ABIN DA ALLAH YA HANA KA/KI KA BARSHI KO DA KOWA NA YI

*ABIN DA ALLAH YA HANA KA/KI BAR SHI KO DA KOWA NA YI.*

Daga cikin mafi sakarci a cikin mutane, akwai wanda Allah Ya halitta da kwakwalwa domin ya yi tunani, da idanu domin gani, da kunnuwa domin saurare, amma a haka za ka same shi yana murna da yin bikin qarewar kwanakinsa tare da sanin cewa ajalinsa ne ke kusantowa, ga shi kuma bai yi wa lahirarsa kyakkyawan guzuri ba. Kawai dai shi burinsa a ce mashi wayayye saboda yana koyi da kiristochi, bikin birthday al`ada ce ta kiristochi, it has no any portion in Islam, ga shi kuma mun ji daga Annabi (SAW) cewa: *"Duk wanda ya siffantu da wani jinsi, to yana cikinsu.* Shin za ka so ranar lahira a tashe ka a cikin masu bautar d`agutu? 
.

Lallai ya zama dole ka fahimta; Yawaitar masu aikata wani abu ba shi ke nuni a kan dacewarsa ba, ka/ki yi da'a ga Mahaliccinka koda kowa ba ya yi. 


Allah Ya sa mu dace. 
.

*Ayyub Musa Giwa.*
*(Abul Husnain).*

*🕌Islamic Post WhatsApp.*
*08166650256.*

Post a Comment (0)