ADDU'A GA MAMACI 02


ADDU'A GA MAMACI0⃣2⃣

📘 SHIN ZA'A IYA YIWA MAMACI ADDU'A BADA ABUNDA YAZO A HADISI BA?? 
   Abunda akafiso kuma yafi falala shine yiwa mamaci Addu'a da abunda yazo ahadisi ingantacce, saboda shi manzon Allah anbashi jawami'ul kalim, amma babu laifi mutum ya rokawa mamaci da duk abunda ya sawwaka masa, domin wannan babi yanada yalwa, matukar dai bazaiyi addu'ar da shirka ko zalunci ba, misalin irin wadannan addu'o'in sune kamar 
١. اللهم عامله بما أنت أهله ولا تعامله بما هو أهله
٢. اللهم اجزه عن الإحسان إحسانا وعن الإساءة عفوا وغفرانا
٣. اللهم اجعل قبره روضة من رياض الجنة ولا تجعله حفرة من حفر النار 
٤. اللهم يمن كتابه ويسر حسابه وثقل بالحسنات ميزانه، وثبت على الصراط أقدامه، وأسكنه في أعلى الجنات في جوار نبيك ومصطفاك
٥. اللهم آنسه في وحدته، وآنسه في وحشته وآنسه في غربته
Dama wasu makamantar wadannan, duka ya halasta mutum yayi. 

📙 WANDA ZAISA MAMACI ACIKIN KABARINSA MAI ZAICE?? 
    Alokacin da mutum zai kwantar da mamaci acikin kabarinsa abunda Shari'a ta karantar shine zaice:
*بسم الله وعلى ملة رسول الله* 
Awata ruwaya kuma ta Abu dawud 
*بسم الله وعلى سنة رسول الله* 
Duka ruwayoyin sun inganta duk wanda mutum yayi dai dai ne. 

📖 ADDU'A BAYAN BUNNE MAMACI. 
    Alokacin da masu bunne mamaci suka gama bunne mamaci anso su tsaya akan kabarinsa su roka masa Allah dacewa kamar yadda yazo ahadisi manzon Allah na cewa "ku nemawa dan uwanku gafara, ku kuma roka masa dacewa domin ahalin yanzu ana masa tambayoyi". 
   Awannan gabar yanada kyau mugane cewa abunda yake sunnah shine kowa yayi addu'ar shi kadansa batare da ansamu dan jagora ba, domin yin hakan bidi'a ne, manzon Allah baiyuba, sahabbansa basuyi ba sannan babu daya daga magabata da aka samu yayi haka. 
    Sannan abunda wasu mutane sukeyi na zuwa kan mamaci suce masa ya kai wane idan mala'iku sukazo maka kace musu kaza da kaza, shima bai inganta ba, ya sabawa sunnah. 
Akwai wasu abubuwa da wasu mutane keyi wadanda basuda rabo acikin koyarwar manzon Allah, kadan daga cikin wadannan abubuwan sune;  
1. Karanta Fatiha da Baqara awurin kafafun mamaci. 
2. Hada mamaci da charbi yayin bunneshi
3. Saukan Alqurani awurin kabarinsa
4. Karanta surah Yaseen akan kabarinsa. 
5. Karanta masa *Qulhuwa* sau 11.
    Duka wadannan babu daya da ya inganta akarantarwar manzon Allah. 
     
📚 ABUBUWAN DA LADANSU KE RISKAR MAMACI. 
   Hakika kamar yadda muka sani idan mamaci ya mutu gabadaya ayyukansa sun tsaya banda nau'in abubuwa guda bakwai da manzon Allah ya ambata mana, wannan a iya abunda shi ya aikatawa kansa kenan, amma a abunda wani ya aikata masa ladansu bai yankeba cikin yardar Allah zai cigaba da samun ladaddakin matukar ba'a daina yimasa ba. 
   Daga cikin nau'in ibadodin da za'a iya yiwa mamaci kuma ladansu ya riskeshi akwai:
1. Karatun Alqurani, ya halasta mutum yayi karatun alqurani ya kyautar da ladan ga wani daga cikin mamatansa, sawa'un iyayene ko waninsu, wannan shine ra'ayin jumhur na malamai. 
2. Sadaqa; Imamun Nawawi ya hakaito ijma'i akan halascin yiwa mamaci sadaqa, kuma ladanta zai riskeshi. 
3. Azumi; haka shima ladansa yana riskar mamaci idan akayi masa. 
4. Aikin hajji da Umrah; shima ladansa yana riskar mamaci. 
5. Yi masa Addu'a, hakika addu'a itace mafi girman abunda mamaci yafi bukata, kuma ladanta da tasirinta yana isa zuwaga mamaci alokcin da aka masa.  
     Babu banbanci tsakanin iyaye da wasunsu gameda addu'a alokacin da daya baya raye, ma'ana ba sharadi Bane cewa lalle sai mahaifankane kadai ko kuma ya'yankane kadai zaka musu addu'a ba bayan mutuwarsu, duk wani musulmi ya halasta ka masa addu'a da nema masa gafara awurin ubangijinsa, dalili kuwa fadin manzon Allah "ku nemawa dan uwanku gafara... " Wanda kuma kowa yasan wannan ba dane ko uba ga su wadannan sahabban ba. Sannan kuma da fadin Allah subhanahu wa ta'ala 
*والذين جاءو من بعدهم يقولون ربنا اغفر لنا ولإخواننا الذين سبقونا بالإيمان....* 
Dama wasun wadannan dalilan. 

Ya Allah ka tabbatar da diga diganmu akan tafarkinka madaidaici.

# zaurenfisabilillah

https://chat.whatsapp.com/ImofrULlS3TAGi2qajt3oB
Post a Comment (0)