsawon rayuwata, sai Annabi SAW ya ce "Kai ke fadin haka?" Na ce masa "Qwarai na fada" sai manzon Allah ya ce "Ba za ka iya ba, ka yi azumi kuma ka huta, ka yi barci sannan ka yi qiyamul laili, a wata ka yi azumin kwana uku, duk wani kyakkyawan aiki za a rubanya shi sau goma, kwatankwacin azumin tsawon rayuwar mutum kenan"

Na ce "Zan iya yin sama da haka" ya ce "To ka yi azumin kwana guda ka huta na tsawon kwanaki biyu" na ce "Manzon Allah zan iya yin sama da haka" ya ce "To ka yi azumin wuni guda ka huta na daya wunin, irin azumin Dawoud AS kenan, shi ne mafi daidaituwan azumi, na ce "Zan iya yin sama da haka" Manzon Allah SAW ya ce "To ba na fifita sama da haka din" Amr bnl As ya ce "Da na karbi kwana ukun da Annabi SAW ya fadi ya fi min sama da iyalina da dukiyata" Bukhari.

Abin da ya fi kyau a muslunci shi ne tsayuwa a kan abin da za a iya dauwama a kai, yin azumin Tasu'a da Ashura, sai neman watanni masu alfarma, sai kuma yin na kwana uku a wata, ko Litini da Alhamis, ko kirdadon ranakun 13, 14, 15 a kowani wata, wannan kawai za su iya gamsar da mutum, alabashi in ya so sai ya yi rabin watan Sha'aban, in Ramadan ya wuce ya sami kwana shida a Shawwal, ga kwana daya na ranar Arfa, Allah ya sa mu dace.

*Gabatarwa: Zauren Sunnah*

*Gamasu Sha'awar Bibiyar Karatukanmu Akan Shafukan Sada Zumunta Kamar WhatsApp da Facebook Zasu iya Bibiyarmu ta Wannan Hanyar*

*_Sai kuturo da Cikakkiyar Sallama. Da Cikakken Suna Tare da Adreshi ta Wadan nan Numbobin_*

_*WhatsApp Number*_
 +2348039103800.
 +2347065569254

_*Facebook @Zauren Sunnah*_
https://www.facebook.com/groups/552998655501583/

*اللهم لا تواخذنى بما نقولوا واجعلنى خيرا مما نظنون. فقلت ما قلت. إن تك حسنة فمن الله وإن تك سيئة فمن نفسك والشيطان. وسبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن لا اله إلا أنت. وأستغفر الله 
لى ولكم ولسائر جميع المسلمين من كل ذنب و استغفر وه إنه هو البرو الوبركاته

*والسلام عليكم ورحمة الله وبركاته*
Post a Comment (0)