SUNAYEN ZAMANI


*SUNAYEN ZAMANI*

Gaskiya abin tir ne da ashsha dangane da yadda wasu musulmai suka kaucewa tsarin koyarwar addini, yana da matukar kyau mu dinga taka tsan-tsan wajen sanin kalar sunan da za mu raďa wa yaranmu, domin haqiqa suna yana tasiri a kan wanda aka sa ma wa, wato ya kan bi tsatsan asalin mai sunan, wannan shiyasa babu wasu sunaye da suka fi dace wa musulmi ya sa wa yaransa fiye da sunan *Annabawa* da *sahabbai,* da kuma sunayen da Annabi (SAW) ya yi mana suggesting irinsu *Abdullahi* da *Abdurrahman,* etc. 
.

Amma su wasu musulmai a yau waďanda suka jahilci addini ko suka biye wa son zuciya gani suke a waďancan sunayen tsofaffi ne, _they were outdated,_ sai suka koma ga qago sunaye marasa inganci suna saka wa yaransu, wani ma sunan idan ka bi diddigin sanin ma'anarsa sai ka samu cewa suna ne na wani abin qi ko wani dabba ko dai wani abu da be dace da kimar ďan adam musulmi ba, wani sunan kuwa a fina-finai da littafai kawai ake tsakuro su sai a laftawa yaro, shiyasa sai ka ga yara suna ta taso wa ta mutacciyar zuciya irin ta 'yan zamani, domin tun fari ba a gina su a kan kwadayin koyi da Annabi da sahabbai ba, shiyasa ma duk mai addini aka koma yi masa kallon ďan gargajiya mara wayau, Allah Ka tsare mu. 
.

Don haka 'yan uwa nasiha ta gare ku, Abba da Umma ku ji tsoron Allah ku sanya wa yaranku sunan da za ku yi masu kwaďayin su gaji asalin mai sunan, kada ku sanya masu sunaye marasa ma'ana ko wanda ma'anarsu ta munana. 


Allah Ya sa mu dace. 
.

*Ayyub Musa Giwa.*
*Abul Husnain.*

*🕌Islamic Post WhatsApp.*
*08166650256.*
Post a Comment (0)